Connect with us

JAKAR MAGORI

Kasuwanci Ne Tsakaninmu – Tsohon Da Ya Yi Wa ’Yar Shekara 13 Fyade 

Published

on

Wani Tsoho mai shekaru 71 da aka kama da laifin yi wa yarinya mai shekaru 13 fyade a Jihar Gombe ya ce kasuwanci ne ya shiga tsakaninsu. Yarinyar ta tabbatar da cewa ya yi mata fyade ya kai sau 10, sannan ya ba ta layar zana wacce za ta dinga sato masara tana kai masa.

Amma kuma tsohon ya ce zai iya rantsuwa da kur’ani a kan cewa bai taba lalata da ita ba sai dai masara da take kai masa yana saya don sayarwa tsoho mai shekaru 71 da aka kama shi da laifin yi wa yarinya mai shekaru 13 fyade tare da amfani da ita wurin yin sata a Jihar Gombe, ya bada labarinsa.

A yayin da aka tambayi Ashiru Sule a kan yadda abin ya faru, ya ce “yarinya ta sanar da cewa na yi mata fyade kuma na ce ta dinga sato min masara. Ni ina sayar da masara ne, kuma ita ke kawo min.” Bayan da aka tambaye shi ko yarinyar manomiya ce da har take kawo mishi masara yana saya.?

Sai ya ce shi bai san satowa take ba. “Ko da aka tambaye ni dangantakar da ke tsakanina da yarinyar, na ce abokiyar kasuwanci na ce. Tana kawo min masara ni kuma ina saya. Ta ce min mahaifiyarta ke aiko ta da masara don ta sayar min. “A da ina zuwa kauyuka saro masara amma na daina saboda tana kawo min,” a cewrsa.

Ya kara da cewa, “A farkon haduwarmu, wani yaro ne ya ce yana sonta. Bayan kasuwanci, babu abin da ke hada mu amma an ce ina mata fyade. Hakan kuwa bai taba faruwa ba.” A zargin da ake wa tsohon na cewa ya bata layar zana, ya yi bayanin cewa “ban san komai game da layar ba. Zan iya rantsewa da kur’ani.” A kan zargin fyaden da yarinyar ta ce yayi mata a kalla sau goma, tsohon ya ce zai iya rantsuwa da kur’ani cewa bai taba lalata da ita ba. Malam Ashiru Sule ya sanar da The Nation cewa yana da mata daya da kuma ‘ya’ya 12.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: