Umar Faruk" />

Kebbi 2019: Mutum Biyar Da Ke Hararar Kujerar Gwamna Bagudu

Yayin da guguwar siyasa ke  kadawa a kasar mu ta Najeriya  inda hukumar zabe ta soma shirya-shiryen tunkar zaben na shekara ta 2019 a dukkan jihohin kasar nan da  ya rage ‘yan watanni masu zuwa domin ta gudanar da zaben.

A yanzu dai jam’iyun siyasar a kasar nan tuni sun fara sayar da takardun neman tsayawa takara a mukamai daban-daban a kowace jiha ta kasar nan da kuma kujerar shugabancin kasa.  A jihar Kebbi dai kimanin ‘yan takara biyar ne ke son kujerar ta Gwamna Abubakar Atiku Bagudu daga ciki da wajen jam’iyyar APC a jihar ta Kebbi, wanda ya shi ma ya tsaya takarar domin zaben sa  karo na biyu, inda  wadanan ‘yan takarar  mutun biyar sun lashi takobin  karbe ofishin Gwamna na jihar daga hannun Gwamna Bagudu a zaben 2019 mai zuwa.

‘Yan takarar biyar dukkan su sun bayyana kudurin sun na tsayawa takarar kujerar Gwamna a zaben 2019 mai zuwa domin karawa da Gwamna Bagudu da ke kan gado  mulkin jihar. ‘Yan takara guda hudu dai sun fito ne daga jam’iyyar PDP sai kuma  dan takara daya daga jam’iyyar APC da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu yake mulki a karkashin jam’iyyar a jihar ta kebbi.  A cikin ‘yan takara  hudu, uku  daga  masarautar Argungu suka fito sai biyu daga masarautar Gwandu . A cikin ‘yan kwanakin nan Dansarautar Argungu  Ibrahim Muhammad Mera (CIROMAN KABI) ya bayyana kudirinsa na neman tsayawa takarar kujerar Gwamnan jihar ta kebbi a karkashin jam’iyyar APC . Ciroman Kabi ya fito ne bayyan kiran da jama’ar sa keyi na ya fito domin yin takarar kujerar Gwamnan jihar , wanda  tsohon mataimakin kwamturola janal na hukumar kwastan ta kasa sanan kuma  shine Ciroman Kabi kuma mai jiran gadon sarautar  Argungu  kuma  kane ga  Sarkin  Argungu  mai ci yanzu wato Alhaji Samaila Muhammad Mera, inda tun shakaru uku da yayi murabus daga aikin kwastom  ya nuna sha’awarsa ta neman tsayawa  takarar kujerar Gwamnan jihar  kebbi wanda ya bayyana . Tun lokacin in don zaka shigo jihar ta kebbi daga jihar sakkwato zaka rika ganin alunan hotunansa aman ne kan babbar hanyar ta shigowa wanda itace  alama  mai nuna cewa yana bukatar shiga fagen dagar neman kujerar da Gwamna Bagudu ke son komawa karo na biyu ga mulkin jama’ar jihar ta kebbi. Haka kuma mutanen da dama na ganin cewa kamar ba da gaske Ibrahim Muhammad Ciroman  keyi ba.  Amma sai gashi wasa ta zama gaskiya domin  ya  mallaki wani katafaren  ofishin kamfen a garin Birnin-Kebbi sai kuma yayi tattaki zuwa babban ofishin jam’iyyar ta APC da ke a Abuja domin saye takardun tsayawa takarar Gwamnan jihar a zaben 2019 mai zuwa.  Jama’a dai na hasashen cewa Ciroma na da kalubale a gaban sa domin zaman sa sabon dan siyasa a siyasar kebbi, don ganin irin karbuwar da Gwamna Bagudu yayi ga jama’ar jihar . Haka kuma a na ganin cewa yana fuskantar barazana yayin gudanar da yakin neman zabe ga samun nasarar lashe zaben jihar a matsayin zababen Gwamnan jihar a zaben 2019 mai zuwa. Har ilayau kuma wani dan takarar da ake ganin cewa yana da karfin gaske  ga takarar kujerar Gwamnan jihar, Sanata Isah Galaudu daga karamar hukumar  mulki ta Augie a cikin jihar. Cewa a daidai lokacin da sanatan ya koma jam’iyyar PDP, sanata Galaudu babban dan jam’iyyar APC ne kafin ya fice daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar adawa ta jihar da kuma ta kasa. Galaudu dai tsohon shugaban ma’aikata ne na majalisar dattawa a karkashin Dakta Abubakar Bukola Saraki. Ya Bayyana aniyar sata tsayawa takarar Gwamnan jihar ta kebbi a karkashin jam’iyyar PDP a ofishin jam’iyyar ta PDP a kwanan a garin Birnin-Kebbi. Bisa ga kwarewarsa na harakokin siyasa, jama’a na  ganin cewa yana da kwarewar da zaya iya mulkin jama’ar jihar ta kebbi idon an zabe shi a matsayin zababen Gwamnan jihar. Tun lokacin da sanata Galaudu ya bayyana kudurinsa na tsayawa takarar Gwamna a karkashin jam’iyyar ta PDP ya shiga bidar mutane da kuma neman goyon bayan jama’a duk fadin kananan hukumomi ashirin da daya da ke akwai a jihar ta kebbi.

