Balarabe Abdullahi" />

Kasuwar Galma Ta Zariya: Kasuwar Da  Ke Tallafa Wa Al’ummar Kudancin Nijeriya

Sana’ar Gwari Da Kasuwancinta

 

A nan abin da ake nufi da sana’ar gwari shi ne noma kayan lambu a kawo kasuwa domin sayarwa ga dan kasuwa. Manoni ne ke sana’ar gwari dangwari kuma mai kasuwancinta, wanda zai saya, ya gyara, ya kai kasuwa, ya jira hukuncin Allah.

A al’ada irinta gwari manomi da dangwari wani lokaci ma har da dire ban gwari, duk sukan taru su zama gwarawa, sai yadda gwarin ta juya su.

Hausawa na yi wa sana’ar gwari kirari da kasuwancinta  da çewa,” gwari danyen kaya, gari daki da duhu, gwari ba kudi ba, sai an sai da.

Bahaushe na Kallon dukkan sana’ar da mai yinta ba shi da iko a kanta, a matsayin gwari. Ma’ana sana’ar da sai yadda ta yi da mai yinta, ba sai yadda ya yi da ita ba. Duk yadda mai sana’ar ya samu kasuwa na tafiya haka zai bi. Ba a jira ballantana ajiya. Bambancinta da sauran sana’o’i sana’a ko kasuwanci shi ne, ba ta ajiyuwa.

Duk inda ta wuce ‘yan kwanaki kadan za ta rube ne, ba kamar wasu sana’o’in ba, wadanda ana iya ajiye su su dade, in kasuwa ta kulle. Da zarar an kawo kayan gwari kasuwa dole a sayar da shi a lokacin, duk yadda kasuwa ta kama, ko samu ko asara ko ma ma rasawa gaba daya, ba kamar sauran  kasuwanci ba, wadanda idan kasuwa ta kulle ana iya ajiye su zuwa wani lokaci

Sana’ar gwari da kasuwancin gwari da daukar kayan gwari a mota da ma duk wani aiki da ya shafi gwari shi ma yana iya zama gwari.

Kasuwar Galma wadda ke kan hanyar Jos daga Zariya, Kasuwa ceta kayayyakin Gwari da babu abin da ta sa wa a gaba a kowace rana sai daukar kayayyakin marmari da kuma kayayyakin miya da suka hada da Tumatir da Attarugu da Tattasai da Kwakawmba da kuma sauran kayayyaki da suka hada da Albasa  da sauran abubuwan bukatu nay au da kullun.

Wannan Kasuwa ta Galma a duk rana,motocin kayayyakin miya, kamar yadda aka ambata, suka tashi daga wannan kasuwa ta Galma zuwa kasuwannin da suke jihohin kudanci da kuma yammacin kasar nan, Jihohin da motocin da suke daukar kayayyakin gwari daga kasuwar Galma sun hada da jihohin Legas da Edo da Akure da Ibadan jihar Ribas, wato Fatakwal da kuma jihar Inugu da dai jihohi ma su yawan gaske.

Duk da wannan kasuwa ta Galma Kasuwa ce da ke karkashin karamar hukumar Zariya,bisa jagorancin kungiyar direbobin mayan motoci ta Nijeriya, Matsalolin da shugabannin da suke kula da wannan kasuwa ta Galma, ko da da rana daya ba taba nuna damuwarsu ba na dakatar da manyan motocin da suke daukar kayayyakin da aka ambata zuwa kudanci da kuma yammacin Nijeriya.

Mtsalolin da suke fuskanta a bayyane suke,da kuma matsalolin na zama a wasu lokuta barazana ga rayuwar direbobin mayan motocin, a wasu lokuta matsalolin na zama silar hadurra har ma da rasa rayuka ga wasu daga cikin direbobin da suke zuwa jihohin da aka ambata, ga kuma sarar kayayyakin da suke dauka da mafiya yawan al’umma sun sani cewar,wadannan kayayyaki, in har aka sami tsawon lokaci ba a kais u kasuwannin da aka bayyana a baya ba,shi ma babbar matsala ce,musamman ga wadanda aka dauki kayayyakin zuwa kasuwannin kudanci da kuma yammacin Nijeriya.

