Connect with us

BABBAN BANGO

Kididdigar Wadanda Suka Kamu Da Korona A Afirka

Published

on

Mun sani cewa ran 14 ga Watan Fabarairun wannan Shekara (2020) ne cutar COVID-19 ta fara lekowa cikin wannan nahiya ta Afurka, yanzu haka an sami wani rahoto da masana suka fitar, wanda ke fitar da adadin jumlar mutanen da suka harbu da cutar cikin kowace Kasa a Afurka, daga lokacin da aka fara arangama da ita, zuwa 2 ga Watan Yunin Shekarar 2020 (June 2, 2020).

 

Babu lokacin kawo daukacin sunayen Kasashen na Afurka bakidaya daki-daki, sai dai za a gabatar da wasunsu, sai kuma a dan yi wani tsokaci daga bisani, sannan kuma sai a cigaba. Misali;

 

Daga lokacin da Kasar South Africa ta fara fuskantar matsalar cutar COVID-19, mutane dubu talatin da biyar (35,000) ne suka kamu. Sai dai zuwa yau, June 2, 2020, sun ragu zuwa mutane dubu goma sha-shida ne, da dari bakwai da arba’in da hudu (16,744) ne ke dauke da cutar.

 

Daga lokacin da Kasar Egypt ta fara fuskantar matsalar cutar ta COVID-19, mutane dubu ashirin da bakwai, da dari biyar da talatin da shida (27,536) ne suka kamu. Sai dai zuwa yau, June 2, 2020, sun ragu zuwa mutane dubu sha-tara, da dari shida da hamsin da bakwai (19,657) ne ke dauke da cutar.

 

Daga lokacin da Kasar Najeriya ta fara fuskantar matsalar cutar ta COVID-19, mutane dubu goma, da dari takwas da sha-tara ne suka kamu. Sai dai zuwa yau, June 2, 2020, sun ragu zuwa mutane dubu bakwai, da dari biyu da sittin da biyar (7,265).

 

Daga lokacin da Kasar Algeria ta fara fuskantar matsalar cutar ta COVID-19, mutane dubu tara, da dari shida da ashirin da shida (9,626) ne suka kamu. Sai dai zuwa yau, June 2, 2020, sun ragu zuwa mutane dubu biyu, da dari takwas da casa’in da biyu (2,892).

 

Daga lokacin da Kasar Ghana ta fara fuskantar matsalar cutar ta COVID-19, mutane dubu takwas, dari biyu da casa’in da bakwai (8,297) ne suka kamu. Sai dai zuwa yau, June 2, 2020, sun ragu zuwa mutane dubu biyar, da dari biyu da saba’in da uku (5,273) ne ke dauke da cutar.

 

Daga lokacin da Kasar Morocco ta fara fuskantar matsalar cutar ta COVID-19, mutane dubu bakwai, da dari takwas da sittin da shida (7,866) ne suka kamu. Sai dai zuwa yau, June 2, 2020, sun ragu zuwa mutane dubu daya, da dari biyu da hamsin (1,250) ne ke dauke da cutar.

 

Daga lokacin da Kasar Cameroon ta fara fuskantar matsalar cutar ta COVID-19, mutane dubu shida, da dari biyar da tamanin da biyar ne suka kamu. Sai dai zuwa yau, June 2, 2020, sun ragu zuwa mutane dubu biyu, da dari bakwai da tara (2,709) ne ke dauke da cutar.

 

Daga lokacin da Kasar Sudan ta fara fuskantar matsalar cutar ta COVID-19, mutane dubu biyar, da dari daya da saba’in da uku (5,173) ne suka kamu. Sai dai zuwa yau, June 2, 2020, sun ragu zuwa dubu uku, da dari uku da hamsin da uku (3,353) ne ke dauke da cutar.

 

Daga lokacin da Kasar Guinea ta fara fuskantar matsalar cutar ta COVID-19, mutane dubu uku, da dari takwas da tamanin da shida (3,886) ne suka kamu. Sai dai zuwa yau, June 2, 2020, sun ragu zuwa dubu daya, da dari biyar da casa’in da shida (1, 596) ne ke dauke da cutar.

