Connect with us

ADABI

Katsina Ta Dikko Dakin Kara: Tsokaci kan kafuwa da shahararta (I)

Published

on

A cikin zamanin mulkin Sarkin Katsina Muhammadu Korau (1445-1495) wuraren da ke kewaye da koramar Tilla da koramar Ginzo a cikin birnin Katsina su ka bunkasa da jama’a, kuma mutanen su na yin noma, kiwo, kira da sauransu. Akwai kuma kwarin tama a kusa da rafin. Karshe dai har koramar Tilla ta zama zangon fatake. Wannan shi ne babban wurin kasuwancin birnin Katsina, da ma sauran biranen da ke a kasar Hausa kwata. Kada kuma a manta da kasuwancin da ya hada Katsina da sauran biranen kasar Hausa, na goro, gishiri, bayi, dawakai, wanda tun daga yankunan tafkin Chadi ake zuwa don yin kasuwancin a dai tsakiyar karni na 15 din. Akwai wurin bauta ko tsafi mai suna Yuna kusa da tsamiyar badawa wanda ke kimanin kilomita daya da rabi tsakanin sa da koramar Tilla.
Sai aka rika ma yin hijira har daga Borno zuwa wurin da a yanzu ake kira Rafukka da Unguwar yammawa da sauran wurare kusa da fadamar Tilla da kuma kwarin tama. Wannan shi ya kara buda birnin har wasu sabbin unguwanni su ka samu. A lokacin ne kuma tsamiyar badawa ta shahara wajen yin tsafi da bautar iskoki. Akwai Fulani masu kiwo da ba musulmi ba da su ke zuwa wurin bauta, tun ma zamanin sarki Sanau. Duk da huldar kasuwanci da ta hada su, a tsakanin musulman da ke zaune a birnin Katsina a wannan lokaci da Wangarawa, Barebari da Fulani, addinin musulunci bai yi tasiri sosai ba a kansu saboda ‘yan kananan addinan su a lokacin masu karfi ne. Gashi kuma Durbawa sun mamaye sha’anin siyasar zamantakewar mutanen, da ma addinan su Shi ma kan sa sarki Sanau an ce yak an je tsamiyar badawa wajen da ake bauta. Zuwan Korau, kamar yanda labari ya gabata, ya yaudari matar Sanau ya amshi wani kambu da Sarkin ke daurawa a jikinsa idan shekara ta zagayo za a yi kokowa. Dama shi kambun, matar sa ce ke ajiye masa. Zuwan Korau, ya samu goyon baya daga birnin Samri da ‘Yandaka. Sannan kuma ya samu dammar zama shugaban wani wurin bauta da ake cema Rawada wanda ya hade da gidan sarauta lokacin da ya zama sarki.
Daga lokacin da ya amshi sarauta ya ci gaba da fadada kasar Katsina, ya shigo da wasu garuruwa da kauyuka a cikin kasar. Wannan shi ya haifar da samun karin wasu birane da garuruwa a kasar Katsina din ko da bayan zamani Sarki Korau. Akan hakan, ya zuwa karshen karni na 17 kasar ta Katsina na da girman murabba’in kilomita 15,500. Lokacin da Sarki Korau ya rasu sai batun wanda za ya gaje shi ya rataya a kan iyalan sa da sauran dangi da masu gari kamar su Samri, ‘Yandaka, Gazobi da Durbi. Wanda ya zabi sarki daga cikin su shi aka ba sabon suna Galadima, daga nan kuma wannan suna ya samu. Gashi kuma ana da bukatar a tattara abin da ya shafi siyasar zamantakewar jama’a da tattalin arziki a wuri daya, Katsina. Korau shi ya fara yin wannan yunkurin. Saboda shigowar baki bama dai Kanawa das u ka shiga yin tururuwa garin a kasha na biyu na karni na 15. Zancen zaben sabon sarki ya kara daga darajar su masu zaben. Wannan kuma ya haifar da kace-na-ce tsakanin masu gari da ke cikin birni da sauran masu rikon sarautu na sauran garuruwan kasar Katsina. Batun zaben ya dada shigo da masu gari na sauran garuruwa kusa da masarautar Katsina.
