Khadi Shehu Ibrahim Ahmad 1958-2021: Yadda Rasuwar Alkalin Alkalan Jihar Kaduna Ta Haifar Da Wagegen Gibi  

Alkalin

Daga Abubakar Abba,

Marigayin wanda aka haifa a Unguwar Albarkawa da ke Birnin Zariya, a ranar 2 ga watan Oktobar 1958, ya rasu yana da shekaru 63 a duniya.

Kafin rasuwarsa, marigayin ya bayar da gagarumar gudunmawa a bangaren Shari’ar Musulunci na Jihar Kaduna, inda hakan ya haifar da gibi mai wuyar cikewa.

Daga cikin abubuwan da marigayin ya aiwatar da ba za a taba mantawa da shi ba, akwai tsayin Dakar da ya yi wajen yaki da cin hanci da rashawa a sashen Shari’ar Musulunci na Jihar Kaduna. A lokuta daban-daban, ya sha bayyana cewa duk Alkalin Kotun Musuluncin da aka kama da wata badakalar cin hanci da rashawa, zai fuskanci fushin hukuma bisa yadda doka ta tanadar.

Marigayi Khadi Shehu ya kuma mayar da hankali, musamman wajen ganin ma’aikatan sashen Shari’ar Musulunci a jihar sun rungumi da’a a yayin gudanar da aikinsu.

Bugu da kari Shehu ya yi namijin kokari wajen daidaita al’amuran kotunan Shari’ar Musulunci na jihar tare da wallafa kasidu da littafai da dama, kamar su littafin ‘Harshen Larabci’, da na ‘Hukuncin Shari’ar Musulunci’ a shekarar 1980, sannan akwai littafinsa a kan tsarin gudanar da mulkin kotuna a 2002.

Har ila yau, wasu daga cikin manyan kasidun da marigayi Shehu ya gabatar a lokacin ruyuwarsa sun hada da, kasida kan Alkalai da Lauyoyi a karkashin Shari’ar Musulunci a 2002, sai kuma wata kasida kan Dokokin Filaye a Shari’ar Musulunci da kuma Dokokin Filaye na Kasa a 2002, wadda ya gabatar a Babban Birnin Tarayya Abuja. Bugu da kari, ya taba rubuta wata shahararriyar kasida a kan Aure a Shari’ar Musulunci, da ta kunshi bayani dalla-dalla a kan yadda ake daurawa, da rabuwa, da kuma  hakkin kula da ‘ya’ya a  2009.

Kamar yadda mutane daban-daban da suka yi mu’amala tare da shi suka tabbatar, Marigayin Alkalin Alkalan, mutum ne mai matukar saukin kai da girmama duk wanda mu’amala ta hada su walau ya sans hi ko bai san shi ba.

Mutum ne mai tsoron Allah da son ganin ana yin gaskiya a fannin Shari’a a Jihar Kaduna, wanda ya kuma gudanar da rayuwarsa wajen yin haba- haba da kowa.

Kafin rasuwarsa, kungiyoyi da dama sun karrama shi da lambobin yabo da suka hada da lambar yabon shugabanci nagari a 2008 ta Alkalin Alkalai da ya fi jajircewa a Nahiyar Afirka a 2015.

Ya rasu a ranar 26 ga watan Oktobar 2022, ya bar mata hudu, da ‘ya`ya 19, da jikoki. An yi masa sallar jana’iza a gidansa mai lamba 7 da ke kan titin Danburan Unguwar Malali GRA Kaduna, inda aka binne shi a makabartar Unguwar Rimi GRA Kaduna. Daruruwan mutane ne suka yi tururuwar zuwa jana’izar ciki har da manyan jami’an gwamnatin jihar ta Kaduna da na sashen shari’a na kasar nan.

