CRI Hausa" />

Kayayyakin Kandagarkin COVID-19 Da Sin Ta Samar Sun Isa Kasashen Afirka

A cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, labarai game da gwamnatin kasar Sin ta tura tawagoyin likitoci zuwa kasashen Afirka domin samar da tallafi gare su yayin da suke kokarin kandagarkin cutar numfashi ta COVID-19 sun fi jawo hankalin al’ummun kasa da kasa, kana labaran dake shafar tallafin kayayyakin likitancin da gwamnatin kasar Sin da kamfanonin kasar suke samarwa ga kasashe daban daban na Afirka su ma sun burge al’ummun kasashen nahiyar matuka.

A ranar 17 ga wata, a kasar Sudan ta kudu, kayayyakin kiwon lafiya da kamfanonin kasar Sin suka samar a karo na biyu sun isa filin jiragen saman kasa da kasa na Juba.
A madadin ministan harkokin wajen kasar Sudan ta kudu, jakadan kasar dake wakilci a kasar Sin John Andruga Duku ya nuna babbar godiya ga kasar Sin saboda take samar da tallafi ga aikin kandagarkin cutar COVID-19 a kasarsa, inda ya bayyana cewa, kasar Sin tana samarwa kasar Sudan ta kudu da sauran kasashen Afirka goyon baya mai karfi yayin da suke kokarin shawo kan annobar, lamarin da ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin da al’ummun kasar suna dora muhimmanci matuka kan huldar dake tsakaninta da kasar Sudan ta kudu da kuma huldar dake tsakaninta da daukacin kasashen Afirka.
A ranar 17 ga wata, a kasar Sao Tome and Principe, an shirya bikin mika kayayyakin kandagarkin cutar COVID-19 da gwamnatin kasar Sin ta samar ga gwamnatin tsibirin Sao Tome and Principe a Sao Tome, fadar mulkin kasar, inda ministan lafiyar kasar ya bayyana cewa, an kara fahimtar ma’anar zumunta yayin da ake fuskantar wahala, kayayyakin da kasar Sin ta samarwa kasarsa suna da muhimmanci kwarai, lamarin da ya sake shaida cewa, ya kasance dadadden amincin dake tsakanin al’ummun kasashen biyu, kana ya yabawa kasar Sin saboda taimakon da ta samar ga Sao Tome and Principe yayin da take yaki da cutar malaria da sauran fannoni.
Kullum sassan biyu wato kasar Sin da kasashen Afirka suna maida hankali sosai kan bukukuwan mikawar kayayyakin kandagarkin cutar COVID-19 da aka yi jigilarsu daga kasar Sin zuwa kasashen Afirka, wadanda suka samu halartar jakadun kasar Sin dake kasashen da manyan jami’an lafiya da manyan jami’an harkokin wajen kasashen Afirka.
Kwayar cutar tana shafar daukacin kasashen duniya, kuma abokiyar gaba ce ga daukacin bil Adama, muddin dai kasar Sin da kasashen Afirka suka hada kai, to hakika za su samu nasarar ganin bayan cutar cikin hanzari. Hakika wannan ba shi ne karo na farko ba da sassan biyu suke yin hadin gwiwa domin yaki da annobar, a shekarar 2014, yayin da annobar Ebola ta yadu a kasashe uku dake yammancin Afirka, kasar Sin ta tura tawagogin likitoci zuwa kasashen domin samar da tallafi gare su, a bayyane an lura cewa, ya kasance dadadden aminci iri na ‘yan uwa dake tsakanin sassan biyu.
Wasu masanan dake nazarin huldar Sin da Afirka sun yi nuni da cewa, kasar Sin tana samar da tallafi ga kasashen Afirka gwargwadon karfinta, yayin da suke kokarin dakile annobar COVID-19, lamarin da ya nunawa kasashen duniya cewa, a matsayinta na babbar kasa a duniya, kasar Sin tana sauke nauyin dake bisa wuyanta, hakan ya nuna cewa, kasar Sin da kasashen Afirka suna gina kyakkyawar makomarsu tare.(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)

Exit mobile version