Ibrahim Sura (1495-1497), wanda ya gaji sarki Korau bai dade ba shima Allah Ya yi masa rasuwa, shekara biyu kacal ya yi akan mulki. Amma kafin rasuwar sa sai da Abd al-Rahman al-Suyudi ya aiko masa da takarda daga Cairo, kamar yanda mu ka ambata a baya, ya na mai bashi shawara da ya yi aiki da gaskiya kuma ya rike amana. Shi al-Suyudi ya aiko da wannan wasika ne don a yi aiki da ita a dora masarautar Katsina a bisa sabuwar turbar sarautar zamani.
Banda masarautar Katsina, masarautun da ke da karfi a wannan lokaci na yankin Bilad as Sudan sun hada da na Kano, Barno, Shongai da Kebbi. A nan, ci gaba na samuwa da sauri na sha’anin sarauta da tattalin arziki. Kai, daga karshen karni na 15 da farkon karni na 16 sarakunan su sun zama masu karfi da iko, su ne: sarkin Kano Muhammadu Rumfa (1463-1499) da Kanta na Kebbi (1513) da Mai Ali Ghazi na Borno (1470-1503) da kuma Askiya Muhammadu Toure na Shongai (1493-1528) Babban batun da ya fi daukar hankalin masu sarauta da talakawa a lokacin shi ne zancen addinin islama da kuma bautar iskoki da gumakka.
Ana cikin wannan yanayi sai ga wani babban malami da ake kyautata zaton ma waliyyi ne, ana ce da shi Sheikh Abu Abdallah Muhammad bin Abd al-Karim bin Muhammad al-Maghil wanda ya iso cikin birnin Katsina a shekara ta 1490 wanda kai tsaye da ya zo wa’azi ya yi ta yi, na zuwa ga addinin Allah (SWA) Wasikar da ya rubuta ma Sarkin Kano Muhammadu Rumfa (1463-1499) mai taken Taj al-din fima yajib ala-l muluk ita ya aiko ma Sarkin Katsina, na ya na ba shi shawara ya sa ido sosai akan masu gudanar da mulkin sa ko masu gari, ya tabbatas da gaskiya ya kuma tabbatas komi an yi shi akan yanda addinin islama ya shimfida. A cikin takardar, ya ce a tilasta ma kowa ya rungumi addinin musulunci. Ya kuma tsara ma gwamnatin sarki yanda za a amshi zakka da yanda za a bada ta ga mabukata. Shi kuma ya tsara masu yanda za su gudanar da mulki kamar yanda ya zo a Alkur’ani mai tsarki da Hadisin Manzon Allah (SAW)
Amma shima Sheikh Abu Abdallah Muhammad bin Abd al-Karim bin Muhammad al-Maghil ya san cewa wasu abubuwa da su ka shafi addinin musulunci da ya ke so Sarkin Katsina da jama’arsa su jaddada ba su yiwuwa. Akwai abubuwa da dama da su ka shafi al’adu da siyasar wannan lokaci da shima ya san ba su baruwa a Katsina da Kano kamar yanda ya je Katsina ya tarar. A cikin littafin. Tarikh Asli Katsina wa Asli Ghubir an bayyana cewa shi wannan bawan Allah shi ya ma kai addinin musulunci Katsinar. Abinda kuma ya sanya cikin lokaci kankane aka yarda da abin da ya kawo shine da bai sa abinda ya shafi son zuciya ko abin Duniya ba, ya zo da abin da Alkur’ani maitsarki ya kawo ne. Tuni wasu masu sha’anin mulki a kasar Katsina su ka amshi kiran Abd al-Karim bin Muhammad al-Maghil su ka kuma fara aiwatar da mulki kamar yanda ya zo daga koyarwar Annabi Muhammad (SAW) Shi kuma Sarkin Katsina Ali Murabus sai ya maishe da gidan Korau kamar wani wurin yin taro ko ganawa a yanda za a kare garin daga mahara. A takaice ya ma kirkiro rundunar sojoji ko dakarun yaki da su ka shata iyaka tsakanin Katsinar da Kano, a lokacin kuma Kano din na yawan kai wa Katsinar harin yaki.
Advertisement

labarai