Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home NAZARI

Kayan Da’a Na Mata: Illa Ko Amfani? (3)

by Muhammad
February 21, 2021
in NAZARI
5 min read
Mata
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Sameerah Bello Shinko, 08025729364:

  1. Hana daukar Ciki: Wasu maganin saboda karfinsu su kan bata mahaifa, ko kuma toshe in da kwai ke fitowa sai kaga macce ta kasa daukar ciki.
  2. Cutar Kansa: amfani da kayan mata barkatai yak an haifar da sankarar mahaifa (uterus cancer), wanda wani lokaci zai iya kai ga macce ta rasa mahaifarta ko kuma rayuwarta gaba daya.
  3. Cutar Hawan Jini ko saukar jini: Sakamakon amfani da kayan mata na sha na haifar da matsalar hawan jini ko saukarsa. Kasancewar jini hanyar tafiyar da abinci, ruwan da muka sha, da magungunan da muka sha. Dan haka idan kayan matan na dauke da wasu sinadarai masu lahani ga shi jinin, ko kuma aka yawaita amfani da su, sai hakan ya kawo hauhawar jini ko saukarsa.
  4. Matsanancin Ciwon Kai: Kayan mata na janyo matsanancin ciwon kai, zafin jiki. Kamar yadda wasu matan suka masu amfani da kayan suka fada min, wannan baya rasa nasaba da karfin da maganin ya musu a jini.
  5. Ciwon Zuciya: Amfani da kayan mata na haifar da ciwon zuciya, kasancewar magungunan da matan kan sha yana samun damar zaga jikinsu ne, ta hanyar zagaya sassan jiki da jini ke yi. Kuma da ma zuciya ita ta ke da hakkin harba jini izuwa kowane sashi na jikin dan Adam, sannan bayan jini ya gama zagaye jikin, yakan dawo zuwa zuciya. Kamar yadda na yi bayani a sama, cewa kayan da’a na kunshe da sinadarai da suke da lahani ga jini, don haka idan bayan jini ya kwashi wadannan sinadarai, ya zaga jiki da su, sannan ya dawo zuwa zuciya, hakan sai ta sanya taruwar wadannan sinadarai a zuciya, in da a nan sai ka samu sun haifar da ciwon zuciya, imma a samu kumburar fatar da take bada kariya ga zuciya wato, ko kuma haifar da nakasu ga ita zuciyar wajen harba jini zuwa ga sassan jiki.
  6. Ciwon Hanta: Kamar yadda bayani ya gudana, wadannan kayan mata su na dauke da sinadarai masu lahani ga jikin dan Adam. Jikin mutum ya na dauke da wasu gidaje da suke da hakkin tace abin da ke shige da fice da kuma zuwa da komayya a cikin jikin dan Adam. A cikin wadannan gidaje akwai hanta, wacce ita take da hakkin bincike wajen tantance sinadaran da jini ya kunsa, don haka idan akwai sinadaran da suka yi wa gangar jiki lahani, sai ta tace shi, don haka idan suka yi yawa, sai ya haifar da ciwon hanta.
  7. Haihuwar yaro ba lafiyayye ba: yawan amfani dasu musamman ga mai juna biyu na iya saka a haifi yaro da wata tawaya ko rashin Lafiya a tattare da shi.

Ta bangaren mu’amala da zamantakewa kuma, mata kan fuskanci matsaloli kamar haka:-

samndaads
  1. Cire wa miji sha’awar matarsa: Da zarar magunguna da aka yi wa mace kafin ta shiga gidan mijinta ya gushe, to ni’imarta zai ragu da kashi 80% sai na asali da take da shi ya dawo, shi kuma miji ba zai dinga jin tana gamsar da shi kamar da ba. Daganan sha’awa da yake mata zai fara raguwa, idan aka yi rashin sa’a sai ma ya haifar masa da sha’awan wasu mata a waje.
  2. Gusar da ni’imar mace na asali da take da shi: Duk macen duniya, akwai ni’imar da Allah ya mata wajen gamsar da namiji, amma irin ni’imar kayan mata na iya haifar masu da illa wajen gusar da ni’imar da suke da shi na asali. Domin da zarar wannan aikin wanan magunguna da suka gushe, to ni’imarta na asali da take da shi ma zai ragu.
  3. Rashin tattali da tanadi: mata da yawa da suka saba siyen kayan basu da tanadi ko ttattali, dan a kullum tunanin su yanda za su samu kudin siyen kayan matan ne, dan haka komai suka samu ko tara a can suke karewa.
  4. Sabo: akwai abinda bature ke kira ‘addiction’, mata da yawa sun saba da amfani da kayan mata da har ya saka basu iya komai sai sun yi amfani da su.

