Wakilinmu" />

Katsinawa Ba su Gaji Siyasar Daba Ba -Nura Khalil

Fitaccen dan siyasar nan a Katsina kuma makusanci ga shugaban kasa Muhammadu Buhari shekaru aru-aru tun ana zamanin PTF ya ce, Katsinawa ba su gaji taron siyasa da fito da makami ba, wato ba su gaji siyasar Daba ba.

Injiniya Nura Khalil, wanda ya yi Takarar Gwamnan Katsina a tsohuwar rushashshiyar Jam’iyyar ANPP a 2003 da 2007 wanda kuma yanzu dan Jam’iyyar APC ne, ya bayyan haka ne a lokacin wata hira da maneman labarai da ya yi a birnin Katsina. Ya ce, akwai lokacin da za su je yakin neman zabe a garin Dutsi a cikin Jahar Katsina wanda a wannan lokacin su Hukuma ta ba damar zuwa yakin neman zabe amma sai ’Yan Jam’iyyar adawa ta PDP da suke rike da Gwamnati a wannan lokacin suka tare musu hanya da makamai iri-iri su kuma ba su da makamai ko daya a hannunsu amma Allah ya taimake su su da ba su da makaman yaransu suka kwace makaman a hannun ’yan PDP, a wannan lokaci a 2003. Ya ce to tun daga wannan lokaci ba a sake wata maganar fito da makami ba.

Injiniya Nura Khalil ya ce, su duk wani abu na rashin mutunci da cin amana da yaudara da sauran duk wani abu da Allah ba ya so, su ba su dauka sun sa shi a cikin siyasarsu ba, kamar yadda wasu suke cewa su ne mahadai kuma sinadarin Siyasa, to su dai ba su yarda da haka ba kuma ba sa yi. Dan haka Katsinawa ba su yarda da Siyasar Daba ba, wannan kuma yana faruwa ne sakamakon Dattawa da sauran Matasa na gari da ke cikin harkar fadakarwa da gyara siyasar katsinawa. Haka kuma ya bayyana cewa dan gane da irin kiran da aka yi masa na ya zo ya tsaya sanata mai wakiltar yankin Funtuwa, ya ce, duk wani abu da mutanansa suka ce ya yi zai yi domin dai cigaba ake nema. Ya ce koda kuwa Kansila aka ce ya yi indai za a samu ingantacciyar Rayuwa da walwala ga mutanensa to zai yi, domin yana cikin masoya ne wadanda suka hada Iyaye da Yayye, Abokai, Kanne ’Ya’ya da Jikoki, dan haka ba shi da wani buri fiye da ya ga al’ummarsa ta cigaba ta hanyar samun ayyukan yi da sana’o’I, domin duk lokacin da Matasa da sauran al’umma suke da abin yi to Kasa za ta cigaba amma in suna zaune ba sa komai, to Kasa za ta durkushe ne.

Haka kuma ya ce, idan ka duba Tarihi za ka ga Alhaji Shehu Shagari Sakkwato ya yi Minista kuma ya zo ya yi Kansila a mazabarsa, haka shi ma marigayi Umar Musa ’Yar’aduwa ya yi Minista kuma ya zo ya yi shugaban Karamar Hukuma. Ya ce, indai bauta wa jama’a za ka yi to mukami ba ya kadan. Haka kuma a karshe a matsayinsa na makusanci ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya ce, Buhari Mutum ne da ba ya karbar munafunci. Ya ce, idan ya yarda da kai to ba mai bata ka, ya yarda, amma in ya kama ka da kansa to shi ke nan fa kai da shi sai dai gaisuwa ta hada ku.

Exit mobile version