Kenyatta Ne Ya Lashe Zaben Shugaban Kenya

Hukumar zaben kasar Kenya ta bayyana sakamakon zaben da aka gudanar a kasar ranar Talata inda ta ce, Shugaban  Kenya Uhuru Kenyatta ne ya samu nasara a babban zaben.

Kenyatta ya samu kashi 54.3 cikin 100 na kuri’un da aka kada, yayin mai biye masa Mista Raila Odinga, ya samu kaso 44.7 cikin 100.

Sai dai gamayyar ‘yan adawar kasar sun yi watsi da sakamakon zaben tun gabanin a sanar da sakamakon zaben.

Exit mobile version