Shima wani dan takara  a jam’iyyar ta PDP Alhaji Abubakar Gari Malam, wanda sanan nene kuma tsohon mataimakin kwamturola janal na kwastan . Gari Malam yana daya daga cikin ‘yan siyasa sanan nu a jihar ta kebbi  wanda kuma ke da tarihin siyasa . Ya kuma taba takarar kujerar Gwamna a jihar ta kebbi har sau biyu amma yafadi. Ya fara takarar kujerar Gwamna a karkashin jam’iyyar  DPP a shekara ta 2007 daga nan kuma ya koma takara a karkashin jam’iyyar CPC a 2011. A shekara 2015 ya kuma yi takarar sanatan kebbi ta tsakiya tare da tsohon Gwamnan jihar Kebbi kuma Sanata mai wakiltar mazabar Kebbi ta tsakiya a majalisar dattawa a halin yanzu Sanata Muhammadu Adama Aliero inda ya rasa. Abubakar Garin Malam abokin Sanata Adamu Aliero ne inda suka shiga jam’iyyar PDP, CPC kuma suka barta  daga baya Abubakar Garin Malam ya koma jam’iyyar PDP daga nan ne suka rabu ko bayan ban-bancin jam’iyyar. Garin Malam dai dan masarautar Gwandu ne kuma dan cikin garin Birnin-kebbi wanda unguwar su daya da Gwamna Bagudu a tsohon garin da a ke kira (KOFAR KOLA). Magoya bayan Garin Malam na ganin cewa tun daga masarautar Gwandu yake takarar kujerar Gwamna a gare shi na da karfin gaske a zaben 2019. Haka kuma tsohon ministan harakokin kasashen waje kuma tsohon ma’ajin jam’iyyar PDP na kasa, Alhaji Buhari Bala, wani dan takarar Gwamna daga masarautar Gwandu mai tahirin siyasa a jihar da kuma kasar bakin daya. Buhari Bala daya daga cikin ‘yan takara hudu da suka jadaga na tabbatar da cewa sun karbe mulkin jihar daga hannun Gwamnan Bagudu a zaben 2019.  Jama’ar san a ganin cewa yana da damar da zai lashe zaben fid da gwani a jam’iyyar PDP domin karawa da Gwamna Bagudu. Kazalika akwai Sanata Umar Abubakar Tafida daga masarautar Argungu wanda shi ma ana ganin cewa wani dan takara ne da ke iya takawata rawa ga takara kujerar Gwamnan jihar ta kebbi a zabe mai zuwa . sanata Tafida tsohon shugaban hukumar kula da tashar jiragen ruwa wato (Nigeria Port Authority), wanda ya dade cikin siyasar jihar tun lokacin da ya fara siyasa . A zaben 2015  shine mataimakin Bello Sarkin Yaki ga takarar kujerar Gwamna a jihar, amma kuma Gwamna Bagudu ne ya lashe zaben a 2015 a matsayin zababen Gwamnan jihar ta Kebbi. Bisa ga tahirin wadannan ‘yan takarar akwai bayyana da ke yawo a duk fadin jihar cewa “ jam’iyyar APC  na da babban kalubale a zaben 2019 a jihar domin dukkan ‘yan takarar tsofafin ‘yan siyasa ne a cikin jihar da kuma a kasar Nijeriya”. Amma  mai magana da yawun jam’iyyar ta APC, Alhaji Sani Dododo ya karyata wadannan maganar da ake yadawa, inda yace” jam’iyyar APC ce jam’iyyar maikarfi  a jihar saboda haka babu filin da wani dan takara zai iya shiga har yaci zaben da zai shiga gidan gwamnatin jihar a matsayin zababen Gwamnan a zaben 2019 mai zuwa insha Allah, wanda Gwamna Bagudu zai koma lashe zaben da yardar Allah”.

Shi ma mai magana da yawan jam’iyyar ta PDP, Alhaji Ibrahim Umar Ummai, ya bayyana cewa jam’iyyar PDP a jihar Kebbi ta shirya karbe mulki jihar daga hannun jam’iyyar APC a zaben 2019 mai zuwa.  A halin yanzu muna daga ‘yan takara kujerar Gwamna masu tahirin siyasa a jihar da kuma kasa saboda haka insha Allahu zamu ba jam’iyyar APC mamaki domin zamu karbi mulkin jihar daga hannun su domin mu shiga gidan gwamnati muwa jama’ar jihar Kebbi mulki nagari kuma inganci insha Allah.

Exit mobile version