Domin tunawa da marigayin da kuma duba irin babban gibin da ya bari mai wuyar cikewa, ga maimaicin wani rahoto na musamman da muka taba wallafawa a ranar 10 ga Satumbar 2021, wato ana sauran wata daya da kwana biyar ya rasu:

 

Darasi Daga Rayuwar Alkalin Alkalai Na Jihar Kaduna, Dakta Shehu Ibrahim Ahmad

Daga Abdulrazak Yahuza Jere

 

Masu zantukan hikima kan ce “da babu makoya, da gwanaye sun kare”. Wannan magana tana nufin ya zama wajibi masu tasowa su rika la’akari da hanyoyin da fitattun magabatan da suke son bin sawunsu suka bi domin samun darasin hawa turbar samun nasara.

Domin taimaka wa wadanda suke son samun nasibi a bangaren shari’a wajen zaben abin koyi mafi dacewa, ya sa na yi azamar nazarin rayuwar Alkalin Alkalai na Kotun Daukaka Kara ta Shari’ar Musulunci ta Jihar Kaduna domin yi wa masu muradin taka matakin da ya kai kyakkyawar shimfida tare kuma da bayyana wa dukkan al’umma darussa masu dimbin fa’ida daga rayuwarsa. Alkalin Alkalan shi ne Maishari’a Dakta Shehu Ibrahim Ahmad.

Idan aka dauki hoton rayuwarsa, babu shakka za a ga cewa shi kansa adabi ne sukutum da ya kamata ya zama madubin dubawa; ba ga masu ruwa da tsaki a bangaren shari’a ba; har ma da masu burin zama jakadun cigaba a cikin al’umma.

Tarihi ya nuna cewa Alkalin Alkalai Dakta Shehu Ibrahim Ahmad, tsatso ne na mashahurin malamin musuluncin nan da ya jagoranci wata tawagar yada musulunci zuwa kasar Borno (Daular Sefawa a wancan lokacin), Shaikh Muhammad Fateh a karne na 15 ko 16. Da farko tawagar shehin malamin ta zauna ne a Laraba Geidam, daga bisani ta nausa zuwa Kukawa. Al’ummar Kukawa ba su yi wata-wata ba suka nada shi Alkalin Alkalai bayan sun fahimci tarin iliminsa na musulunci, wanda idan na fadi cewa tun daga wannan lokacin ne Alkalin Alkalan Jihar Kaduna na yanzu, Dakta Shehu Ibrahim Ahmad ya samu sirrin alkalancinsa; ban yi kuskure ba.

Dakta Shehu Ibrahim Ahmad jika ne na takwas ga Shaikh Muhammad Fateh. Mahaifinsa Shaikh Ibrahim Ahmad, da ne ga Makama Ahmadu, jika ga Shaikh Umarul-Walin Zazzau, mashahurin shehin musulunci masanin shari’a.

Daga cikin malaman da mahaifin Alkalin Alkalai Shehu Ibrahim Ahmad ya yi karatu a wurinsu har da mashahurin shehin nan na Zariya, Shaikh Malam Yahuza Zariya wanda Babban Waliyyin Allah Shehu Ibrahim Inyass ya yi masa albishirin cewa duk wanda ya zama almajirinsa ya rabauta da babban rabo. Bisa wannan, za a fahimci cewa Alkalin Alkalai Shehu Ibrahim Ahmad ya fito ne daga babban gida.

Da yake daga tushe nake son dauko nazarin nawa, zan waiwayi tarihin rayuwar Alkalin Alkalan kamar yadda na ciro daga wani littafin da maidakinsa, Malama Amina Shehu Ibrahim Ahmad ta rubuta a kan tarihinsa mai suna “Justice Dr. Shehu Ibrahim Ahmad: A Dynamic Jurist”.

