A gun taron manema labarai na musamman da ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta gudanar a yau Talata, jami’ai masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa, yayin da manufofi da matakai daban daban na fadada kashe kudi ke ci gaba da yin tasiri a bana, kasuwannin kayayyakin masarufi na kasar Sin baki daya, sun ci gaba da nuna yanayin bunkasa bisa daidaito.
Jami’an sun kuma ce ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin za ta inganta ayyuka na musamman don bunkasa kashe kudi, da gudanar da ayyuka a fannoni hudu, wato inganta yadda ake amfani da kayayyaki, da fadada amfani da hidimomi, da samar da gajiya daga sabbin kayayyaki, da kuma kirkirar sabbin yanayin cimma gajiya.
Ma’aikatar kasuwancin ta kuma bayyana cewa, za ta karfafa bincike kan manufofin da suka shafi amfani da fasahohin zamani, da kuma inganta ci gaba da amfani da kayayyakin dijital. (Safiyah Ma)