Kebbi Za Ta Kashe Miliyan N464 Kan Karfafa Wa Mata Marasa Karfi – Aisha Maikurata

Karfi

Daga Umar Faruk,

A kokarin da ci gaba da gwamnatin jihar Kebbi keyi wurin rage talauci da inganta rayuwar mutane musamman Mata marasa karfi a duk fadin jihar Kebbi.

Haka kuma Gwamnan jihar, Abubakar Atiku Bagudu ya amince da aiwatar da ayyuka da tsarin inganta rayuwar mutane a jihar musamman Mata marasa karfi da za a kashe kudaden kimanin Naira Miliyan dari hudu da sittin da hudu, da dari biyar da talatin da biyu da kuma dubu dari takwas da tamanin da takwas (N468,532,888) a karkashin ma’aikatar harkokin mata da ci gaban da walwalarsu.

Sakatariyar din-din-din ta ma’aikatar harkokin matan, Hajiya Aisha Muhammad Maikurata ce ta sanar da hakan a yayin zantawa da manema labarai a Birnin kebbi a jiya.

Ta ci gaba da bayyana cewa” Ma’aikatar Harkokin Mata da ci gaban su za ta shiga a dama da ita wajen aiwatar da ayyukan na tallafawa Mata marasa karfi da galihu yankunan kananan hukumomi goma sha daya da yan Majalisar Dokokin a Jihar masu wakiltar su suka zakulo a yankunan su da ake Kira a turance ( constituency project).

“A cewar babbar Sakatariyar ta Din dindin, kananan hukumomin da za su ci gajiyar tallafin ayyukan sun hada da, Gwandu, Koko Besse, Aliero, Maiyama, Jega, Bagudo, Fakai, Ngaski, Argungu, Danko-Wasagu da Yauri, inji babbar Sakatariyar Aisha Muhammad Maikurata yayin da take zantawa da manema labarai a Birnin-Kebbi”.

Hakazalika ta ce” Manufar ayyukan shi ne a karfafawa manoma, zawarawa, Marayu, matasa da mata masu rauni a cikin al’ummar da ke a wadanda kananan hukumomin da aka ambata tun a farko, inji ta”.

Hajiya Aisha Maikurata ta kuma kara da cewa a kwanan nan, Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayar da tallafi ga mata Dari uku da Hamsin (350) masu a Kasuwancin Tumatir a duk fadin jihar don kara karfafa Kasuwancin nasu da kuma tattalin arzikin jihar da na kasa baki daya.

Bugu da kari ta ci gaba da bayyana cewa ‘Wannan na daya daga cikin wasu shirye-shiryen da gwamnatin jihar Kebbi a karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu keyi kan karfafa ea wurin farfado da tattalin arziki a fannoni daban-daban da aka aiwatar wa a jihar ta Kebbi inda suka karbi Naira Dubu Talatin (N30,000) kowannen su.

Haka kuma ta ce” Kudin da Ma’aikatar za ta kashe kan aiwatar da ayyukan bada tallafi ga marasa karfi a yankunan kananan hukumomi goma sha daya na jihar na daga cikin Naira biliyan biyu da Miliyan dari hudu da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya bada umurnin fitarwa don yin ayyukan mazabu a cikin jihar.

Daga karshe Sakatariyar din-din-din, Hajiya Aishatu Muhammadu Maikurata ta bayyana jinda dinta da yaba da irin goyon bayan da ake bai wa Ma’aikatar Mata tare da nuna kauna da gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya yi wa marayu da sauran wasu mutanen da basu da karfi a jihar.

Exit mobile version