El-Zaharaddeen Umar" />

Killace Daura: Dole Mutane Su Fito Neman Abinci Idan Ba So Ake Su Mutu Ba -Hon Sirika

Kwamishinan yada labarai na jihar Katsina kuma shugaban kwamitin wayar da kan jama’a akan matsalar Cobid 19 Hon. Abdulkarin Yahaya Sirika ya bayyana cewa dole mutane Daura su fita sayan abinci ko neman magani idan ba su ake su mutu ba.

Duk da dokar ta bacin da aka kakabawa Daura, amma jama’a na cigaba da yin hada-hadarsu, shin ko Hon. Kwamishina ya ga wadannan mutane tunda ya zagaya cikin garin Daura?, sai ya ce shi kam bai ga kowa ba, kuma ko da an ga mutun bai wuce wanda zai je sayan magani ko abinci ba, saboda an ware wasu wurare domin yin haka.

Shugaban kwamitin yana wannan magana ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Daura lokacin da muka kai ziyarar gani da akan irin abubuwan da suke faruwa a garin na Daura dangane da dokar tana shiga da fita da gwamnati jihar Katsina ta sanya a ranar asabar din da ta gabata.

Hon. Sirika ya kara da cewa duk abinda aka ga gwamnatin ta yi to ta yi ne domin jama’a saboda haka wannan doka ta dan wani lokaci ce, kuma da zaran an samu abinda ake so, wannan abu zai kwaranye kamar ba a yi.

“Kuma abinda muke cewa shi ne, gwamnatin na nan tana kokarin wajan ganin ta tallafawa mutanen garin Daura saboda yanayin da aka shiga ciki, saboda haka muna kira ga masu kudin Daura da ‘yan kasuwa da ‘yan siyasa da su taimakawa mutane Daura domin aikin ba na gwamnati bane kadai” inji

A cewarsa tallafin da gwamnatin jihar Katsina zata bada ba zai dauki wani lokaci ba, saboda haka jama’a su kara hakuri, nan gaba kadan za su ga wannan sako na bangaran gwamnatin jihar Katsina.

Da yawan jama’ar da muka tattauna da su, sun koka akan yadda aka hana su fita kuma babu wani taimako da aka yi masu duk da kasancewar mafiyawan mutane sai sun fita suke neman abinda za su sanya a bakin sati.

Haka kuma mun lura da cewa jami’an tsaro ba su takurawa kowa ba, domin jama’a na cigaba da yin huldarsu a kofar gidajansu, wasu kuma na ta yi akan titi wasu kuma na zaune a majalisa a ya yin da wasu ke cikin gidajansu domin bin doka da oda.

Exit mobile version