Dakta Ibrahim Shehu Liman" />

Kayan Aro Ba Ya Rufe Katare!

08023703718 (TES Kawai )   ibrahimshehu781@yahoo.com

Kamar yadda kowace al’umma ta ke, al’ummar Hausawa da duka masu jibi da su, suna da kyawawan al’adunsu da suke tinkaho da su. A nan zai yi kyau mu waiwayi abin da ake nufi da al’adar jama’a kasancewar za a iya samun wadanda ba su fahimci abin da ake nufi da Kalmar ta ‘al’ada’. Kalmar wadda asalinta daga harshen Larabci take, tana da ma’anoni da dama. A wannan fage al’ada na nufin yadda al’umma tun tsirarta ta mince da wasu dabi’u, ko halaye, da hanyoyin gudanar da rayuwarsu, wadanda suka hada da tarbiyya da sarrafa harshensu, da ire-iren sutura, da sauran abubuwan da suka shafi rayuwar tasu.

Al’ummar Hausawa da duka masu alaka da ita a wannan kasa tamu ta Nijeriya, suna da kyawawan al’adun da sun dara na wasu al’ummomin, ko kuma a ce alal a kalla sai dai su yi kafada da na wasu basu gaza su ba.

Duk da yake tsarin zamantakewa ya tabbatar da cewa akan samu naso, ko tasirin wasu bakin al’adu a tsakanin al’ummomin da suka kusanci juna, ko ta hanyar wata al’umma ta iske wata, ko kuma duka su kasance a atre suka bakunci wuri. Abin da ake kyautata zato shi ne, kowace daga cikin wadannan al’ummomin zata yi kokarin riko da nata kyawawan al’adu, in ya so, sai ta ara, ta kuma yafa bakin al’adun da take ganin masu kyau ne, domin kuwa, ba wanda yake so a ce yana aiwatar da wasu miyagun al’adu, ko na wulakantar da kai, ko masu cutarwa.

Ko ta wani bangare aka yi kokarin nazari, za a tarar da Hausawa na da kyawawan al’adu. A nan zamu waiwayi yanayin zantukanmu, da tarbiyya da kuma sanya sutura a matsayin karar-gwaji.

A zantuka, wato yanaye-yanyen maganganun da aka san Hausawa da su, wadanda kuma ake sa ran su tabbata  a tsakanin manya, har zuwa yara, akwai wasu fitattun abubuwa kamar haka, babu miyagun zage-zage, babu batsa, babu kausasan zantuka, babu daga murya. Duk inda aka samu mutum na yin irin wadannan zatuka, ko dabi’u a lokacin da yake zamnce, akan ce yana yin zance wanda yake yasasshe! Abin mamaki, ko saboda rashin kwabo ne, ko kuwa saboda hulda da wadand aba su san irin wadannan halaye ba ne, sai a samun yawaitar wadannan yasassun zantuka. Allah ya kyauta.

Dangane da tarbiyya kuma, a al’adar Bahaushe, tun kafin bayyanar addinin Musulunci, har zuwa bayyanarsa, Hausawa suna da kyawawan dabi’u da suka tarbiyyantu da su, kuma sukan yi tarbiyyar ‘ya’yansu da duk wadanda suka jibancesu dasu. Irin wadannan halaye na tarbiyya sun hada da girmama manya, da tausaya wa kanana ko mara sa karfi, da kunya, da kara, da kyauta da saukin kai da kuma taimakawa juna. Tambaya dai a nan, ita ce, shin abin haka yake a yau. Idan haka yake, to madalla! Idan kuwa ana kuka, to da sake, kila jiya ta fi yau kenan.

Ta fuskar sutura kuma, tsiraici babban abin ki ne. inda ciken kyawawan halaye na karimci, akan yabi wanda ke iya ciyarwa da tufatar da mara sa wadata. Haka kuma ana Allah wadai ga masu yin shiga na homa, ato na alfahari don jin wai sun isa. Ba kamar yanzu ba da akan samu masu kudi kan rika yin almubazzaranci wajen sanya tufaffi na kece raini. A wajen matasa kumwa, samari kan rika yin sabulanci da sanya tufafin da bambancinsu da babu kadan ne. su kuwa ‘yanmata, abin sai Allah ya sawwaka, ba zamu ce Allah-wadai ba, domin tufafin nasu wasu kan zama fam-darinka tsirara, wato shaka-shaka, wasu kuma digilallu, wasu kuma irin abin da akan ce na wagairuhum ne.

To mu a nan, zamu yi kira ne da a waiwayi kayawawan al’adun ba kawai ta wadannan fuskoki da muka ambata ba, har ma da sauran al’adu da suke abin yabo da aka san al’ummarmu da su. A kul muka ce zamu rika koyi ko aron miyagun bakin al’adu. Kayan aro dai, an ce ba ya rufe katare!

 

Exit mobile version