Connect with us

BUDADDIYAR WASIKA

Kasuwar Bukata

Published

on

Yan siyasa su kan fassara cewa siyasa harka ce wadda ba ta da tabbataccen aboki ko makiyi. To a hakika wannan akida ta munana a tsarin siyasar Nigeria. Kowa na da ‘yancin ya bi jam’iyyar da ya ke muradi amma kuma zababbu wajibi su gane cewa su na kan kujerunsu ba don kawai saboda akida ko siyasar da ta kai su kan wannan kujera ba, ma su zabe na da hakki dari bisa dari a kansu. Da zarar dan siyasa ya hanga ya hango cewa a inda ya ke ba zai iya samun biyan wata bukata ta sa ta kansa ba, sai kawai ya canza sheka ba tare da la’akari da mutanen da su ka fita rumfunan zabe su ka zabe shi zuwa wannan mukami ba. Duk da cewa akwai dokoki da suka tanadi cewa idan aka zabe ka a doron jam’iyya, matukar wannan jam’iyya ba ta shiga rikicin cikin gida wanda ya yaga ta gida-gida ba, to kana canza sheka dole ka yi asarar kujerar ka. Wannan tsari an samar da shi don kare hakkokin masu jefa kuri’a amma abin takaici babu wata jam’iyya da ta ke yin amfani da wannan tsari.
A shekarar 2014, gungun yan siyasa, wadanda akasari gwamnoni ne suka fice daga jam’iyyar PDP su ka koma jam’iyyar APC, abinda ya kai APC ga nasara a zaben 2015. Kwankwaso na daya daga cikin jagororin wancan sauya sheka kuma dawowarsa APC ta haifar da rikici a jam’iyyar domin ya zo ya tarar da abokin adawar siyasar sa Malam Ibrahim Shekarau a matsayin daya daga cikin jagororin da su ke rike da jam’iyyar a matakin kasa. Kwankwaso da Shekarau sun kasance abin misali a bangaren adawar yan siyasa masu karfi a arewacin Nigeria. A shekarar 1999 da Kwankwaso ya ci gwamnan Kano, ya tarar da Shekarau a matsayin Permanent Secretary a hukumar ilimi wanda ya yi wa ritaya. Daga wannan lokaci gaba ta kullu tsakaninsu, yadda sai wani attajiri ne a Kano ya bawa Shekarau gidan da ya zauna. Kasancewar takalmin karfe da kwankwaso ya saka ya tattake mutane da dama a kano ya sa an sami wani gungu na ‘yan boko da attajirai da suka fito neman wani mutum wanda za su marawa baya domin ya kalubalanci Kwankwaso a shekarar 2003. Malam Ibrahim Shekarau ya kasance wanda su ka yarda su goyawa baya. Duk da cewa a wannan lokaci an yi zaben takarar fid-da-gwani na jam’iyyar ANPP inda Ibrahim Little ya sami takara, sai wadannan mutane da suka fito da shekarau su ka tuntubi Buhari wanda shi kuma a wannan lokaci ya fito takarar shugaban kasa da neman alfarmar a goya wa Shekarau baya don zama dan takarar ANPP. Da karfin tsiya a ka kori takarar Ibrahim Little aka bawa Shekarau wanda kuma a zaben gwamna ya kayar da Kwankwaso.
Shekarau ya yi mulki har karo biyu a jere, abinda ya karya canfin da ke cewa ba wani gwamna da zai iya mulkin Kano sau biyu. Allah cikin ikonsa kuma, kamar yadda Kwankwaso ya mika wa Shekarau mulki a 2003, sai gashi shi ma Kwankwason ya dawo a karo na biyu ya sake takarar gwamna a 2011 inda ya kayar da dan takarar Malam Shekarau, wato Salihu Sagir Takai, kuma Shekarau ya mika wa Kwankwaso mulki.
Wadannan yan siyasa guda biyu, hakika Allah ya yi musu duk irin ni’ima ta siyasa da zai wa wani dan Kano, amma abin takaici dukkansu sun butulce wa wannan ni’ima. Domin maimakon kowannensu a lokacin da ya ke da dama ya yi wa mutanen Kano abinda ya kamata ba su yi ba. Shekarau dai ya bude gwamnatinsa inda Malamai da Attajirai da Sarakuna su ka kwashi karensu babu babbaka. Shekarau ya kashe biliyoyin kudade ga masarauta wajen siya musu motocin alfarma da bada kwangiloli. Malamai sun yi wadaka yadda a kullum ana fitar da kudaden tallafin gina masallatai da makarantu da tallafi neman kiwon lafiya a kasashen waje daga asusun gwamnati. Kwankwaso da ya karbi mulki bai binciki duk wadancan badakaloli ba amma sai ya zo da wata sabuwar fuska ta fitar da ayyukan raya kasa na zahiri saboda ya na da muradin tsayawa takarar shugaban kasa a 2015. Hakika duk wanda ya shiga kano bayan shekaru 2 kacal na mulkin Kwankwaso a karo na biyu sai ya jinjina masa saboda irin tituna da gadoji da azuzuwan makarantu da fitulun kan titi da su ka samu a cikin kwaryar birnin Kano. Akwai mutaka jirgin sama da suka rika tambaya ko an yi sabon