An haife shi a cikin iyalan Shaikh Ibrahim Ahmad, Sarkin Ruwan Zazzau. Shi ne na tara a cikin ‘ya’yansa su 13. Mahaifiyarsa, Hajiya Maryam wanda ake mata lakabi da ‘Amfana’, ita ce malamarsa ta farko da ta koyar da shi karatun addini. Daga nan sai kakansa ta wurin uwa, Malam Ahmadu Baban Ali kana daga bisani ya dora a wurin mahaifinsa. Har ila yau, ya yi karatu a wurin malamai da zaurukan karatu daban-daban da suka hada da Makarantar Malam Mani (Sarkin Ladanan Zazzau), Makarantar Alu (Sarkin Ladanan Zazzau), Makarantar Malam Rufa’i, Makarantar Ladan Sharehu (Matawallen Zazzau), Makarantar Malam Ibrahim Kakaki, Makarantar Malam Mamuda da ke Anguwar Kaura kusa da gidan Malam Tanimu da sauran su. Ya karanci ilimi sosai a wadannan makarantun musamman na bangaren shari’a.

Kishinsa na zurfafa iliminsa bai bar shi ya zauna ba, Malam Shehu ya cigaba da daukan darasi a wurin kakansa na wurin uba Malam Ahmadu Baban Ali da kuma wurin kawunsa Alhaji Yahaya Sunusi (Dan Masa’i) wanda yake da ga Wazirin Zazzau Sanusi, musamman a fannin fikihu da sha’anin mulki. Haka ya ci gaba da nazartar sauran ilmomi har zuwa lokacin da ya shiga fannin karatun zamani (boko).

Da farko an sa shi a makarantar koyon Larabci ta firamare ta Lardin Zazzau da ke Zariya a shekarar 1966. Amma kuma sai ya kammala karatunsa na firamare a makarantar nazarin shari’a da ke Kano a 1973 inda ya samu shaidar karatun Larabci da Ilimin Addini. Makarantar ta Kano matakinta daya ne da wacce ya fara yi a Zariya.

Marubuciyar littafin, Malama Amina ta bayyana a  shafi na 10, sakin layi na karshe cewa, “wani abin ban sha’awa da na gani shi ne shugaban makarantar nazarin shari’ar (ta Kano) a wannan lokacin dan kabilar Ibo ne – sunansa Malam Usman.”

Daga nan makarantar ne Dakta Shehu ya cigaba da karatu a Makarantar Nazarin Larabci ta Kano (S.A.S) wacce take a matakin sakandare inda ya kammala a 1977 kuma ya samu babbar shaidar karatu na ilimin Addini. Wani abin sha’awa game da karatunsa shi ne, tun yana matakin firamare a Lardin Zazzau, malamansa ke shan tambayoyi daga gare shi har ma ta kai ga daya daga cikin malaman makarantar, Shaikh Jalaluddeen Abdullahi ya tabi yi ma sa lakabi da “Shehu na Allah, yaro da gari abokin tafiyar manya!”. A lokacin da yake kwaleji kuma, Dakta Shehu yakan shafe sa’o’i da dama a dakin karatu na makarantar yana nazarin littafai har ma da wadanda ba su shafi fannin da yake karantawa ba. Abokan karatunsa kan bayyana mamakinsu da irin tarin iliminsa a lokacin.

Wani zai iya cewa shin Dakta Shehu ba y ]a shiga sauran harkoki ne na makaranta sai karatu kawai? A’a, ba haka lamarin yake ba. Ya shiga harkokin wasanni na makaranta musamman kwallon kafa a har ma ‘yan wasan makarantarsa ba su jin dadin taka leda idan ba ya nan.

Ya kasance dalibi mai kwazo da hazaka ta ko wane fanni, sannan ga iya walwala da jama’a da nuna halin kirki ga kowa ba tare da nuna bambanci ba. Daya daga cikin abokan karatunsa, Muhammad Buseri Denesi (wani dan asalin yankin Bendal) da kuma wani dan kabilar Yarabawa, Suleman Murtala mai inkiya “Olu Mazare”, sun ce Shehu mutum ne da ba ya taba mantawa da fuska ko sunan mutumin da suka san juna komai dadewa. Wani abokin karatunsa shi ma ya tabbatar da cewa “Shehu irin mutanen nan ne da ba su da mantuwa da wuri wanda ba kasafai ake samun ire-irensu a cikin jama’a ba. Yana da bin dokokin makaranta sau da kafa”. Abokansa sun yi masa kyakkyawar shaidar kasancewa mutum mai saukin kai da taushin hali kuma ga shi kamili. Wakazalika, abokan sun ce ba ya yarda da duk wani abu da zai dauke ma sa hankali daga karatu, sannan ga shi da kyauta ba rowa ko da kuwa dan abin da ke hannunsa ba yawa.