Kadan daga cikin matsalolin da direbobin motocin kayayyakin Gwarin ke fuskanta sun hada da yawan karbar haraji da ba shi da alkibla ga direbobin motocin  da suke daukar kayayyakin, kuma a wasu lokuta da in ma su dammara suka tare direbobin motocin da suke daukar kayayyakin da aka ambata, wasu dalilai suka sa bas u tsaya ba, a cikin lokacin kadan sai ma su dammarar su damko wanda yah au-motar kare,da zarar sun yi wa direban kofar rago, sais u lafta wa direban tarar kudi,in kuma ya saba layar cewar, ba shi da kudacen da suka ambata, ba tare da wani bata lokaci ba, sai su umurci direban motar ya aje motar a gefen hanya inda suke zaune, suna gudanar da ayyuka, na tsawon lokaci, ba tare da tunanin direban zai iya tafka asara ba.

Wata matsalar kuma ita ce, na yadda a cikin tsawon kilo mita daya zuwa biyu, sai jami’an tsaro kashi-kashi fiye da biyar su tasaya a kan titi,duk direban da ya je wucewa, sai an yi wa direban tarar da ba a bayar da rasit na tarar da aka yi wa direbobin.

Wannan tara za a iya kirar ta ta  gama gari ga duk direban da ya fito daga arewacin Nijeriya,wanda babu tausayin halin da direban ke ciki ,ko kuma tunanin halin matsan rayuwa ko kuma asarar da  wanda aka yi masa dakon kayayyan zai fuskanta, na lalacewar kayayyakin da direban ya dauko, zuwa kudancin Nijeriya ko kuma yammacin Nijeriya Wani abin mamaki kuma shi ne, duk da wannan kungiya ta direbobin manyan motoci ta kasa baki daya ce, direbobin kan tsici kansu a cikin tsomomuwar matsalar da aka tsoma su a ciki, sai ka ga sai dai reshen kungiyar da ke Arewacin sun aika wa da direba kudaden tarar da na bayyana a baya ba batun rasiti in an biya tarar, in ko aka tatuke direba a kan titin zuwa inda zai aje kayayyakin da ya dauko, bai iya biya biyan wannan haraji mara-alkibla ba, ya na kallo zai tafka asarar  na kayayyakin day a dauko.Mai karatu, ka san in an sami sa’o’i a kalla hudu  ba a  biya wannan tara ba a dalilin haka, direba da kuma wanda aka daukar masa kayan sai su yi asarar da ba  ba ta  cika misiltuwa ba, wato kayayyakin da direban ya dauko, su lallace,sai direban da kuma wanda aka dauko ma sa kayan ya yi sallama da direban, ya dawo arewa, ba tareb da an kai wannan kaya da dauka zuwa wata kasuwa a kudanci ko kuma yammacin Nijeriya.

Tarihi ba zai taba mantawa da matsalar rikicin addini da ta faru a wasu sassa na jihar Kaduna ba,inda a dalilin wannan matsala, an shafe makonni hudu ba a kai timatir da dangoginsa kudanci da kuma yammacin kasar nan ba,a wannan shekara ta 2000,wato kimanin shekara goma sha takwas ke nan, a wannan lokaci, rashin tsaro da ya sa al’ummar arewa duka kasa kai kayayyakin miya zuwa kudanci da kuma yammacin kasar nan ba, in mutum ya saba sayen abincin Naira dari biyu ne, ya koshi, a wannan lokaci, sai ya biya naira dari biyar zuwa shida a abincin da zai ci ya koshi a nan take.

Lokaci ya yi da uwar kannan kungiya ta kasa da cibiyar ta ke Abuja, ta fara aiwatar da  da tsare-tsaren da za su tallafa wa mambobinsu da suke daukar kayayyakin da aka ambata daga wannan kasuwa ta Galma da sauran kasuwanni da suke kai timtirr da dangoginsa, ba su rika sa hajar mujiya matsalolin da direbobinsu ke fuskanta  a kudanci da kuma yammacin Nijeriya.

Malam Haruna Kakiyeyi,shi ne shugaban kungiyar direbobin manyan motoci na tashar  Galma a Zariya,ya ce su a kullun suna da tsare-tsare  da suke tallafa wa mambobinsu a duk lokacin daya daga cikin mambobinsu ya sami matsala,su kan aika ma sa duk kudaden day a ke bukata, a wasu lokuta ma kungiyar kan tashi wani cikin shugabannin kungiyar ya je duk inda direbansu ya sami wata matsala.

Game da kare dukiyoyin wadanda suka bayar da kayayyakinsu  a kai kudanci ko kuma yammaci,shugaban kungiyar y ace suna kula  da matar da za ta dauki kayyan, motar na da matsala,su kan hana direban ya dauki kayan,wannan mataki da suke dauka,a cewar Malam Haruna Nuhu Kakiyeyi, ya zama silar raguwar yawan hadurran da suke faruwa a kan hanyoyi.

 

Exit mobile version