Kasuwar ‘Yan Lemu Ta Bukaci Tallafin Karamar Hukumar Sabon Gari

Daga Nasiru Adamu,

Ranar litinin makon da muke ciki ne shugaban kasuwar yan lemu kwangila zariya, Malam Abdulkadir Abubakar ya yi kira ga mai girma shugaban karamar hukumar sabon gari Hon Muhammad Usman da ya waiwayi Kasuwar yan lemu dake kwangila domin kawo mata dauki, don samun gudanar da harkokin su cikin kwanciyar hankali da lumana

Malam Abubakar yace kasuwar tasu na fuskantar barazanar cin- ruwa musamman ganin cewar kasuwar ta na cikin yanayi na Fadama, sanan kuma ana fuskantar damina.

Hakanan yace tun zamanin shugabancin Hon Annur aka mallaka musu filin amma har yanzu basu taba moran romon dimokoradiya ba, haka nan yace filin an taba mallaka shi ga kungiyar masu tomatur da gungiyar Employa, da kungiyar masu saida goro amma duk suka gudu sabo da yanayin sa na fadama, Sai daga bisani aka basu,

Tashin farko Malam Abdulkadir ya ce, sai da suka hada zunzurutun kudi sama da naira milyan daya da rabi daga “yayan kungiyarsu, aka kawo masu tifan maramari sama da dari biyu suka bazata a filin, kuma tun daga wancan lokacin haka suke ta yi duk shekara. duk da kasancewar kasuwar tana daya daga cikin jerin wuraren da karamar hukumar take samun kudaden shiga mafi tsoka .

Kuma yace baya ga kudaden shiga da wannan kasuwar take samarwa, tana kuma bada gudunmawa ga al`ummar wanna yankin wajen samar da aikin yi domin hana zaman banza, wanda shi ke kawo bata gari. Don akalla a duk yini mutanen da ke zuwa suna amfana a cikinta sunfi dubu dari 5 tsakanin maza da mata manya da kankana yara.kuma itace kasuwar kayan marmari mafi girma a wannan yanki dake samara da kayan marmari tun daga nan har karshen iyakar kasarnan ta bangaren Arewa.

Don haka ya ce ba za su taba yin kasa a gwiwa ba har abada, wajen mika kokon baransu na neman tallafi daga mai girma shugaban karamar hukuma, har sai hakar da suke ta cimma ruwa.

Ya ci gaba da cewa abinda suke bukata tallafinsa bai wuce marmar da tsaga magudanan ruwa a cikin kasuwar, sanan suna bukatar a kewaye masu kasuwar da katanga mia get, don samar da tsaro wadannan abubuwan su suka fi damun mu inji shi.

Daga karshe ya yi wa shugaban karamar hukumar, tare da mai martaba Sarkin Zazzau addu`ar fatan alkairi tare da murnan kammala azumi lafiya tare da kwanciyar hankali.

Exit mobile version