Wani abokinsa da har ila yau suka yi karatu tare, Ali Magashi ya yi waiwayen cewa Shehu ya yi zaman lafiya da kowa da kowa, malamai da dalibai a makaranta. Bayan haka, abokansa sun ce yanayin yadda ya dauki rayuwarsa da sauki da tawali’u ya birge kowa.

Tun da kuruciyarsa ya fara nuna kulawa ta musamman ga mahaifiyarsa, kasancewar yakan kukuta alawus din da ake biyansu a makaranta ta karshe-karshen 1977 ya yi wa mahifiyarsa da kakarsa sayayya idan zai ziyarce su daga Kano. Ko wannan kadai ya isa ya samu albarka a rayuwarsa ballantana kuma ya kara a kan hakan.

Bayan ya kammala firamare da sakandare, Malam Shehu ya shiga Makarantar Nazarin Shari’a ta Aminu Kano inda ya yi difiloma a kan fannin shari’a daga 1977 zuwa 1980. Daga nan sai ya tafi Jami’ar Bayero ta Kano ya kammala digirinsa a sashen shari’a (LLB) a shekarar 1985. Ya halarci makarantar horas da ma’aikatan shari’a da ke Legas inda ya kammala aka yaye su tare da shigar da shi cikin kwararrun ma’aikatan shari’a na Nijeriya a shekarar 1986.

Zan dakata da batun makaranta da kwasa-kwasan da ya yi in juya akalar zuwa fannin aikace-aikacen da Alkalin Alkan na Jihar Kaduna ya fara a rayuwarsa har zuwa matakin da yake kai a yanzu.

Dakta Shehu Ibrahim Ahmad ya fara aiki ne a bangaren shari’a na Jihar Kano a matsayin Akawun Kotu a shekarar 1977, inda aka tura shi zuwa Garu Dutse da ke cikin Jihar Jigawa yanzu. A sakamakon kwazonsa na aiki da cigaba da karatunsa da ya mayar da hankali a kai, ya yi ta samun karin girma cikin hanzari daga Akawun Kotu zuwa Magatakardan Kotu, aka kara ma sa girma zuwa Babban Magatakardan Kotu na biyu, aka kara ma sa zuwa Babban Magatakarda na daya kana daga bisani ya zama Babban Magatakardan Kotun baki daya. Ya samu karin girma sau shida a cikin shekara takwas, watau daga 1980 zuwa 1988.

Dakta Shehu ya sauya layin aiki daga bangaren magatakarda zuwa bangaren alkalanci inda aka nada shi Alkalin Majistare a mataki na biyu inda ya kasance Majistare na farko a yankin Karamar Hukumar Gezawa a Jihar Kano. Daga kan wannan mukamin ya yi ta samun karin girma har ya zama Babban Majistare baki daya duk a tsakanin shekara biyar kacal, watau daga 1988 zuwa 1993.

Da yake masu karin magana sun ce “nagari nakowa”, nagartar Dakta Shehu Ibrahim ta habaka aikinsa a tsakanin Jihar Kano da Jihar Kaduna a fannin aikin alkalancin Majistare, sai dai ya dakatar da aiki da bangaren na dan wani lokaci a matsayin Babban Majistare na Tudun Wada Zariya a 1993, ya koma aiki da bangaren tattalin arziki mai zaman kansa a matsayin Jami’i na biyu mai kula da hulda da bangaren shari’a a Bankin Habib (Habib Nigeria Bank Ltd). A nan ma, likkafarsa ta cigaba har zuwa matakin mataimakin manajan hulda da bangaren shari’a. A shekarar 2000 ya yi sallama da bangaren ya koma layin aikinsa na asali inda aka nada shi Babban Magatakardan Kotun Daukaka Kara ta Shari’ar Musulunci. Shekara uku kacal ya yi a matsayin ya samu cigaba aka nada shi daya daga cikin manyan Alkalan Kotun (Kadi) a shekarar 2003.

