Connect with us

RIGAR 'YANCI

Kasuwar Kwari Ce Ta Farko A Yakar Korona – Ambasada Sagir Shariff

Published

on

Ambasada Sagir Wada Shariff, shugaban kungiyar ’yan kasuwar Kantin Kwari ya bayyana cewa, kasuwar ita ce kasuwa ta farko a sahun gaba wajen amsa kiran Gwamnatin Kano karkashin Jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje a daukar matakai na yaki da cutar Korona tsakanin kasuwannin Kano.

Ambasada Shariff ya bayyana haka ne a ofishinsa da ke kasuwar Kantin Kwari a ranar Laraba da ta gabata a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai kan namijin kokarin da su ke yi na kaffa-kaffa da cutar ta Korona da kuma yakarta.

Har ila yau ya ce tunda wannan Annoba ta zo kano Gwamnati da Likitoci da Malamai da sauran masu ruwa dda tsaki akan wannan cuta sukai ta fadakarwa a kafafan yada labarai, Jaridu, Rediyo,Talabijin da dai sauransu to mu `yan kasuwa sai muka dau wannan fadakarwa da Nasiha ta Malamai da likitoci da kuma ita kanta Gwamnatin kano sai muka fara daukar matakan yaki da Korona domin dai tafi da har kokin kasuwancin mu ba tare da yaduwa da yada wannan cuta ba a cewar Ambasada Shariff Wada, shugaban kungiyar kasuwar kantin kwari Kano.

Haka zalika ya ce yanzu haka matakin su shi ne sanya sabulu da sinadarin wanke hannu a kowace kofar kasuwar ta yadda mai siye da sayarwa duk wanda ya shigo sai ya wanke hannun sa da kuma yin amfani da Takunkumin Baki da Hanci da kuma kokarin a ga anyi zama nesa da nesa kamar yadda masana suka tabbatar cewa haka yana daga cikin matakan yaki da wannan cuta ta Cobid-19.

Baya ga wadannan matakai kuma ga kuma gudummawa da tallafi da su ka bawa kananan `yan kasuwa sakamakon wannan Annoba ta Cobid-19 da ta kawo shiga wani hali na damuwa wanda tsarin kasuwar kantin kwari su na da tsarin Gidaje-Gidaje ne wanda a kowane gida Allah ne ka dai yasan a dadin wadanda su ke cin abinci a kowane Gida da ke kantin kwari kuma a dadin Gidan a kalla akwai 176 to a cikin su an kai kayan tallafin Abinci a Gidaje 150 domin kowane gida shiyasan a dadin mutanan da ke Gidan kuma su suka san masu karamin karfi da bukatar taimako a kowane Godi kuma ansamu tallafin ne daga masu karfi da zuciyar tallafawa masu karamin karfi na wannan kasuwa ta kwari.

A karshe Ambasada Sagir Wada Shariff ya yabawa Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje kan matakan sassauta kulle da ba yan kasuwa damar bude kasuwan ni har sau Uku a mako a yi sallar Jumaa ayi kasuwanci a kano, sabanin wasu Jahohi Kamar Kaduna wanda kuma bisa yadda da bin wadannan kaidoji da daukacinyan kasuwa da kasuwan nin kano su ke yi muna sa ran samun karin rana ku daga Dr. Abdullahi Umar Ganduje Kasncewar sa Mutum ne mai hangen nesa da kishin kasuwanci da Alummar kano, idan kuma ya bukaci Alummar kano da a dukku fa da Adduoi a masallatan Jumaa da sauran masallatai dan neman Allah ya kawar da cutar korona a kano da kasar mu Najeriya dama duniya baki daya Albarkar shugaban mu shugabam mu shugaban Halittar Duniya da Lahira baki daya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: