Sulaiman Bala Idris" />

Kazafi Ga Buhari: Kotu Ta Ki Aminta Da Bukatar Atiku

A jiya ne wata babbar kotu dake zama a Babban birnin tarayya, Abuja ta ki aminta da bukatar tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar na son kotun ta yi watsi da neman diyyar miliyan 40 da shugaban kasa da iyalinsa suka shigar suna zarginsa da laifin kazafi.

Tun farko dai, a karar wacce Mallam Gidado Ibrahim ya shigar, ya sanar da kotu cewa Atiku da kakakinsa sun yi kazafi ga Shugaba Buhari, wanda kuma suka dauki nauyin wallafa wannan kazafi a wasu jaridu a ranar 27 ga watan Disambar 2018 don su yaudari al’umma. Inda ya nemi kotu da ta tilastawa wadanda ake kara su biya su diyyar naira miliyan 30, don abin da suka wallafa din a jaridu ya sa dole masu kara sun kashe kudade makudai don warware wannan kazafi da suka yi. Mai shari’a Binta Mohammed ta yi hukunci da cewa, ya sabawa sashe na 36 na kundin tsarin mulkin 1999, tare da ra’shin adalci matukar a ka yi watsi da wannan kara da Shugaba Buhari ya shigar.

A dalalin haka ne kotun ta amince da ci gaba da sauraren shari’ar, ta kuma umurci lauyan masu kara da ya rubuta rubutaccen jawabin bukatarsu da kuma shaidu. Kotun ta dage shari’ar zuwa 9 ga watan Yunin 2020 domin fara sauraron shaidu.

Idan dai ba a manta ba, tawagar lauyoyin Atiku karkashin jagorancin Chukwuma-Chikwu Ume SAN a ranar 21 ga watan Fabrairun 2019 ta nemi kotun da ta yi watsi da shari’ar domin ba su bi ka’idojin da aka tanadar ba.

Sai dai lauyoyin masu kara sun bayar da kariya da cewa, sun yi gyara ta hanyar biyan kudaden chaji na lattin da suka yi.

A jiya dai kotun ta bayyana cewa za a ci gaba da sauraron wannan shari’ar, ba za ta yi watsi da ita ba.

A hukuncinta, wanda ta zare sunan kungiyar BCO, Mai Shari’a Mohammed ta shigar da sunan Gidado Ibrahim a matsayin wanda zai tsayawa iyalin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Exit mobile version