 

Daga lokacin da Kasar Senegal ke dauke da cutar ta COVID-19, mutane dubu uku, da dari takwas da talatin da shida (3, 836) ne suka kamu. Sai dai zuwa yau, June 2, 2020, sun ragu zuwa dubu daya, da dari takwas da talatin da tara (1, 839) ne ke dauke da cutar.

 

Daga lokacin da Kasar Djibouti ta fara fuskantar matsalar cutar COVID-19, mutane dubu uku, da dari bakwai da saba’in da tara (3, 779) suka kamu. Sai dai zuwa yau, June 2, 2020, sun ragu zuwa dubu biyu, da dari daya da arba’in da bakwai (2, 147) ne ke dauke da cutar.

 

Daga lokacin da Kasar Ivory Coast ta fara fuskantar matsalar cutar ta COVID-19, mutane dubu uku, da ashirin da hudu (3, 024) ne suka kamu. Sai dai zuwa yau June 2, 2020, sun ragu zuwa mutane dubu daya, da dari hudu da casa’in (1, 490) ne ke dauke da cutar.

 

Daga lokacin da Kasar Gabon ta fara fuskantar matsalar cutar ta COVID-19, mutane dubu biyu, da dari takwas da uku (2, 803) ne suka kamu. Sai dai zuwa yau, June 2, 2020, sun ragu zuwa mutane dubu biyu, da hudu (2, 004) ne ke dauke da cutar.

 

Daga lokacin da Kasar Kenya ta fara fuskantar matsalar cutar ta COVID-19, mutane dubu biyu, da casa’in da uku (2, 093) ne suka kamu. Sai dai zuwa yau, June 2, 2020, sun ragu zuwa dubu daya, da dari biyar da ashirin da uku (1, 523) ne ke dauke da cutar.

 

Daga lokacin da Kasar Somalia ta fara fuskantar matsalar cutar ta COVID-19, mutane dubu biyu, da tamanin da tara (2, 089) ne suka kamu. Sai dai zuwa yau, June 2, 2020, sun ragu zuwa mutane dubu daya, da dari shida da arba’in da tara (1, 649) ne ke dauke da cutar.

 

Daga lokacin da Kasar Mayotte ta fara fuskantar matsalar cutar ta COVID-19, mutane dubu daya, da dari tara da tamanin da shida (1, 986) ne suka kamu. Sai dai zuwa yau, June 2, 2020, sun ragu zuwa dari hudu da tamanin da tara (489) ne ke dauke da cutar.

 

Daga lokacin da Kasar Mali ta fara fuskantar matsalar cutar ta COVID-19, mutane dubu daya, da dari uku da hamsin da daya (1,351) ne suka kamu. Sai dai zuwa yau, June 2, 2020, sun ragu zuwa mutane dari biyar da hudu (504) ne ke dauke da cutar.

 

Daga lokacin da Kasar Ethiopia ta fara fuskantar matsalar cutar ta COVID-19, mutane dubu daya, da dari uku da arba’in da hudu (1,344) ne suka kamu. Sai dai zuwa yau, June 2, 2020, sun ragu zuwa mutane dubu daya, da casa’in da tara (1,099) ne ke dauke da cutar.

 

Daga lokacin da Kasar Niger ta fara fuskantar matsalar cutar ta COVID-19, mutane dari tara da sittin (960) suka kamu. Sai dai zuwa yau, June 2, 2020, sun ragu zuwa mutane arba’in da bakwai (47) ne ke dauke da cutar.

 

Daga lokacin da Kasar Tunisia ta fara fuskantar matsalar cutar ta COVID-19, mutane dubu daya, da tamanin da shida (1, 086) ne suka kamu. Sai dai zuwa yau, June 2, 2020, sun ragu zuwa mutane saba’in da uku (73) ne ke dauke da cutar.

 

Wannan rahoton bincike da aka farawa bincinawa a sama, ya tabbatar da cewa, zuwa kwanan Watan June 2, 2020, jumlar adadin mutanen da aka hakkake sun kamu da cutar ta COVID-19 a duk fadin Kasashen na Afurka, sun kai kimanin mutane dubu  dari da hamsin da biyar, da dari biyu da sittin da daya (155, 261) cifcif.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: