Sameerah Bello Shinko" />

Kayan Da’a Na Mata: Illa Ko Amfani?

A wannan zamani dabarun mata na burge mazajensu a wurin kwanciya sun dauki wani sabon salo, in da suke amfani da wasu sinadirai walau na matsawa ko na sha, da a kan kira  da suna hakkin maye ko kayan da’a . Iren- iren wadannan magunguna a na amfani da su a kasashen Hausa da sauran kasashen Yammacin Afirka. Shin menene kayan mata? Wane amfani suke da shi? Me ya sa farin jininsu ya karu a ‘yan shekarun nan?  Hasashe ya nuna cewar wadannan magungunan ko hade-haden na iya saka maza cikin wani halin da ke iya mayar da su tamkar bayin matansu. Abin tambayar anya kayan matan na da wani tasiri kuwa? Da me ake hada kayan mata? Me ya sa suka bazu a ko ina? Anya suna aiki kuwa? Ko kuwa dabarun raba mata da kudadensu ne?

Wasu matan sun ce kayan matan na ba su damar mallake mazajensu, don su rika yin dukkan abin da su ke so. Sun ce amfani da wadannan magunguna na  saka mazan kara ganin darajar su. Su mayar da su yan gaban goshinsa; su mayar dasu sun fi nono fari; sun fi zuma zaki; kuma  sun fi turare kamshi.

A halin yanzu ba abin mamaki ba ne ka ga mata na sayar da kayan mata a shafukan sada zumunta kamar Instagram ko youtube, kuma abokan cinikinta na yabawa da tasirin kayan nata. Wannan rubutun zai karba mana tambayoyi da yawa a kan kayan mata.

MENENE KAYAN MATA?

Masana sun ce kayan matan wani hade-haden magunguna ne da ke samar da nishadi ga ma’aurata. Suna tayar da sha’awar mace,su kara mata ni’ima, ya kuma ba ta damar gamsar da mijinta a shimfida.

A ganin wasu hakan na taimakawa wajen zaunar da su daram a gidajen aurensu. Mata da yawa na ganin amfani da kayan mata ne kadai hanyar da za su bi su ji dadin aurensu, kuma su kanainaye mazajensu sai yadda suka yi da su.

A cewar mata da yawa dana tattauna da, sun ce akwai matukar amfani tattare da wadannan magunguna …. in da daya daga cikin amfaninsu shi ne kare mata daga kamuwa da cututtuka  da suka shafi mata,ko kuma warkar dasu gaba daya. Mata da yawa ganin suke  ba za ki kai ko a kira ki da cikakkiyar mace ba, in har ba kya amfani da kayan mata. Su na ganin dole mace ta kasance mai daddadan dandano don jawo hankalin mijinta a yayin auratayya.”Mace ba za ta taba jin dadi ko morar auren ta ba  in har ba ta gamsar da mijinta, kuma ta hanyar amfani da kayan mata hakan zai samu.” A cewar Innar Hauwa wata mai siyar da kayan da na zanta da ita.

Mata da yawa  su na ganin a duk lokacin da mace ta samu rashin jituwa da mijinta, to kayan mata ne za su dawo mata da zaman lafiya a cikin aurenta, na tabbata mata da yawa na ganin haka abin yake. Amma abin tambayar a nan akwai wasu dalilai da ke saka mata fara amfani da kayan mata?

DALILAI DA KE SAKA MATA AMFANI DA KAYAN MATA

  1. Iyaye mata: Wasu matan kan yi amfani da kayan da’a sakamakon shawara daga iyaye mata ko kuma koyarwar iyaye mata. A kasar Hausa wasu iyayen duk lokacin da ‘yarsu za ta yi aure, sai sun shirya ta, wato su dafa ta, ta hanyar dura mata jike-jike,shaye-shaye ,shafe-shafe ko kuma yin turare-turare da kayan da’a,hakan kan dore wani lokaci har bayan aure, a jika wannan, a kuma shafa wancan, har hakan ya zame musu jiki.
  2. Kawaye : Mata kan zauna hirar yadda al’amuran rayuwar aurensu take garawa, ciki kuwa har da yadda suke gudanar da kwanciyar aure. Ta wannan hanyar matan kan labarta amfani da kuma aikin da kayan da’a suke yi musu yayin gabatar da kwanciyar aure.

Ta nan matan da ba sa amfani da kayan da’a, sai su shiga amfani da su, suma su ji abin da a ke ji, ko kuma su burge mijinsu, ko dai su samu daraja da daukaka a wajen mazajensu kamar masu basu labarin.

  1. Kishi:Wasu matan na amfani da kayan da’a don son fita daban daga sauran mata, musamman ma idan mijin yana da mata sama da daya. Wannan sai ya sanya su shiga amfani da kayan , duk don mijin ya ba su wani fifiko da daraja daga cikin matansa.

Shin da amfani da rashin amfanin kayan mata wane yafi rinjaye? Daga tattaunawar da na yi da kwararru, na gano wasu abubuwa kamar haka:

ILLOLIN KAYAN DA’A

Sakamakon ziyarce-ziyarcen zuwa asibitoci hade da kuma tambayar wadanda abin ya shafa kai-tsaye da kuma sauran nazarce-nazarce da bin diddigi da na yi, sai na fahimci cewa, amfani da kayan daa na da illoli ga wadanda suke amfani da su. Irin wadannan kayan matan na iya janyo wa matan da ke amfani da su matsalolin kiwon Lafiya, ko zamtakewa da mazajen su. Likitoci sun bayyana irin matsalolin da mata masu amfani da kayan mata ke fuskanta da suka hada da cututtuka. Sun kuma bayyana yadda hadin magunguna ke iya yin illa ga farjin mace, ya barnata jikin nata, musamman irin wanda a ke saka shi cikin jiki.

Kadan daga Illolin da suke haddasawa sun hada da:

  1. kaikayin Gaba da : Sakamakon amfani da kayan da’a, musammman ma na matsawa da na Turare da wasu matan kan yi, sai hakan ya haifar musu da kaikayin gaba. Sukan matsa ko saka sinadarin kayan daa a al’aurarsu, ko kuma turara al’urar tasu, wanda a karshe maimakon hakar ta cimma ruwa, ta hanyar samun biyan bukata, sai cibi-ya- zama-kari ta hanyar samuwar kaikayin gaba. Wanda i dan suka zauna ba abin da za ka ga su na yi sai sose-soshe.
  2. Zubar Ruwa Daga Al’aura: Sakamakon amfani da kayan da’a na matsi da na turare, wasu matan hakan kan haifar musu da zubar ruwa mai doyi daga al’aurarsu. Wanda zai dinga bata musu dan kamfai, ka ji suna wari mai tayar da hankali.
  3. Barin Ciki: Amfani da kayan mata yana kawo barewar ciki, saboda shan maganin ake ba wani kaida ko ma’auni, kuma wasu maganin suna da karfi sosai da za su hana ciki zama a mahaifa.

 

Exit mobile version