Kasuwar Yawon Bude Ido Ta Sin Ta Farfado A Lokacin Hutun Ma’Aikata

Daga CRI Hausa

A yayin da kasar Sin ta yi nasarar dakile bazuwar annobar COVID-19 a cikin kasarta, da ma yadda ake samun karuwar yiwa jama’a alluran rigakafin annobar, ya sa jama’a a cikin kasar ziyarar wuraren bude ido a lokacin hutun kwanaki biyar na ranar ma’aikata.

Rahotanni na nuna cewa, yadda fasinjoji ke shiga da fita a birnin Beijing, ya kai sabon matsayi a ranar 1 ga watan na Mayu. A mataki na kasa kuma, fasinjojin da suka yi bulaguro ta jiragen sama a ranar 30 ga watan Afrilu, ya zarce wanda aka gani a makamancin lokaci na shekarar 2019, yayin da a hanyoyin cikin gida ma, aka samu karuwar sama da kaso 20 cikin 100 kan na makamancin lokaci na shekarar 2019.

Masu sharhi a fannin yawon shakatawa, sun bayyana cewa, adadin jiragen sama da suka yi zirga-zirga a cikin gida a lokacin hutun, ya zarce wanda aka yi kafin barkewar annobar COVID-19, ana kuma sa ran cewa, zai kai babban mataki.

Hukumar al’adu da yawon shakatawa ta birnin Shanghai, ta bayyana cewa, masu yawon bude sama da miliyan 10.3 ne suka ziyarci birnin a ranaku uku na farko na ranar hutun ma’aikatan. Idan aka kwatanta da makamancin lokaci na shekarar 2020, sashen al’adu da yawon bude ido, ya samu karuwa matuka, har ma ya zarce karuwar da aka samu a wasu sassa a makamancin wannan hutun shekarar 2019. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CRI Hausa)

Exit mobile version