Khairat Gwadabe: Shahararriyar ‘Yar Siyasa A Babban Birnin Tarayya Abuja

Khairat Gwadabe tsohowar Sanata wacce ta shiga majalisa tun farko-farkon zamanin mulkin Demokradiyya, ta kasance mambar majalisar dattawa a kwaryar majalisa ta hudu. Inda ta shafe shekaru sama da 16 da barinta kujerar Sanata mai wakiltar mazabar cikin Abuja, amma yanzu haka ta sake dawowa don neman wannan kujerar, shin ya mulkin majalisa yake a da baya da yanzu da take son dawowa, shin za ta tabuka wani abun a zo a gani hasashen masana kenan a kanta.

Wace ce Khairat Abdulrazak Gwadabe?
Sanata Khairat Abdulrazak Gwadabe wacce aka haife ta a shekarar 1962 ta kasance zababbiyar sanata ce mai wakiltar mazabar babban birnin tarayya Abuja wacce ta samu nasarar tsunduma kafarta a majalisar a karkashin jam’iyyar PDP wacce ta shiga aiki a tsakanin watan Mayun 1999 zuwa Mayun 2003.
Khairat wacce ake haife ta a garin Illorin a watan Afrilun shekarar 1962 ta karanci aikin Lauyanci a jami’ar Buckingham. Bayan da aka zabeta a matsayin Sanata an nadata a kwamitinin muhalli, lafiya, da kuma zama shugaban kwamitin harkkoin mata, zama a cikin kwamitin Federal Character, kwamitin harkokin yawon bude ido da al’adu da kuma kwamitin birinin tarayya Abuja dukka a lokacin da take matsayin sanata.
Khairat wacce ta nemi kujerar sanata a shekarar 2003 a karkashin jam’iyyar PDP, amma ba ta yi nasara ba, hakan bai rasa nasaba da batun tsige shugaban kasa a wancan lokacin Olusegun Obasanjo da aka bijiro da shi, wanda watan Janairun 2003 din ta sanar da sauya sheka daga jam’iyyar zuwa cikin jam’iyyar All Nigerian People’s Party (ANPP), biyo bayan rashin fahimta da rashin adalci da take ganin jam’iyyar PDP na yi a wancan lokacin. Tun bayan wannan lokacin ta dan janye kafarta daga neman kujerar siyasa kwatsam a ‘yan watannin nan kuma sai ta dawo da neman sake komawa majalisar dattawa.
Sanatar da ta zauna a majalisa na tsawon shekaru hudu kacal a tsakanin 1999 zuwa 2003, ta shirya damarar sake shiga majalisar dattawan bayan shekaru sha shida da bacewarta daga zauren majalisa.
A bincikin wannan filin ya gano mana cewar Gwadabe ta dawo da muradin son komawa majalisa ne biyo bayan gazawar shugabanci da wakilci da cikin birnin tarayya ke fuskanta wacce ita take kallon gazawar wadanda suke kan mulka a yau, inda ta daura damarar komawa majalisar na dattawa domin dawo da martabar wakilci.
A cewarta, al’ummar FCT sun gaza samun damar daukaka muryarsu har a ji, domin a cewarta sautin mazauna Abuja ya yi kasa tun bayan ficewarta daga zauren majalisar a 2003, wanda ta sha alwashin dawo musu da sautinsu a sama idan ta koma majalisar.
Yanzu haka dai, Gwadabe tana son a zabe ta a wannan kujerar na Sanata mai wakiltar cikin Birnin tarayya Abuja ne a karkashin jam’iyyar APC, inda mazauna Abuja suka fara na’am da dawowarta duba da yadda suka gamsu da salon wakilcinta a tsakanin 1999 zuwa 2003.
Shahararta:
Sanata Khairat Gwadabe, ta samu karbuwa sosai a cikin Abuja tun daga zamanin Obasanjo domin kuwa ta sha tashi gaban majalisa ta kare martabar mazabarta wanda hakan ya sanya al’umman FCT suka ji dadi a lokacin da suka sake ganin ta yunkuro domin neman wannan kujerar. Da kuma nuna rashin samun kyakkyawar wakilci a halin yanzu da neman tsoffin hannu wadanda suka yi aka gani a kasa. Duba da irin gogewarta da har ya sanya ta samu kanta a kwamitoci da dama inda a wasu ta kasance mamba a wasu kuma ta zama shugaba, hakan ya kara mata shahara da daukaka a idon duniya.
Sama da wata biyar da bayyana kudurinta na neman shiga wannan majalisar ta dattawa, to ko jama’an mazabar za su zabi tsohowar hannu?

Exit mobile version