kwamared sanusi Mai lafiya">

Kawo Karshen Kashe-kashe A Arewa Ya Fi Kawo Karshen SARS

Sama da shekara biyu da suka gabata aka fara kawo maudu’in kawo karshen tsagin Rundunar Yan Sandan dake yaki da fashi da makami (SARS), sakamakon zarge-zarge da suka danganci cin zarafin al’umma da kisa. To amma kusan ba wanda ya ja hankali kamar na wannan lokacin bayan bayyanar wani faifan bidiyo da yake nuna yadda SARS din suke cin zarafi har ma da kisa. Hakan ya janyo zanga-zanga a jihar Lagos, inda kusan suka fi gabatar da ayyukan su, da kuma Babban Birnin Tarayya, wannan maudu’in me taken #EndSars ya sanya har wasu suka karkata hankulan su tare da goyon bayan wannan zanga-zanga. Yadda wasu manyan mawaka da sauran al’umma suka biyewa al’amarin, hakan ya sanya har aka dinga arangama tsakanin Yan Sanda da masu gabatar da wannan zanga zangar, babban abinda yafi jan hankalina a wannan al’amari, shine ganin yadda Shugaba Buhari da Mataimakinsa suka gayyaci Shugaban Rundunar Yan Sanda ta kasa don tattaunawa akan yadda za’a canza fasalin ayyukan SARS, banda kuma umarnin da aka basu na dena tsare mutane a shingayen duba ababen hawa. Wato dai alamu na zahiri sun nuna yadda hankalin Gwamnatin ya tashi akan wannan kiran da akeyi na rushesu daga hukumar yan sanda.
Tun ma kafin mu goyi bayan rushe ayyukan SARS, ko kuma barin su, mu kalli abubuwan da suke faruwa a Arewacin Kasar nan na kisan gilla da ake yiwa yan’uwan mu babu gaira babu dalili, tun daga Boko haram a Arewa maso gabas, zuwa jihohin Zamfara, Katsina, wasu yankuna na Sokoto, Kebbi da Jihar Naija, babu wanda zai iya kirga adadin rayukan da suka salwanta batare da sun aikata laifin komai ba. Zanga-zangar da aka gudanar a jihar Katsina ta nuna fushi akan abinda yake faruwa, muna ji muna gani yan sanda suka tafi da Shugaban Gamayyar Ƙungiyoyin Arewa Kwamared Nastura Ashir Sheriff wanda ya jagoranci wannan zanga-zangar, amma har kawo yanzu ana ci gaba da kisan sari ka noke a jihar ta Katsina, to amma yan Kudancin Kasar nan da suke ta wannan kumfar bakin a kawo karshen SARS, har an gayyaci IGP domin cika musu burikan su.
Da yawan lokutta na kan rasa wanda zan zarga tsakanin Shugaba Buhari ko kuma Jagororin mu na Arewa wanda zasuyi magana da yawun mu. A ranar juma’ar data gabata Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo shine ya jagoranci IGP gaban Shugaba Buhari, saboda ya isa yayi magana da yawun Ƴan Kudancin Kasar nan, musamman tunda dama shi tun a farko ya fara taka musu birki, to amma mu kuma mun rasa jajirtattun da zasu tsayar da duk ayyukansu domin ganin Shugaba Buhari ya karkata hankalin sa akan kawo karshen kashemu da akeyi har cikin gidajen mu. Idan har zamu rasa wanda zasu tsaya kai-da-fata akan damuwar mu, to tabbas watarana Arewa zata rasa duk ragowar tagomashin da take dashi, domin mun rasa masu tsayawa kai-da-fata akan share mana hawayen mu.
Bamu da inda yafi Nijeriya, sannan kuma bamu da inda yafi Arewa, ba inda muke kauna fiyeda wannan yanki namu. Amma muna ji muna gani an kakaba mana talauci, an hanamu ilimin zamani nagartacce, an kashe kasuwancin mu, sannan kuma ana bi gida-gida ana kashemu, wasu kuma ayi awon gaba dasu, kuma duka hakan yana faruwa ne a karkashin Gwamnatin Shugaban da yazo daga cikinmu. Shugaban Kasar da aka dinga mana gori, aka ci mutuncin mu saboda kawai munce mun gaji da Gwamnatin Mai Malafa(GEJ) sai mun canza. Yau gashi shekara biyar munata maimaita irin kiranye-kiranyen da muka dinga yi na matsalar tsaro a wannan yankin namu na Arewa.
Idan har zanga-zangar mutane irinsu Reno Omokri, Wizkid da Sowore zata sanya fadar Shugaban Kasa ta gaggauta gayyatar IGP domin amsa bukatun wadancan masu zanga-zangar, to mu me ake bukata muyi kenan? Ba wai fa ina goyon bayan abinda SARS suke bane, ko kusa ko kadan bana goyon bayan cin zarafin da suke yiwa al’ummar Kasa, to amma matsalar da take cikin gidana ta shafe wacce ake zargin rundunar da aka kirkira a shekarar 1992. Duniya ma tasan halin da Arewacin Kasar nan take ciki. Dubunnan al’umma ne suka gudu daga gidajen su saboda kawai su tsira da rayukan su, har kawo yanzu wasu shekara 11 da fara Boko haram basu san inda Ahalinsu suke ba, suna raye ko sun mace. Wasu a gaban idanunsu aka karkashe ahalinsu, duk yawan jami’an tsaron Kasar nan amma basu iya hana afkuwar hakan ba, amma kuma za’a iya tura jami’an tsaro akalla dubu talatin zuwa jihar da al’ummar ta basu wuce miliyan uku ba, saboda kawai ana tsoron rikicin zabe, amma kuma wasu tsirarun guraren da yan ta’adda suka mamaye suna girbar rayukan al’umma ya yiwa yan sandan wahalar shiga. Haka kuma duk biliyoyin kudaden da aka warewa bangaren tsaro da sunan kawar da yan ta’adda, har kawo yanzu ba’a samar da isassun makaman da jami’an tsaron zasu iya fada da waɗannan yan ta’adda ba, amma kuma an farantawa su Reno Omokri rai saboda kawai SARS suna kashe yan Yahoo-boys a jihar Lagos.
MU TASHI MU FARKA YAN AREWA.

Exit mobile version