Katse Kwangilar Kamfanin Atiku: Siyasa Ko Ƙa’idar Aiki?

Daga Sulaiman Bala Idris, Abuja

A ranar Juma’ar da ta gabata ne Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta ƙasa ‘NPA’ ta yi ƙoƙarin wanke kanta daga zargin da aka fara yi dangane da katse kwangilar lura da jirage da sanya ido wanda kamfanin ‘Intel Nigeria Limited’ ke yi. Kamfanin kuma da tsohon mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ke da kaso mai  tsoka na hannun jari.

Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwan ta fid da wannan matsaya nata ne a wata takarda da Babban Manajan kula da yaɗa labarai, Abdullahi Goje ya fitar.

Goje ya tabbatar da rahotannin da ke cewa hukumar ta ɗauki matakin katse kamfanin na Atiku ne bisa dogaro da shawarar da Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami ya ba hukumar na ta katse kwangilar kamfanin na ‘Intel’.

Sai dai wannan matakin da Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta ɗauka ta tayar da ƙura sosai a Nijeriya, musamman ganin cewa Atiku Abubakar na ɗaya daga cikin jiga-jigan da zasu yi takarar shekarar 2019.

Bayanin na Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa, ya bayyana cewa, hukumar ta nemi shawarar Ministan Shari’an ne bayan an kwashe kusan shekara ɗaya suna fama da kamfanin na ‘Intel’ da ya yi biyayya ga matakin gwamnatin tarayya na amfani da asusun baiɗaya.

Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa  ta bayyana cewa: “Umurnin farko da aka ba kamfanin ‘Intel’ na ya bi ƙa’idar da gwamnatin tarayya ta shimfiɗa shi ne wanda tsohon Babban Daraktan kuɗi da gudanarwa, Mista Olumide Oduntan ya aike wa kamfanin a ranar 28 ga watan Yunin 2016, inda yake umurtar kamfanin da ya riƙa zuba dukkan kuɗaɗen da ya samo a madadin Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa zuwa ga asusun baiɗaya na babban bankin tarayya.

“Duk wani ƙoƙari da hukumar ta yi na ganin kamfanin ya yi biyayya ga wannan umurni, abin ya ci tura, ta yadda har sai da aka kai hukumar bango ta aika wa da Ministan Shari’a da takardar neman shawarar yadda wannan alaƙa a tsakanin hukumar da kamfanin Intel za ta ci gaba da kasance wa. Wasiƙar wacce aka aika wa da Ministan a ranar 31 ga watan Mayun 2017.

“Shawarar ta Ministan Shari’a wacce aka aiko da ita a ranar 27 ga watan Satumbar 2017, wacce kuma aka aika ta zuwa ga Babban Darakta na Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa, Hajiya Hadiza Bala Usman, daga Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Tarayya, Abubakar Malami (SAN) ce ta shawarci da a katse wannan kwangila.” Inji

Takardar wacce Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta fitar ta ci gaba da cewa, dole ne hukumar ta bi shawarar da Ministan Shari’ar ya ba ta.

Sai dai da yawa na kallon lamarin a matsayin wani sabon salon bita-da-ƙulli ga tsohon mataimakin shugaban ƙasan, wanda kuma aka amfani da Hadiza Bala Usman a matsayin makamin yaƙi. Musamman ma bisa la’akari da cewa Atikun a lokacin da zai yi takarar shekarar 2015 ya ayyana kamfanin ‘Intels’ cikin kadarorinsa; hanya mafi girma da yake samun kuɗaɗen kasuwanci.

 

Exit mobile version