Bincikena bai tsaya a nan ba sai da na tintubi malamai na ji meye hukuncin amfani da irin wannan maganin a wurin matan. Kuma sun mana bayani kamar haka:

  1. Idan hard a halastattun abubuwa aka hada maganin, kuma baza su cutar da mijinta ba ko abokiyar zamanta ba; toh hakan ya hallata, ba laifi.
  2. Idan an hada da shirka, ko abinda bai hallata a yi amfani da shi ba a addini, ko kuma zai iya cutar da mijin ko abokiyar zama idan akwaita. To wannan ya haramta amfani da shi.

Sai dai bincikena yana nuna da yawa maganin da ake amfani da shi a zamanin nan ana kaucewa wani lokacin har da shirka saboda kawai neman biyan bukata. Mafi akasari ma zaka ji harda najasa ake hadawa wurin hada maganin. A tattaunawa ta da wani matashin Malamina mai suna Malam kabir, ya baiwa mata shawara kamar haka:

Yawan Shan ‘ya’yan itatuwa da ganye, madara da irinsu nama da kifi suna gyarawa macce zamantakewar aurenta sosai. Haka ma magungunan Musulunci da aka samu ingancin warakarsu daga Manzon Allah SAW, irin su zuma, habbatus sauda, zaitun da sauransu. Wannan za suna kawowa macce lafiyar jiki da ta ruhi gaba daya wajen sanya ni’ima. Da wannan za ki iya gyara zamantakewar auren, kuma ba boka ba malam ki mallaki  kin sauki.

KAMMALAWA

A karshe dai ina so na ja hankalin mata masu amfani da kayan mata da su hankaltu da irin illolin da amfani da su ke janyowa. Wadanda ba sa amfani da wadannan magunguna su auna amfani da rashin amfanin su kafin su fara. Har ila yau ina so na yi kira ga iyaye mata da su sani cewa shirin nan da su ke yi wa yayansu ta hanyar amfani da kayan mata kafin su aurar dasu, yana da matukar hadari ga rayuwar yayansu, maimakon su zama mowar mata ko yan lelen mazajensu, kamar yadda suke buri, sai labari ya sauya, wato su koma borar mata.

A fannin mazaje ina so su fahimci kowane dan Adam da yadda Allah Ya halicci shi a dangane da shaawa da kuma yanayin juriya yayin gudanar da kwanciyar aure, don haka goranta wa mata, zai sa su aikata abubuwan da karshe zai haifar da da-na-sani ne.

Sannan ga mazajen da matansu suka kamu da cututtuka sakamakon amfani da kayan mata, kada su guje su, su gane a dalilin faranta musu da neman burge su matan nasu suka samu kansu a wannan halin. Don haka su rungume su, ta hanyar tashi tsaye har sai an shawo kan matsalar.

Labarin ba dadin ji; wani lokacin idan mace ta kurbi wani hadi, kawai kamar sihiri, sai mijinta ya zama tamkar wata tinkiya, ke kuwa kin zama wata sarauniya Daga nan kin mallake shi, kin kuma zame wata  Kina ganin kin cimma bukatunki ko? Kina ganin babu wani laifi tun da ai mijinki ne ko? Komai lafiya lau ko? Muji tsoron Allah a komai muke, mu kaucewa shiga hakkin wasu. Ba zan yi dai kasa a gwiwa wajen kira ga mata wadanda kishi ke sanya su amfani da kayan ba, da su sassauta kishi, su kuma yi kishi irin na matan manzon Allah (SAW).

SendShareTweetShare
Previous Post

Satar Dalibai Ko  Kassara Ilimi A Arewa?

Next Post

Noman Bana: Ci Biyu A Gonar Dadin Kowa, Masara Sau Biyu Shinkafa Sau Biyu

RelatedPosts

Dan Uwan Minista

Ayyukan Ta’addanci A Arewacin Nijeriya

by Sulaiman Ibrahim
3 days ago
0

Ga duk mai tabaraun hangen nesa, zai fahimci cewa lallai...

Sarkar Da Za Ta Sarke Kaduna Bayan Amsar Bashin Dala Miliyan 350 Daga Bankin Duniya

Sarkar Da Za Ta Sarke Kaduna Bayan Amsar Bashin Dala Miliyan 350 Daga Bankin Duniya

by Sulaiman Ibrahim
4 days ago
0

Daga Dr. Nasiru Aminu “Babu al’ummar da za ta kasance...

National Economy

Shekara Daya Da Fara Fitowa: Gudumawar Jaridar NATIONAL ECONOMY Ga Tattalun Azikin Nijeriya

by Muhammad
1 week ago
0

Daga Khalid Idris Doya, A jiya Asabar ne jaridar NATIONAL...

Next Post

Noman Bana: Ci Biyu A Gonar Dadin Kowa, Masara Sau Biyu Shinkafa Sau Biyu

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version