Kaunar Juna Da Salama Yesu Almasihu Ya Koyar Da Mu –Rabaran Adeyemo

Daga Abdullahi Muhammad, Kano

An bayyyana ranar kiriseti a matsayin ba ranar shaye shaye ba ranar ce ta kauna da kuma Salama wannan bayani ya fito daga bakin shugaban kungiyar Kiristoci CAN ta jihar Kano Rabaran Adeyemo A Sauel JP  alokacin da yake jawabi  ga manema labarai a ofishinsa Rebaran ya ce bikin Kirisimeti ba biki ne na shaye shaye ba, lokaci ne da Yesu Almasihu  ya koyar da kaunar juna da kuma salama. Yace duk wani kirista  na akika shi ne  wanda aduk lokaci yake kokarin koyi da kyawawan aabbubuwan da Yesu almasihu saboda haka ya bukaci duk wani mai biyayya da abin da littafi mai tsarki ya zoda shi ya zama wajibi ya tabbatar koyi tare da aiwatar da abubuwan da Yesu Almasihu ya koyar

Haka kuma Shugaban kuniyar Kiristoci na Jihar  Kano Reb Adeyemo  A Samuel JP  ya ba ya bayyana cewar  zuwan Yesu Almasihu Rahama ne kuma Albarka ne ga alumma, wanda kuma ke bayyana tsananin bukatar riko da bisa kauna da Salama saboda haka  bukuwan Kirsimeti na jaddadda fadar Yesu Almasihu  na samar ta tamaiko musamman Marayu da Masu bukata  ta musamman, saboda haka ake bukatar kai ziyara  ga ‘yan uwa wanda ni har masallachi  nake ziyarta.

Daya ke tsokaci kan batun hadin kai da zama kwabta lafiya akwai bakatar kawar da matsalar banbance banbance addini ko kabila sannan akaucewa yin magana akan abin da duk mutum bai da iliminsa ba saboda haka muna kara kira da babbar murya kan kara yiwa gwamnan Kano Addu’a musamman kan kokarin da ya ke na hada kan kowa da kowa musamman yadda ya gayyace mu taron shan ruwa aka ci aka sha tare, wannan ya tabbattar da irin aniyarsa na ganin ana tafiya da kowa.  Haka kuma shugaban ya yaba da kokarin da wata Kungiyyar mahaddata alkur’ani ta kasa wadda saboda kaunar hadin kan kasa ta karrama wasu manyan mutane a matakin kasa wadanda kiristoci ne ba  musulmi ba saboda gina makarantun tsangaya da suka yi alokacin da suke mulki, yace wannan ya tabbatar da cewa idan kowa ya fahimci haka an daina tunzura matasa da sunan addini suna tayar da husuma

A karshe Rebaran  Adeyemo A Samuel JP ya bukaci masu tukin ababan hawa da a ci gaba tuki cikin nutsuwa, sannan kua ya taya al’ummar Kirista da sauran jama’ar kasa murnar zagayyowar wannan rana mai Albarka da fatan za’ayi bukukuwan Kirsimeti lafiya

Exit mobile version