Gaskiya matakin nasara kuma duk wanda ya cire komai ya sa Allah a gaba, zai ga falalar Rahmanu a dukkan abin da ya sa gaba. Maishari’a Dakta Shehu Ibrahim Ahmad ya zama mukaddashin Alkalin Alkalai a ranar 31 ga Disambar 2014, kana daga bisani a ranar 28 ga Mayun 2015, Allah Rahimin Sarki ya tabbatar ma sa da matsayin baki daya.

Daga lokacin da ya hau matsayin na Alkalin Alkalai, ya yi tsayuwar daka wajen daidaita al’amuran sashen kotunan Shari’ar Musulunci na Jihar Kaduna. Ma’aikatan sashen daban-daban da suka zanta da wakilinmu sun tabbatar da cewa kama aikin Alkalin Alkalan ke da wuya suka shaida cewa tabbas an mayar da amana ga ahalinta.

Wata shaida da ta ke kara fito da nagartarsa a fili ita ce, a shekarar 2017 daukacin Alkalin Alkalai na Nijeriya sun amince ya zama shugabansu a karkashin Kungiyarsu ta ‘Forum of Grand Kadis of Nigeria (FGKN)’. Wakazalika, daukacin Alkalin Alkalan da Manyan Alkalan Kotunan Daukaka Kara na Gargajiya na Nijeriya baki daya sun yi hadin gwiwa inda suka sake zaben Dakta Shehu Ibrahim Ahmad ya zama shugabansu a karkashin ‘Forum of Grand Kadis & President Sharia/Customary Courts of Appeal of Nigeria (FGPSCCAN)’ a wannan shekarar ta 2018.

Gogewarsa a kan aiki da iya mu’amala da al’umma sun sa masu shirya tarurruka na kara wa juna ilimi da na bita kwadayin neman cin gajiyar ilimi da hikimomin da Allah ya yi wa Alkalin Alkalai Dakta Shehu Ibrahim Ahmad baiwa da su. A sakamakon haka, ya halarci manyan taruka sama da 50 a ciki da wajen kasar nan tare da gabatar da kasidu a mafi akasarinsu.

Kadan daga cikin kasidu da littafan da ya wallafa sun hada da Littafin da ya yi da harshen Larabci a kan ‘Hukunce-Hukuncen da Aka Soke da Wadanda Suka Soke Su a Shari’ar Musulunci’ a shekarar 1980. Da kasidar da ya gabatar a Jami’ar ABU da ke Zariya a shekarar 2002 mai taken ‘Judges And Lawyers Under Sharia (Alkalai da Lauyoyi a Karkashin Shari’ar Musulunci)’. Da Littafinsa da ya yi da Hausa a kan ‘Tsarin Gudanar da Mulkin Kotuna’ a shekarar 2002. Da Kasidar da ya gabatar a taron Babbar Majalisar Shari’a ta Kasa (NJC) mai taken “Aspects of Islamic Land Law bis-a-bis Land Use Act (Mahangar Dokokin Filaye na Shari’ar Musulunci da Dokokin Filaye na Kasa) a shekarar 2002 a Abuja.

Sauran sun hada da: “Marriage Under Sharia:- Contract, Dissolution And Custudy Of Children (Aure a Shari’ar Musulunci: Daurawa, Rabawa da Hakkin Kula da ‘Ya’ya” a shekarar 2009. Da Littafin ‘Unity Amongst The Neighbour-Hood In The Society 2011 (Hadin Kai a Tsakanin Makwabta a Cikin Al’umma)’ a shekarar 2011. Da Littafin ‘The Modernization Of Almajiri System In Nigeria, A Biable Solution To the Realization Of Education Rights 2011 (Zamanantar da Tsarin Almajirci a Nijeriya, Ita ce Mafitar Tabbatar da ‘Yancin Samun Ilimi)’. Da littafin ‘Contribution Of Islam In Health Care Serbices 2016 (Gudunmawar Musulunci ga Ayyukan Kiwon Lafiya)’ a shekarar 2016. Da littafin ‘Peace And Unity In Nigeria “The Role Of Nigerian Media 2016 (Gudunmawar Gidajen Yada Labarai Ga Zaman Lafiya da Hadin Kai a Nijeriya)’ da sauran wasu da dama.

Har ila yau, daga cikin gudunmawar da bayar a kan mu’amalar ciyar da al’umma gaba, Alkalin Alkalai Dakta Shehu Ibrahim Ahmad ya yi shugabancin Kungiyar Daliban Makarantar Nazarin Shari’a ta Malam Aminu Kano a shekarar 1978 zuwa 1979. Ya taba zama mamba a Kwamitin Fitar da Dokokin Shari’ar Musulunci a Kan Manyan Laifuka ta Gwamnatin Jihar Kaduna a 2001. Yana daya daga cikin ‘yan kwamitin amintattu na Gidauniyar Bunkasa Kiwon Lafiya da Ilimi domin Cigaba (SHED).

Game da kyaututtuka da lambobin yabo kuwa, ya karbe su da dama a kan shugabanci da rikon gaskiya da amana da kwazon aiki. Ciki akwai na ‘Distingushed Award Par Edcellence In Recognition Of Leadership Performance, Transparency, Probity And Accountability-2006’; da Lambar yabon shugabanci nagari na ‘African Leadership Gold Award-2008’; da Lambar Yabon Jakadan Zaman Lafiya ‘Ambassador for Peace 2008’; da Lambar yabon Alkalin Alkalai mafi kwazo da ake baiwa shugabanni a Afirka, wato “African Leaders Par Edcellence “The Most Baluable Grand Kadi Of The Year 2015”; da Lambar yabon wadanda suka samu gagarumar nasara a rayuwa daga cikin daliban Makarantar Horas da Lauyoyi na aji na 86 “Nigerian Law School Class 86 “The Great Achiebers Award” 2015.

Kwazon Alkalin Alkalan na aiki ya sanya Jami’ar Baerkley da ke Michigan, Kasar Amurka ta karrama shi da Digirin Girmamawa a fannin Shari’a a shekarar 2010 ‘Honorary Doctorat Degree (Doctor Of Laws)’ da sauran lambobin da ya samu bila’adadin.

Babban buri ko abin da Alkalin Alkalan na Jihar Kaduna yake fatan gani a koyaushe game da Nijeriya shi ne; hadin kai da zaman lafiya da kwanciyar hankali a matsayin kasa daya dunkulalliya da sadaukarwa ga Allah Mahalicci tare da samun daukaka da hadin gwiwa a kan zaman lumana a duniya da kuma fahimtar juna.

Hakika rayuwa ta yi albarka, koda yake ba za a yi mamakin haka ba idan aka waiwayi jawabin da Mahaifiyarsa, Hajiya Maryam Amfana ta yi a cikin littafin rayuwarsa da Malama Amina ta wallafa a shafi na 2 cewa, “Wannan yaro dai da Allah ya kawo shi, mahakurci ne, mai hankali ne. Ba wai yabon shi ni ke yi ba. Tun da yake, ba shi da abokin dambe ba shi da na fada har Allah ya kawo shi wannan matsayi. Shi da kowa ba sabawa; ga natsuwa. Sannan kuma ya yi biyayya a gare ni da mahaifinshi, har mahaifinshi ya tafi ya bar ni, yana nan yana biyayya a kaina. Wallahi bai taba saba mani ba da rana daya. Duk abin da na ce wa Shehu yi sau daya wallahi shikenan sai dai kawai in ga ana yi…”.

Tabbas, idan aka samu masu bin sawun Alkalin Alkalai Dakta Shehu Ibrahim Ahmad da dama a cikin al’umma, maslaha za ta wanzu, adalci ya karu, gaskiya da rikon amana su yi karfi kana a samu cigaba mara misaltuwa.

 

 

Exit mobile version