Daga Khalid Idris Doya,
Gwamnan Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen dafawa mata su samu daukaka a fagagen rayuwa daban-daban domin inganta musu nasu rayuwar a kowani bigire.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya karbi bakwancin sabuwar Jakadiyar Nijeriya a kasar Malaysia, Dakta Hajara Salim, wacce ta samu rakiyar al’ummar Akko karkashin jagorancin Lamido Akko a ziyarar godiya da suka kaiwa gwamnan a gidan gwamnati, kamar yadda sanarwar da Ismaila Uba Misilli, Babban Daraktan yada labarun gwamnan jihar ta shaida.
Gwamna Inuwa ya ce mata da matasa sun taka gagarumar rawa wajen kawo gwamnatinsa bisa karaga, don haka kar su ji wata shakkar samun cikakkiyar goyon bayan sa wajen dafa musu su kai ga kowane irin matsayi.
Ya ce, “Allah ya albarkaci jihar Gombe da nagartattun mata masu kima irin su mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Hajiya Amina Mohammed, da tsohuwar shugabar kotunan daukaka kara mai shari’a Zainab Bulkachuwa, da ‘yar majalisar tarayya mai wakiltar Dukku da Nafada Hon Aishatu Jibir Dukku da kuma sabuwar jakadiyar Nijeriya a kasar Malaysia Dakta Hajara Salim da wassu da dama da suka yi ritaya daga aikin gwamnati”.
“Tun farko wannar gwamnatin take tafiya da mata, kuma tana kan kokarin ganin sun samu kason su a mukaman gwamnati daban-daban, domin mata da dama a sassan duniya sun taka rawar a zo a gani, don haka muma namu matan ba za su zama bare ba”.
Gwamnan ya ce yana da kwarin gwiwan cewa Dakta Hajara Salim ta dace da mukamin duba da muhimman mukaman data rike yayin da take aikin gwamnati, yana mai kira a gareta ta kasance Jakadiya ta kwarai ga Nijeriya da jihar Gombe da kuma yankin da ta fito karamar hukumar Akko.
Sai ya bukaci ta bullo da sabin dabarun kulla alaka da yin hadin gwiwa da kasar ta Malaysia don jawo harkokin ci gaba ga jihar Gombe da Nijeriya baki daya.
Ya ce, “Jihar Gombe tana da kokarin kulla alaka da daya daga cikin jami’o’in kasar ta Malaysia kan yadda za ta tallafawa Jami’ar kimiyya da fasaha ta jiha dake Kumo don nausa ta gaba, kuma sai ga shi kin fito daga karamar hukumar Akko, muna fata za ki shiga tsakani don zaburar da hadin gwiwan dake tsakanin mu don jihar mu ta amfana.”
Tun farko a jawabin ta, Dakta Hajara Salim ta bayyana cewa, ta je gidan gwamnatin Gomben ne don mika godiya ga Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya game da goyon bayan da ya ba ta wajen tabbatar da mukamin nata a matsayin jakadiyar Nijeriya, inda ta bada tabbacin yin wakilci na gari.
Ta ce, “Wannar gwamanti ta Jihar Gombe ta bunkasa mata don su kasance daga cikin masu gudanar da harkokin mulki, kuma muna baiwa gwamna tabbacin cewa, ba zai yi dana sanin bamu dama da aka yi ba, ba irin yadda ake dauka cewa, mata sun gaza wajen aiwatar da shugabanci ba”.
Sai ta bukaci karin goyon baya da addu’o’i yayin da ta dauri damarar kama aiki gadan-gadan.
Shi ma Mai Martaba Lamido Akko, Alhaji Umar Mohammed Atiku ya bayyana dacewar nadin na Dakta Hajara Salim, yana mai bayyana ta da cewa mace ce da ta san matsalolin ‘yan uwan ta mata da matasa, yana mai fatan jakadiyar za ta kara dankon dangantaka tsakanin Nijeriya da Malaysia a sassa daban-daban.
Umar Atiku sai ya godewa Gwamna Inuwa Yahaya na irin goyon baya da yake bawa mata a harkokin gwamnatinsa.
A jawabinta, mamba mai wakiltan yankin Dukku da Nafada a majalisar wakilai Hon. Aishatu Jibir Dukku wacce ta raka Dr. Hajara don nuna goyon baya ga mata, ta bayyana cewa, sabuwar jakadiyar, dama can jakadiya ce a sassa daban-daban kafin ma samun wannan mukami, sai ta bayyana ƙwarin gwiwar cewa zata bawa maraɗa kunya ba.
Yayin da take mika godiya ga gwamna Inuwa Yahaya na tallafawa mata da yake yi, Hon. Aishatu Dukku ta kara da cewa, sabon mukamin da aka bawa Dr Hajara Salim ya karawa mata karsashi a Jihar Gombe.