Khalid Idris Doya">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Kididdigar Borno Ta Nuna… An Samu Raguwar Matsalar Tsaro Lokacin Buhari – Zulum

by Khalid Idris Doya
December 8, 2020
in LABARAI
3 min read
Zulum
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Duk da kisan manoma a baya-bayan nan da wasu hare-haren da a ka kai, kididdigar lissafin da a ka samu daga kananan hukumomi 27 na Jihar Borno tun daga shekarar 2011, kai tsaye sun nuna har yanzu Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari shi ne wanda gwamnatinsa ra fi nuna kwazo da hazaka wajen kokarin shawo kan matsalolin tsaro da dakile shi a jihar ta Borno, kamar yadda gwamnan jihar, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya shelanta.

Zulum, wanda ya shaida hakan a ranar Lahadi yayin da ke jawabi ga mambobin kungiyar Dattawan Arewa a Maiduguri, tawagar wacce Shugaban Amintattu na Kungiyar, Ambasada Shehu Malami, da Shugaban Kungiyar, Malam Audu Ogbeh, su ka jagoranta.

samndaads

Kungiyar Dattawan, wadanda su ka je Maiduguri, domin jajentawa kan kisan manoma sama da 40 a kwana-kwanan nan da mayakan Boko Haram su ka aikata a kauyen Zabarmari da ke karamar hukumar Jere a jihar ta Borno, sun nuna jimaminsu kan faruwar lamarin.

Gwamnan ya na cewa, a zahirance ya ke irin maida hankali da kokarin da Buhari ya nuna kan shawo kan matsalar tsaro a shiyyar ya zarce irin wanda gwamnatocin baya suka nuna wajen yaki da ‘yan ta’adda a jihar.

“A misali, a shekarun baya kafin zuwan Buhari, akwai wasu kananan hukumomin da ba a iya shigansu kwata-kwata, ‘yanzu haka akwai ‘yan kasa wadanda sarakunanmu ke jagoranta, sun dawo cikin kwanciyar hankali zuwa Bama, Gwoza, Askira-Uba, Dikwa, Ngala, Monguno, Kukawa, Damboa, Konduga, Mafa,  a shekarun baya babu wani da zai iya ziyartar wadannan yankunan balle ma maganar zama.

“Sarakunanmu da suka yi gudun hijira. A yau, ana dawowa Bama tare da rayuwa a cikinta, haka ma Askira-Uba, Damboa, Gwoza da kuma sauran yankunan. Rayuwa ya dawo a na zuwa Baga.”

“Dukka wadannan lamuran ba su faru ba kafin zuwan Buhari, don haka Buhari ya nuna kwazo da hazaka matuka. A zahirin gaskiya ba ma zai iyu mutum ya motsa wasu kananan hukumomi zuwa wajen Maiduguri ba tare da fargaba ba.

“Masu tada kayar baya sun nuna kwarin guiwar kai hare-hare da kwace barikokin soji kamar Barikin Monguno, Bama, Giwa Barrack da shalkawatan Multinational Joint Task Force  da ke Baga da wasu ma.

“An samu lokacin da kullum sai an samu kai harin Bam a sassa daban-daban na Maiduguri, hakan ya faru kusan mafi yawan manyan biranen jihar, amma dukkanin wadannan ababen marasa dadi sun daina tun zuwan Buhari. Wannan lamuran su na kunshe cikin kundin tarihi da kididdigar da suke akwai,” kamar yadda Zulum ke shaidawa.

Gwamnan, daga nan sai ya nuna cewa dole su nuna gamsuwa kan cigaban tsaro da aka samu idan su ka kwatanta lamuran da shekarun baya.

“Sautari, ‘yan ta’addan sun fi son jawo hankalin jama’a wanda hakan na daga cikin dabarun yada farfagandarsu, don haka suke kai hari ga al’ummominmu su arce, wanda a hakika wannan na matukar damunmu,” Inji shi.

Ya nemi masu ruwa da tsaki da su cigaba da baiwa gwamnatinsa goyon baya da gudunmawa domin su samu nasarar yaki da ‘yan ta’adda kamar yadda suka sanya a gaba.

SendShareTweetShare
Previous Post

Mafi Yawan Almajirai Ba ’Yan Nijeriya Ba Ne, Cewar Ganduje

Next Post

Gobe Za A Kammala Zaben Cike Gurbin Dan Majalisar Jihar Zamfara

RelatedPosts

Kananan Hukumomin Jihar Kano

Yau Za A Yi Karon Batta A Zaben Kananan Hukumomin Jihar Kano

by Khalid Idris Doya
19 mins ago
0

 Jam’iyyu 11 ne za su fafata PDP Kwankwasiyya ta ce,...

Sojoji

Tsofaffin Sojoji Sun Nemi Karin Kudin Fansho

by Khalid Idris Doya
31 mins ago
0

Kungiyar tsofaffin sojoji ta kasa reshen jihar Anambra ta bukaci...

Ali Baba

Zaben Kananan Hukumomi: PDP Kwankwasiyya Ta Maka KASEIC A Kotu

by Khalid Idris Doya
47 mins ago
0

Bangaren Kwankwasiyya na jam'iyyar PDP a jihar Kano, ta jadadda...

Next Post
Ma’aikatan INEC Biyu Sun Yi Batan Dabo A Zaben Dan Majalisar Jihar Zamfara

Gobe Za A Kammala Zaben Cike Gurbin Dan Majalisar Jihar Zamfara

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version