Al’umma Badawa da ke cikin Karamar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano sun bukaci Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta sake gina ajujuwan makarantar Sankandiren ‘yan mata ta unguwar Badawa da Gobara ta kone a cikin makon da ya gabata.
Gobarar wadda ta tashi da misalin karfe 1:00 na safiya a ranar litinin 25 ga wtan marcis shekara ta 2019 data gabata, wadda ta kone ajujuwa, dakin gwaje gwaje da dakin karatu (liabry), lokacin da wakili Jaridar leadership a yau Lahadi ya ziyarci makarantar ya rawaito cewa al’ummar
unguwar ta Badawa sun gudanar da addu’o’i domin neman tallafin ubangiji domin kare faruwar haka nan gaba. Dagacin Badawa Zakariyya Garba ya bayyanawa Jaridar leadership ayau Lahadi cewar gobarar ta fara ne da misalin karfe 1:00 na safiyar Litinin lokacin da jama’a ke tsaka da barci, ya ci gaba da cewar gobarar ta kone ajujuwa da dakin gwaje gwaje wanda aka cika da kaya da kuma wani dakin karatu Liabry.
Alhaji Zakariyya Garba yace wuraren da gobarar ta kone wanda suka kai kimar Naira Miliyon 172 wanda kamfanin Maltina da kuma kamfani samar da man fetur na Esso suka gina domin bayar da tasu gudunmawar ga cigaban al’umma. Don haka sai ya bukaci Hukumomin Kananan Hukumomi da gwamnatin Jihar Kano da daidaikun mutane su kawo dauki domin ganin daliban wannan yanki sun ci gaba da karatunsu. Tsohon shugaban kugiyar iyaye da malaman Makarantar Muhammad Makaye shima ya bukaci Gwamnatin Jihar Kano ta kawo masu dauki ta hanyar sake ginin wurare da gobarar ta lalata wanda yanzu haka dalibai ke ci gaba da zama a gudajensu sakamakonr ashin wuraren karatu. Musamman ganin cewa yanzu an kusa fara jarrabawa kuma makaratar bata da wani wurin gudanar da gwaje gwaje wanda a halin yanzu daliban wannan makaranta na maleji ne a wata makarantar firamare.