birnin a sashen Sahel saboda yadda su ke iya hango birnin Kano daga sama. Sai dai kash! Duk wadannan ayyuka da kwankwaso ya yi na yaudara ne kawai domin cimma burinsa na takarar shugaban kasa. Akwai mai bashi shawara da ya tab ace masa ya saka kudi a harkar noma, sai ya kale shi y ace “Banda abinka wa zai saka kudinsa a harkar noma, idan ka sa kudi a noma wa zai ganshi”. Kwanan nan gwamnatin Kano ta fitar da kididdiga da ke nuna cewa Kwankwaso ya bar wa Jihar Kano bashin da ya haura Biliyan 300 banda ayyuka da a ka fitar da kudadensu amma kuma ba’a kamala su ba, kamar titin Zaria Road, da titunan kilomita 5 na kananan hukumomi da makarantar Fim ta Bagauda da sabon Gidan zoo da sauransu.
Kwankwaso tun sanda ya bar mulkin Kano ya koma Sanata a majalisa a 2015 ba wanda ya sake jin duriyarsa sai a wannan shekara da kakar zabe ta zo. Kuma kamar a shekarar 2014, da ya tabbatar cewa Jonathan PDP zata tsayar takarar shugaban kasa, shine ya jagoranci ficewar gwamnoni zuwa APC inda ya ke ganin watakila zai iya cin takarar shugaban Kasa. Burinsa bai cika ba, don haka ya koma gefe tsawon wadannan shekaru uku ba tare da ya taimaki gwamnatin Buhari ba, ko jama’ar jihar Kano a majalisar dattijai, shine a yanzu ya sake komawa PDP cikin tsammanin zai iya samun takarar shugaban kasa.
Kamar yadda dawowar Kwankwaso cikin jam’iyyar APC a 2014 ta kori Malam Ibrahim Shekarau, yanzu ma a wannan shekara ta 2018 da ya dawo PDP ya sake korar Malam Ibrahim Shekarau daga jam’iyyar PDP.
Wajibi ne talakawan Nigeria idanuwansu su bude don gane cewa yan siyasar mu na Arewa mayaudara ne, makaryata wadanda kasuwar bukatarsu kurum su ke karewa ba ta talakawa ba. Mu duba yadda Atiku Abubakar ya ke sauya sheka duk kakar zabe, da Bukola Saraki da Aminu Tambuwal, da Attahiru Bafarawa da Ali Modu Sheriff da sauransu. A kullum gani su ke wayonsu ne zai basu mulki saboda sun manta cewa Allah kadai ke bada mulki ga wanda ya so. Abin kunya a garesu shine ku dubi Bola Ahmed Tinubu, dan siyasa da babu irinsa a yanzu a Nigeria, domin ba wani shugaba na siyasa a Arewa da yau zai bugi kirji ya nuna mutum 3 wadanda ya renesu su har su ka yi shura a siyasar Nigeria. Bola Tinubu ya dora Lagos a turbar nasara daga 1999 zuwa 2007 inda ya bawa yaronsa Fashola mulki wanda shi ma ya yi shekara 8 daga 2007 zuwa 2015 inda su ka bi tsari na ci gaba wanda babu kaucewa daga kansa. Sannan shima Fashola ya bawa wani yaron Tinubun, wato Ambode wanda ake ganin kamar ma ya fi Tinubu da Fasholan aiki. Abinda mutane da yawa ba sa lura da shi, shine cewa a tsawon shekarun 1999 zuwa 2018, shekaru 19, Tinubu bai taba kwan-gaba-kwan-baya na canza sheka daga wannan jamiyya zuwa waccan ba, jam’iyya guda su ke yi shi da yaransa har zuwa yanzu. Nasarar Tinubu mafi girma a Nigeria shine a yau, tsohon yaronsa wanda ya yi masa kwamishina a yau shine mataimakin shugaban kasar Nigeria kuma watakila shugaban Nigeria a nan gaba. A yayin da Tinubu ke gina yarbawa da yankinsu, tare da tallafawa wajen gina sabuwar Nigeria, a yau su Kwankwaso da Shekarau na yakar junansu saboda kasuwar bukatar kansu. Duk cikinsu, bayan shafe shekaru takwas-takwas su na mulkin Kano babu wani mutum guda da su ka taimaka su ka cicciba ya zama shugaba mai zaman kansa. Tun da Abubakar Rimi ya mutu Arewa ba ta sake samun wani dan siyasa da a yau za’a nuna a ce wane da wane yaransa ba ne. Rimi ne ya reni Sule Lamido, Kwankwaso, Ganduje da sauransu, amma su kuma wa su ka rena? Tinubu kan sa daga wajen su Rimi su ka kwaikwayi irin wannan siyasa ta ci gaba da gina mutanen gidanka su zama wani abu, amma mu namu shugabannin na yau sai dai bakin ciki, handuma, babakere da danniya. Wajibi talakawa su daina bata lokacinsu a kan irin wadannan ‘yan siyasa irinsu Kwankwaso, Shekarau, Sule Lamido da sauransu domin ba za su taba kai talaka gaci ba duk da cewa da bazar talakan su ka zo inda su ke. Mutane su tsaya su yi karatun ta nutsu su zabi mutanen da ke kishinsu wadanda ke sadaukar da rayuwarsu don kwato musu hakkinsu ba ‘yan kasuwar bukata ba, wadandan daidai su ke da “Ramin kura sai yayanta”
Advertisement

labarai