Connect with us

LABARAI

Kilu Ta Ja Bau A Kebbi Sanadin Kin Zaben Fitar Da Gwani Na APC

Published

on

A duk lokacin da mutane biyu ko fiye da haka ke neman wani abu daya kuma kowane daga cikin su yana iya daukar hanyar da duk ya ke ganin za ta iya kai shi ga cimma nasara to ba shakka akwai gumurzu.
Yanzu haka dai a kullum garin Allah ya waje a jihar Kebbi siyasa ta kan dauki wani wani sabon salo musamman a wannan lokacin da guguwar siyasa ta soma kadawa inda duk masu son tsyawa takarar mukaman siyasa dabam-daban ke ta fasowa daga ko ina don nuna aniyar su sai dai maganar zaben fitar da gwani don tsayawa takarar mukamai dabam-daban a zabe mai zuwa shi ne ya fi daukar hankali.
Kwanan nan ne dai jam’iyar APC mai mulki a jihar ta Kebbi tayi taron masu ruwa da tsaki wanda ya hada da yan majalisar dattijai da wakilai, yan Majalisar dokoki ta jihar, shugabannin jam’iyya a matakan jiha da kananan hukumomi da kuma shugabannin kananan hukumomi wanda jim kadan bayan kammala taron sai shugaban jam’iyyar ta APC a jihar Alhaji Bala Sani Kangiwa ya bayyana wa manema labarai cewa dukkan su dai sun yi ittifaki a kan shugaba Muhammadu Buhari ne dan takarar su a matakin shugaban kasa sannan kuma Sanata Atiku Bagudu shi ne dan takarar su na gwamna sannan kuma za a yi sulhu tsakanin yan takara a sauran mukamai sai dai idan a ka kasa samun daidaituwa tsakanin yan takarar za a yi zaben wakilai watau zaben delegates.
Wannan maganar fa ba ta yi wa yayan jihar dadi ba musamman wadansu yan takara da ke ganin idan aka yi zaben fitar da gwani bisa gaskiya za su iya kai wa ga tsayawa takara da jam’iyyun adawa a lokacin zaben game-gari mai zuwa a shekarar 2019.
Alhaji Sani Fari Zuru wanda bai goyi bayan wannan maganar ba kuma ya bayyana wa wakilin mu da cewa za su kalubalanci duk wanda ke ganin ba za a yi zaben fitar da gwani ba a zaben gwamna ba inda ya ke cewa maganar ba za a yi zaben fitar da gwani ba a musamman Yar tike ba ya baiwa yan Nijeriya mamaki saboda idan shugaban jam’iyyar APC Adams Oshimole da kuma shugaba Buhari za su amince tare da ba da umarnin yin haka sannan a jiha wadansu su na daga su ce ba za su yi ba wannan ya san wa sanin da yan Nijeriya suka yi wa shugaba.
Sannan kuma hana Ibrahim Mera ko kuma wani shiga takara ba demokuradiyya ba ce, ya kamata duk wanda ya zo shugabanni su kashe shi amma a ce sai dantakara ya zo ofishin jam’iyya amma ya tarar duk sun gudu wannan ba a shirya gaskiya ba, wannan yar manuniya ce da ke nuna wa talakawa ba a tare da su kuma ba a yi musu aikin komai ba. Idan har gwamnati ta yi wani abin a zo a gani bai kamata ba a ce tana jin tsoron wani dantakara ba sai ta bar kowa ya shigo da irin ta sa rawa.
Ya kuma ambato maganar wai an yi matsaya daya a kan a matakin shugaban kasa Buhari ne dantakarar su sannan a jiha kuma Atiku Bagudu ne wannan maganar banza ce kuma suna yaudarar kawunan su ne saboda tuni Shugaba Buhari ya ya yarda da duk wanda ke son takara da shi ya fito a yi zabe kuma na yar tike saboda haka a nan jiha ma haka za a yi in sha Allahu.
Alhaji Sani Fari ya gargadi gwamnatin jihar Kebbi da kuma yan barandan ta da su daina jin tsoron duk wani dantakara su daina gudu suna barin ofis, a maimakon haka ya kamata su rinka karbar duk dantakarar da ya zo saboda kaucewa maimaitawar tarihi a bisa ga abin da ya faru a jam’iyyar PDP shekarar 1999 a lokacin da ta ki tsayar da Marigayi Alhaji Garba Koko wanda yin haka kai Sanata Aliero darewa bisa ga kujerar gwamna alhali PDP tana da kananan hukumomi goma sha shida (16) ita kuma APP tana da biyar (5) kacal.
Ya kuma shawarci Atiku da ya fito fili ya gaya wa duniya irin ayukkan da ya aiwatar da billiyoyin kudaden da gwamnatin tarayya ta turo masa tun da ya hau mulki wanda ta nan ne talakawa za su sake zaben sa idan ya cancanci a sake zaben sa idan kuma bai cancanta ba sai su yi waje rod da shi, amma fa ya sani jihar Kebbi ta tara masana ta ko wane fanni saboda haka duk abin da ya amso ana biye da shi kuma an kididdige.
Binciken jin ra’ayi da wakilin mu ya gudanar ta karkashin kasa yana nuna al’ummar jihar sun fi raja’a ne a kan rashin aiwatar da zaben kato bayan kato yana iya sanya tarihi ya maimaita kan sa inda a zaben shekarar 1999 wanda a lokacin jam’iyyar PDP tana da kananan hukumomi goma sha shida amma ta rasa gwamna sanadiyyar yin gaban kan ta wajen tsayar da dan takarar da jama’a ke so wanda ya baiwa Sanata Adamu Aliero dantakarar jam’iyyar APP galaba a kan marigayi Kanar Bello Kaliel wanda ba shi ne ra’ayin mutanen jihar ba saboda a wannan lokacin marigayi Alhaji Garba Koko ne mutane ke so saboda haka sai duk jiga-jigan siyasar su ka umarci magoya bayan su da su yi angulu-da-kan-zabo (kwakwa-lema).
Har wa yau dai yayan jihar jihar Kebbi ta Kebbi a sanadiyyar wata jita-jitar da ke yawo a cikin jihar wai shugaba Buhari zai tsoma bakin sa a cikin wannan badakalar, sun soma guna-gunin idan har haka ta kasance to ba shakka Buhari bai yi wa yayan jihar adalci ba saboda sun dade suna korafi a kan gwamnatin Sanata Atiku Bagudu tun kama daga rashin baiwa manoma bashin kudin da gwamnatin tarayya ta umarce shi da ya bayar amma ya yi gaban kan sa, hana wa ma’aikatan jihar hakkokan su na kudin hutu da kuma yan fansho wanda har sai da ta kai ga yan fanshon suka dauki matakin yin gangami don gudanar da Sallar Allah tsine, ya zuwa rashin tabuka wani aikin a zo a gani duk da irin billiyoyin da gwamnatin tarayya ta turo wa jihar ba ko sau daya ba amma har yanzu bai ce komai ba.
Har wa yau dai binciken ya nuna shari’ar da Atiku Bagudu ke yi da Janar Bello Sarkin Yaki ta zabtare kaso mai yawa a cikin dukiyar da ya kamata a yi wadansu ayukkan more rayuwar yayan jiha.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: