Connect with us

LABARAI

Ki Yaki Matsalar Tsaro Kamar Yadda Ki Ke Wa Korona – Reb Bukisin Ga Gwamnati

Published

on

An shawarci ma su madafun iko, tun daga jihohi ya zuwa gwamnatin tarayya da su hada hannu kamar yadda suka yi yekuwar kare al’ummar Nijeriya daga kamuwa da cutar korona.

Wannan shawarar ta fito ne daga babban Rebaran na cocin Nasara Baptist da Gakiya a Tudun Wadan Zariya Rebara Bukisin D. Sammuel, a lokacin da ya yi tsokaci kan dage dokar hana yin ibada a masallatai da kuma coci-coci da suke daukacin kananan hukumomin jihar Kaduna, da gwamnatin jihar tasa a dalilin kare al’ummar jihar daga kamuwa da cutar Korona da ta addabi duniya bakidaya.

Rebaran Bukisin ya ci gaba da cewar, duk wanda ya lura da matakan da gwamnatin tarayya musamman da gwamnatin jihar Kaduna suka dauka na sa dokar motsawa da sauran matakai ma su yawan gaske, ya ce, da gwamnati za ta dubi bangaren tsaro, da ya shafi ‘yan ta’addan Boko Haram da masu garkuwa da mutane da kuma ma su kisar gilla, tare da sa tsauraran matakan da aka sa da ya shafi kawo karshen wadannan matsaloli, a cewarsa, da al’ummar Nijeriya sun sami natsuwa a rayuwarsu.

A kan haka babban Rebaran Sammuel ya kara shawartar Gwamnatin Jihar Kaduna, musamman gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufa’I, da ya  duba yiwuwar daukar matakan day a dauka ma su zafi ga bangaren tsaro da daukacin al’ummar jihar Kaduna a yau, suna cikin kamfar kwanciyar
hankali tare da iyalansu.

A game da sassauta dokar hana fita kuma da gwamnatin jihar Kaduna ta yi, da ya bayar da damar yin ibadu a masallatai da kuma coci-coci, Rebaran Bukisin D. Sammuel ya nuna matukar jin dadinsa da matakin da gwamnatin jihar Kaduna ta dauka, na sa ka’idoji ga masallatai da kuma coci-coci.

Sai dai kuma jagoran addinin ya ce batun da gwamnati ke yin a tabbatar da tazara a tsakanin al’umma da ta sa a masallatai da kuma coci-coci kuwa, ya tabbatar da cewar  shugabannin majami’u da kuma limamai a masallatai duk za su iya bin wadannan ka’idoji da gwamnatin Jihar Kaduna ta gindaya ga mabiya addinan nan guda biyu da aka ambata.

Ya kara da cewar, gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da umurnin bude kasuwannin jihar ta cigaba da yin kasuwanci a wasu makarantu, wannan, a cewarsa, ko da kasuwar  da ta ke cikin gidan mutum ne, ba zai iya tabbatar da wannan tazara ba, a nan sai Rebaran Bukisin ya shawarci gwamnatin jihar Kaduna da ta rika neman shawarar daga shugabannin addinin Musulunci da kuma na kirista, a duk lokacin da matsala mai kama da wannan in ta taso a nan gaba.

A cewar Rebaran Sammuel, wadanda gwamnatin jihar Kaduna ta kira su da sunan shugabannin addini, ko da sun zauna da gwamnatin jihar Kaduna, ba sa bayyana wa sauran shugabannin addini shawarar da suka ba gwamnati a madadinsu, kuma bayan taron, ba sa yi wa nakasa da su wani bayani.

A dai zantawar da wakilinmu ya yi da Rebaran Bukisin  ya alakanta cutar korona ga wasu da ba su da sha’awar gudanar da hidimarsu a gida Nijeriya, a dalilin fita kasashen waje da suke yi, a cewarsa, shi ne su ka gayyato wannan cuta ta korona Nijeriya, sai ya yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnonin jihohi, da su su yi karatun-ta-natsu ga wadanda ke yawan fita kasashen waje, domin gudun ka da su cigaba da gayyato cututtuka Nijeriya a nan gaba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: