Sulaiman Bala Idris" />

Kazafi Ga Buhari: Rashin Halartar Lauyoyin Atiku Ya Kawo Tsaiko A Shari’arsa Da BCO

Sauraren shari’a kan karar cin zarafi da aka shigar kan tsohon mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya hadu da tarnaki sakamakon rashin halartar lauyoyin Atikun jiya a gaban kotu.

Kamar dai yadda aka sani ne, babbar kotun babban birnin tarayya, Abuja wanda ke karkashin mai shari’a Binta Mohammed ya sanya jiya 25 ga watan Fabrairun 2020 ne domin ci gaba da sauraren shari’ar, inda sakamakon rashin halartar lauyoyin Atikun, ya sa Mai Shari’ar ta sake dage shari’ar zuwa ranar 17 ga watan Maris din 2020.

A shari’ar wacce aka shigar ranar 22 ga watan Janairun 2019, masu karar sun bukaci kotu da ta tilastawa Atiku biyan  diyyar Naira miliyan 40 bisa zargin cin zarafin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da iyalinsa, inda ya ce, suna da wani kaso na hannun jari a kamfanonin 9mobile, da bankin Keystone.

A hukuncinta, wanda ta zare sunan kungiyar BCO, Mai shari’a Mohammed ta shigar da sunan Gidado Ibrahim a matsayin wanda zai tsayawa iyalin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wannan ya biyo bayan ankararwar da lauyan mai kara, Abdulrazak Ahmed ya yi ga kotun na bukatar a sa wanda ake kara ya gabatar da takardar kariya, da kuma gabatar da shaidu.

Tun farko dai, a karar da Daraktan Sadarwa da tsare-tsaren BCO, Mallam gidado Ibrahim ya shigar, mai karar ya sanar da kotu cewa Atiku da kakakinsa sun yi kazafi ga Shugaba Buhari, wanda kuma suka dauki nauyin wallafa wannan kazafi a wasu jaridu don su yaudari al’umma.

Haka kuma kungiyar ta BCO ta nemi kotu da ta tilastawa wadanda ake kara su biya su diyyar naira miliyan 30, don abin da suka wallafa din a jaridu ya sa dole masu kara sun kashe kudade makudai don warware wannan kazafi da suka yi.

A jiya Talata, bangaren masu kara sun halarci kotun a shirye, sai dai su kuma masu kare kai ba su halarta ba.

Haka nan kuma masu kare wadanda ake kara sun ki rubuta jawabin kariya kamar yadda kotu ta umurce su da su aikata cikin kwanaki 14.

Yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan dage shari’ar, lauyan wanda ke kara, A. Ahmed ya ce: “An dage sauraron shari’ar zuwa ranar 17 ga watan Maris din 2020. Ba mu ga korafin da lauyin da ke kare wanda ake kara suka rubuta ba ballantana mu san me ya kumsa, amma dai na sanar da magatakardan kotun cewa, dole ne mu ga wannan takardar korafi cikin wannan makon. Duk da sun rubuta takardar korafi, ko da ba su shiryawa shari’ar ba, ya kamata a ce sun halarci zaman kotun don su sanar da mu dalilin da ya sa suka rubuta takardar korafin.

“Kuma ba su ma rubuta jawabin kriya ba. Ya kamata a ce suna kotu, domin jiya ne alkali ta sa ranar sauraron shari’ar, kuma an sanar da su hakan. A zama na gaba idan suka ki zuwa, za mu bukaci alkali da ta soke korafinsu, ta ci gaba da shari’ar domin mun fahimci kokarin haifar da tsaiko suke yi. Za mu kawo shaidunmu a ranar 17 ga watan Maris domin a fara sauraron shari’ar.” Inji lauyan.

 

Exit mobile version