Daga Sagir Abubakar, Katsina
Gwamnatin jihar Katsina za ta kafa kwamiti da zai gudanar da kidaya ga dukkan yara na wadanda yan bindiga suka kashe iyayensu a fadin jihar nan.
Gwamna Aminu Bello Masari ya sanar da hakan a lokacin da ya karbi bakuncin shuwagabannin kungiyar yansintiri na kasa a karkashin jagorancin babban kwamanda na kungiyar Dr. Usman Muhammad Jahun da Isuka kawo mashi ziyara. Kamar yadda ya ce yunkurin zai taimaka ma gwamnatin jiha ta fiddo da hanyoyin da za ta taimaka ma yaran. Gwamnan ya yi la’akari da cewa barin irin wadannan yaran haka nan zai iya haddasa wani abu.
Gwamnan jihar ya yi la’akari da cewa shigowar makamai da miyagun kwayoyi a kasar nan shi ne babban abun da ya ke taimakawa wajen aikace-aikacen yanbindiga.
Don haka, ya bukaci shugabancin kungiyar yansintirin musmaman wadanda suke a yankunan kan iyaka da jihar da su zama masu sanya idanuwa kuma su kai rohoton shigowar irin wadannan haramtattun kayayyakin a wasar nan ga hukumomi mafi kusa da su.
Wannan kamar yadda ya ce kari ne bisa ga aikce-aikce wasu da su ke kiran kansu yan sakai, wadanda suke zuwa daga wasu wurare su kai hari ga jama’a da sunan suna zarginsu da aiakce-aikace na ynabindiga.
Gwamnan ya kara jaddada kukurin gwamnati na taimakawa duk wata kungiyar da take da niyyar taimakawa wajen tabbatar da tsaro a jihar nan. Tun farko, babban kwamandan kungiyar yansintiri ta kasa Dr. Usman Muhammad jahun ya jaddada kudurin kungiyar domin taimakawa wajen kawar da yanbindiga a jihar nan.
Kamar yadda ya ce kungiyar za ta turo yayanta daga fadin kasar nan domin hada karfi da fiye da yayan kungiyarta yansintiri dubu ishirin da shidda da ke jihar nan domin kawar da aikace-aikacen yanbindiga a cikin watannin ukku.
Ya yi roko gwamnati da ta tallafama kungiyar da mota da kuma ofis domin samun damar gudanar da ayyukansu na sintiri yadda ya dace. Dr. jahun ya yi roko ga gwamnatin jiha da ta yi wata doka da za ta samar da yanayi mai kyau na aiki ga kungiyar kamar yadda wasu jihohin kasar nan suka yi.