Kauran Bauchi Ya Kaddamar Da Kwamitin Sulhunta ‘Ya’yan PDP

A jiya Lahadi ne, dan takarar gwamnan jihar Bauchi a karkashin jam’iyyar PDP, Alhaji Bala Muhammad Kauran Bauchi ya jagoranci kaddamar da wani kwamitin dattawa mai mutane goma da za su sanya ido wajen sasantawa hadi da sulhunta dukkanin ‘ya’yan jam’iyyar da kuma aza tubalin jawo dukkanin wanda suka tabbatar zai basu gudunmawa a babban zaben 2019 da ke tafe a jihar ta Bauchi.

Ha kan na daga cikin yunkurin da jam’iyyar take yi na ganin ta samu nasarar kwace mulki daga hanun jam’iyyar APC a babban zaben 2019 da ke tafe.

A ya yin taron kaddamarwar, an gayyaci ‘yan takarar da suke neman kujerun daban-daban da suka hada da Sanatoci, ‘yan majalisun tarayya da na jahohi da suke cikin jam’iyyar, kana an kuma gayyaci wadanda suka yi takara a jam’iyyar wadanda Allah bai basu nasara ba, inda aka nemi hadin kansu domin kaiwa ga babban manufar da aka sanya a gaba.

Da yake jawabinsa a wajen kaddamarwar, Bala Kauran Bauchi ya shaida cewar sun yi ha kan ne domin ganin sun jawo kowa da kowa a jika domin cimma muradin da aka sanya a gaba, ya shaida cewar kowanne dan jihar na da gagarumin muhimmanci a garesu, a don haka za su tabbatar da janyo kowa a jiki domin tafiya tare.

Yake cewa, “wannan kwamitin da aka kafa domin sulhu tsa kanin ‘yan takarar da suka yi nasara da wadanda basu yi nasara ba zai kai ga ci gaban jam’iyyar, domin za a shawo kan wani gab da ke akwai.

“yanzu haka akwai sauran mutanen da suke wasu jam’iyyun da muke tattaunawa da su domin ganin an samu nasara, don haka aikinku ne wannan kwamitin ku jawosu cikin jam’iyyar nan,” Inji Kauran Bauchi Kaura ya shaida cewar adalci da jam’iyyar ta PDP ta yi wajen fitar da gwaninta ya kara mata farin jinni, inda ya shaida cewar dukkanin wadanda ba a yi musu adalci ba a jam’iyyar APC suna da cikakken damar da za su shigo PDP domin kwace mulki daga gwamna mai ci, “ku jawo kowa a jikinku domin a ceto jihar Bauchi. Daga cikin jam’iyyar nan da wajen jam’iyyar nan. mu kowa yana da muhimmanci a wajenmu,” Inji shi Daga bisani Kaura ya yi wa kwamitin addu’ar samun nasara wajen hada kan dukkanin ‘ya’yan jam’iyyar PDP da kuma janyo wasu daga wasu jam’iyyun zuwa cikin PDP.

Da yake tasa jawabin, shugaban kwamitin sulhu na jam’iyyar PDP da aka kaddamar, Sanata Bala Adamu Kariya ya yaba da samar da wannan kwamitin, yana mai shaida cewar Kauran Bauchi ya yi tunani mai zurfi wajen daukan mata kan da suka dace na shawo kan gibin da ke akwai, don haka ne ya sha alwashin cewar za su yi aiki tukuro domin gini jam’iyyar.

Yake cewa, “za mu yi aiki tukuro domin tabbatar da PDP ta zama dinkakkiyar gida. Za mu yi kokarin bibiyar dukkanin wadanda suka dace domin ci gaba. Hatta ‘yan sauran jam’iyyu ma, za mu bisu domin a hada kai don ceto jihar Bauchi,” Inji Kariya Ya shaida cewar jam’iyyar PDP ce kadai za ta iya yaki domin ceto jihar Bauchi daga cikin ukubar da ta tsinci kanta a ciki, yana mai bayanin cewar babu wanda zai yi sai su, don haka ne suka nemi hadin kan dukkanin wadanda abun ya shafa domin cimma nasara.

Wakilinmu ya shaida mana cewar kwamitin sulhu da daidaita ‘ya’yan jam’iyyar dai zai gudana ne a karkashin jagorancin Sanata Bala Adamu Kariya, (shugaba).

Sauran mambobin da suke ciki sun hada da; Tsohon shugaban PDP Alhaji Sule Doguwa, Bappa Haruna Disina, Shatiman Bauchi Alhaji Inuwa, Alhaji Inuwa Malamin Kasuwa, Alhaji Imamu Adamu Itas, Alhaji Lawal Darazo, Alhaji Yakubu Shehu Sarkin Dawakin Ningi, Alhaji Bako Akuyam, da sauransu Inda aka nada Alhaji Yusuf Garba ne aka nada a matsayin sakataren wannan kwamitin domin sasanta ‘ya’yan jam’iyyar ta PDP.

Ita dai wannan kwamitin sulhu da daidaitawar ta samu ne a karkashin dan takarar gwamnan jihar Bauchi a jam’iyyar PDP Alhaji Bala Kauran Bauchi, inda tunin suka fara aiki da zimmar neman kowanne dan PDP don tabbatar da ana tafiya a lema guda.

Exit mobile version