Katin Zabe: INEC Za Ta Fara Bin Gida-gida A Jihar Kogi

A kokarin da ta ke yi na tabbatar da ganin kowa ya mallaki katin zabensa gabanin babban zaben kasa da za a gudanar badi, hukumar zabe ta kasa (INEC) a jihar Kogi ta ce nan bada dadewa ba za ta dukufa bin gida-gida domin tabbatar da ganin ta rarraba katinan zaben na dindindin ga masu su.

Kwamishinan hukumar na jihar, Farfesa James Apam, ne ya bayyana hakan a taron daya gudanar da shugabanin jam,iyyu da jami,an tsaro da kungiyoyin farar hula da kuma manema labarai a birnin lakwaja.

Ya ce har ya zuwa yanzu akwai katunan zabr na dindindin dubu dari biyu da casa,in da uku da dari uku da arba,in da daya da masu su basu karba a jihar ta Kogi,inda kuma ya kara da cewa hukumar ta INEC zata tabbatar katunan zaben sun kai ga masu su kafin babban gamagari da za a gudanar a 2019 idan Allah Ya kaimu.Farfesa Apam ya kuma bayyana cewa hukumar zata rarraba katunan zuwa dukkan yankuna(wad wad) dari biyu da talatin da tara dake fadin jihar domin rarraba su ga masu su.

Ya ce hukumarsa ta riga ta shirya tsaf domin gudanar da rarraba katunan. Ya kara da cewa hukumar ta INEC tayi rajistan sabbin masu kada kuri,a dubu dari biyu da sittin da daya da dari shida da sittin da tara daga watan yulin 2017 zuwa yulin 2018 inda yace sabbin wadanda hukumar tayi wa rajistan sun hada da maza dubu dari daya da ashirin da daya da dari da casa,in da shida da kuma mata dubu dari daya da ashirin da tara da dari shida da arba,in da uku.

Kwamishinan zaben ya kuma yi bayanin cewa hukumar ta rarraba katunan zabe dubu hamsin da tara da dari shida da sittin da tara ga masu su ,sannan kuma ta maye gurbin katuna dubu goma sha biyu da dari shida da sittin da daya wadanda suka lalace ko bata ko kuma fuskar mai katin ya goge(Defaced).

Kamar yadda farfesa Apam yace,ci gama da yin rajistar take yiwa masu jefa kuri,a a yanzu zai kawo karshe a ranan sha bakwai ga watan Agusta,amma kuma hukumar zata ci gaba da rarraba katunan zaben har mako guda kafin babban zaben 2019.

Sai dai kuma Far fesa Apam yayi kira ga yan jarida da kuma kungiyoyin farar hula dasu tamaikawa hukumar ta INEC wajen wayarwa da jama,a kai akan mhimmancin yin rajista da kuma karbar Latin zaben na  dindindin.

Dangane da zaben cike gurbi da hukumar data gudanar a mazabar lokoja da Kotonkarfe ta tarayya a ranan sha data ga watan Agusta kuwa, Farfesa James Apam yace hukumar ta INEC ta riga ta kammala dukkan shirye shiryen gudanar da zaben , lnda had ma ya nemi hadin kan jam, iyyun siyasa da yan jarida da kungiyoyin farar hula da jam, ian tsaro da kuma sauran masu ruwa da tsaki don ganin hukumar ta samu nasarar gudanar da zaben ba tare da wata matsala ba, sannan ya tabbatarwa da dukkan jam, iyyun siyasa da zasu fafata a zaben cike gurbin cewa hukumarsa zata gudanar da zabe mai tsafta tare da yin adalci ba tare da Santa son zuciya ba ko kuma fifita wata jam, iyya akan data.

Zaben cike gurbin ya biyo bayan gibin da aka samu a mazabar Lokoja da Kotonkarfe sakamakon rasuwar dan majalisa mai wakiltar yankin kuma mataimakin masu rinjaye a majalisar wakilai ta kasa, wato HON Umar Buba Jibrin kwanakin baya bayan yayi fama da doguwar jinya.

 

Exit mobile version