Bincike ya tabbatar mana da cewa, wani Kifi da ake kira da suna Whale shark a Turance, shi ne kifi mafi girma da aka taba kamawa a Duniya. Wato a Hausance dai a iya bayyana wannan kifi da cewa, babban Kifin da ake samu a Teku. Kuma an kama wannan Kifi ne a Tekun kasar Thailand, a shekarar 1919, wato kimanin shekaru 87 kenan da suka wuce.
Tsawon wannan Kifi dai ya kai kafa 59, kuma ba wai gamdakatar a kai ba, dama dai shi jinsin kifi na Whale shark, shi ne jinsin kifi da aka dauka a matsayin kifi mafi girma a Duniya, inda bisa al’ada babban kifi na Whale shark ya kan kai tsawon kafa 45, a nauyi kuwa ya kan kai har Ton 15, wato kimanin buhu hatsi 150 kenan.
An fara gano kifin Whale Shark a watan Afrilun 1828, lokacin da aka gudanar da wani bincike a dakin bincike na kimiyya a kan wani karamin Whale shark da aka kama, wanda tsawonsa ya kai kafa 15 a kasar South Africa. Kuma daga baya an samu cikaken bayanin wannan kifi daga wani likitan sojoji mai suna Andrew Smith, tare da taimakon wasu Sojoji ‘Yan kasar Birtaniya wadan da suka yi kaka-gida a birnin Cape-town, inda a shekarar 1849 aka radawa wannan kifi suna Whale shark. Kuma ya samu wannan suna ne saboda tsananin girmansa da kuma yanayin cin abincinsa.
Gashi dai Shark ne, amma mai girma da yanayin cin abinci Irin na Whale.
Ana samun nau’i na irin kifin Whale shark a Tekunan da suke a bangaren kasashen Duniya masu zafi. ko da dai, bincike da aka yi na kimiyyar halittun ruwa na baya-bayannan, ya tabbatar da cewa, yawansu yana raguwa.