Sayyadi Ismail Umar Mai Diwani">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAUSAYIN MUSULUNCI

Kebance-kebancen Manzon Allah (SAW) I

by Sayyadi Ismail Umar Mai Diwani
January 1, 2021
in DAUSAYIN MUSULUNCI
5 min read
Kebance-kebancen Manzon Allah
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

A uzu billahi minas shaidanin rajim. Bismillahir rahmanir Rahim. Wa Sallallahu ala Nabiyyil Karim. Masu karatu assalamu alaikum warahmatullahi ta’ala wa barkatuh.

Kwana biyu mun yi karatun cewa duk wani abu da Allah ya ba Annabawa, Allah ya ba Annabi Muhammadu (SAW) irinsa, sannan shi kuma Allah ya kebance shi da nasa shi kadai wanda bai ba Annabawa ba. Imamu Suyudi ya yi littafin Khasa’isul Kubra wanda a ciki sai da ya kawo abubuwa dubu da Allah ya ba Annabi Muhammadu (SAW) shi kadai.

samndaads

Shehu Sukairajul Ayyashi, shi ma ya fitar da Khasa’isu (kebance-kebance) na Annabi (SAW) guda dari biyar. Shehunmu Yusufun Nabahani shi ma a cikin littafinsa Anwarul Muhammadiyya ya fitar da wani abu daga cikin abubuwan da Manzon Allah (SAW) ya kebanta da su shi kadai wanda a ciki za mu dora karatunmu a kai, in sha Allahu.

Nabahani yake cewa, yana daga abin da Manzon Allah (SAW) ya kebanta da su na daga Mu’ujizozi da abubuwan da Allah ya daukaka Manzon Allah da shi a kan sauran Annabawa na daga girmamawa wadanda sun fi rana fitowa a fili. Allah ta’ala ya kebanci Annabi Muhammadu da abubuwan da bai taba ba wani Annabi da ya zo kafin shi ba (SAW). Haka nan duk abin da aka kebanci wani Annabi da shi sai ka ga an bawa Annabinmu irin nasa. Idan an ce an ba wa Annabawa Annabta, to Annabinmu (SAW) an ba shi wannan Annabtar tun Annabi Adamu (AS) yana tsakanin rai da yunbunsa (tun kafin a busa masa rai), amma kowane Annabi sai da ya zo a zamaninsa tukuna sannan aka ba shi Annabtar, idan Manzo ne kuma sai lokacin aikensa ya yi ake ba shi Manzanci. Galibi ma sai sun cika shekara arba’in da haihuwa kafin a ba su, amma Annabinmu (SAW) tun Azal aka ba shi Annabta. Yayin da aka ba Annabi (SAW) wannan matsayi, sai muka san cewa shi ne yake wa dukkan halitta madadi kuma ya kasance cikakke (a wurin Allah) tun kafin a yi su (Annabawa).

Yana daga Mu’ujizarsa, Kur’aninsa ya tattare dukkan komai. Ya tattare duk littattafan Annabawa, ka ga wannan ya fi ban mamaki. Kuma Allah ne da kansa ya jibinci kiyaye Kur’anin Manzon Allah (SAW); ba wanda ya isa ya canja shi, ba wanda ya isa ya cire wani abu daga ciki. To wannan babbar Mu’ujiza ce ta Manzon Allah (SAW). A yau duk duniya babu wani littafi da ya kai Alkur’ani yawa. Kowane gida na Musulmi sai ka ga akwai Alkur’ani har ma da gidan wasu da ba Musulmi ba yanzu.

A zamani da yawa, wadanda ba Musulmi ba sun yi wa Alkur’ani hidima. A lokacin da Hijirar Manzon Allah take da wajen shekara 500, Kasar Jamus ta buga Kur’ani. Ta rubuta shi ta wallafa shi. Musulmi suka tashi suka nuna rashin yarda, sai kasar ta ce ga Kur’anin da ta wallafa Musulmi su duba, duk inda suka ga ta bata su yi mata magana. Aka tashi Malaman duniya na wannan lokacin suka tafi Jamus suka duba suka ga an rubuta shi lafiya kalau komai ya fita. Malaman suka ce a ba su su kawo Makka, Jamus ta ce ba za ta bayar ba; za ta ajiye shi a gidan tarihi.

Bayan hidimar da Jamus ta yi, ba a kuma yin shekaru 100 ba ita ma Rasha ta buga Kur’ani. Rubutu lafiya kalau da komai. Nan ma Malaman Musulunci suka tashi suka tafi kasar suka duba, suka ga komai lafiya kalau, suka nemi a ba su su tafi da shi, Rasha ta ce ba za ta bayar ba; za ta ajiye a gidan tarihi. Ba a kuma yin wata shekara 100 da faruwan haka ba, ita ma Andulus (Spain) ta rubuta nata. Ba a dade ba sannan ita kuma Turkiyya ta samu injin wallafa Kur’ani. Ba a yi shekara 100 da fara wallafa na Turkiyya ba; ita ma Iran ta samu injinan rubutawa ta fara nata. Sai da aka zo 1900 sannan Kasar Misra ta fara rubuta Kur’ani, daga nan ne abin (wallafa Kur’ani da na’ura) ya zo hannun Larabawa.

Iran Musulmai ne amma kabilar Farisawa. Turkiyya Musulmai ne amma kabilar Turkawa, duk gabadayansu ba Larabawa ba ne. A 1900 da Misra ta fara wallafawa ne sai abin ya yawaita, tana rubutawa Kur’anin yana shiga sauran kasashen Musulmi. Amma ita kasar da aka saukar da Kur’anin ma, watau Makka sai wajen 1960 da wani abu sannan ta fara; zamanin Fahad. To ka ga, Kur’ani lamarin Allah ne.

Kuma kwanan nan ma, kamar fiye da shekaru biyar da suka gabata, Rasha ta rubuta Kur’ani da ruwan Zinare. Kuma na Sayyidina Usman (RA) din nan ta dauko ta rubuta da ruwan Zinare. Yau akwai irin su a Indiya amma kuma irin na Rasha sun dauwara shi ya fi na Indiya. Kuma aka sa Kur’anin a cikin motar shugaban kasa na Rasha da ministocin kasar aka kewaya babban birnin kasar da shi tare da malaman Az’har da wasu daga cikin Musulmi. Sannan Rasha ta yi masa gidan tarihi na daban, wannan duk yana nan a rubuce.

To kun ga mun gode Allah. Kur’ani Mu’ujiza ce na Manzon Allah. Allah kuma ya ce shi zai kiyaye shi kuma yana kiyayewa din. Babu wanda zai canza wani abu na Kur’anin domin yin hakan ma ridda ne. Su kansu Turawan da wasu ke tunanin ko sharrinsu zai shafi Kur’anin su da kansu suna kiyaye shi, suna kuma kula da tarihinsa.

Muna da Tafsirin da wani Bature Dan Amurka ya rubuta, ba ma Musulmi ba ne. Sai da Sarki Faisal (na Makka) ma ya ba shi kyauta. Shi kawai ya rubuta ne saboda ya ji wasu na cewa Kur’ani ba littafin Allah ba ne, na wani mutum ne a Sahara amma kuma yana tafiya da Technology (fasahar kimiyya ta zamani). Old Testament da New Tastament (Bible) su ne littafan Allah amma kuma ba su tafi da Techonology ba. Wannan ne dalilin da ya sa ya je Az’har ta Misra ya haddace Kur’anin, sannan ya yi karatun Larabci ya haddace Alfiyatu bin Malik. Sannan ya yi karatun bangaren Tafsiri sai da ya haddace su Dabari har ma yana cin gyaransu yana cewa don ba su zo a zamanin nan ba ne, sun fassara aya kaza da kaza sun yi kokari amma don Allah bai kawo su a lokacin jirgin sama ba ne, da sun ce ayar (da yake magana a kai) tana nufin jirgin sama ne, to mun gode Allah. Wannan Mu’ujizar Manzon Allah (SAW) ce.

SendShareTweetShare
Previous Post

Jawabin Shugaban CMG Na Murnar Sabuwar Shekarar 2021 Ga Masu Sauraro Da Masu Kallo

Next Post

Shawarata Ga Matan Gida Da Ba Su Yin Sana’a – Hassana Hamisu

RelatedPosts

kebance

Kebance-kebancen Manzon Allah (SAW) II

by Sayyadi Ismail Umar Mai Diwani
1 week ago
0

Daga Sayyadi Ismail Umar Mai Diwani, Masu karatu assalamu alaikum...

Annabi Isah

Mu’ujizozin Annabi Isah (AS) Da Aka Bai Wa Annabi (SAW) Har Da Kari (II)

by Sayyadi Ismail Umar Mai Diwani
3 weeks ago
0

Tare da Sayyadi Ismail Umar Mai Diwani, Bismillahir rahmanir Rahim....

Mu’ujizozin Annabi Isah (AS) Da Aka Bai Wa Annabi (SAW) Har Da Kari (I)

Mu’ujizozin Annabi Isah (AS) Da Aka Bai Wa Annabi (SAW) Har Da Kari (I)

by Sayyadi Ismail Umar Mai Diwani
1 month ago
0

Mu’ujizozin Annabi Isah (AS) Da Aka Bai Wa Annabi (SAW)...

Next Post
Hassana Hamisu

Shawarata Ga Matan Gida Da Ba Su Yin Sana’a – Hassana Hamisu

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version