Kimanin Masarar Naira Biliyan 30 Aka Yi Asara Sakamakon Matsalar Tsaro A 2020 – Manoma

Manoma

Don magance hare-hare yayin da suke noma amfanin gona a gonakinsu, manoma sun yanke shawarar aiwatar da ayyukan noma a rukuni na mutane 100, 200 ko 300, kamar yadda aka ambata a ranar Talata.

 

An kuma tattaro cewa, masu harkar masara sun yi asarar kimanin metric tan miliyan 10 na masara da kudinta ya kai Naira biliyan 30 saboda rashin tsaro a kakar noman da ta gabata.

 

Jami’an kungiyar manoma ta kasa baki daya sun bayyana cewa, dole ne manoma su kirkiro hanyoyin da zasu bijire wa hare-haren ‘yan bindiga da makiyaya da suka mamaye gonakinsu.

 

Sun shaida wa manema labarai cew, duk da cewa hakan ya yi tasiri a wasu jihohin, amma hakan ya takaita yadda manoma za su iya noma filaye masu yawan gaske.

 

“Wannan ya taimaka ta fuskar tabbatar da tsaro a gonaki da manoma, amma wannan adadi mai yawa ana takura shi zuwa wani yanki ne saboda rashin tsaro,” in ji Mataimakin Shugaban kungiyar manoma ta Nijeriya, Daniel Okafor.

 

Ya kara da cewa, “akwai yawaitar ‘yan bindiga da satar mutane a Nijeriya. Manoma ba sa zuwa gonakinsu kamar yadda suke yi a baya. Idan za su je gonaki a wannan karon sai su tafi cikin hadin gwiwa.”

 

“Suna zuwa rukuni-rukuni. Dole ne su zama da yawa kafin su tafi gonaki, musamman a yankunan da ke da matsala. Ba haka ba ne a da. Maimakon haka, kafin yanzu za ka iya zuwa gonarka kai kadai, tare da iyalanka ba tare da tsoron wani hari ba. Amma yanzu ba za ka iya zuwa gona tare da iyalanka ba, maimakon haka sai ka tafi tare da hadin kan mutane. Wasu lokuta wadannan hadin gwiwar na iya zama sama da mutane 100, 200 ko 300. Dole ne mu fito da wannan matakin.”

 

Okafor, duk da haka, ya bukaci Gwamnatin tarayya da ta magance matsalolin tsaro a Nijeriya, yana mai jaddada cewa, baya ga mummunan tasirinsa kan farashin abinci, hakan yana shafar karfin manoma na samar da amfanin gona don fitarwa.

 

Haka zalika, Shugaban manoman masara, masu sarrafawa da masu kasuwacinta a Nijeriya, Dakta Edwin Uche, ya shaida wa wakilinmu cewa, shawarar da manoma suka yanke ita ce ta asali don kare kansu da amfanin gonarsu daga cutarwa.

 

Ya yi nuni da cewa, hakan ya zama dole saboda manoman masara kadai sun yi asarar kimanin Naira biliya 30 saboda rashin tsaro a daminar da ta gabata.

 

Uche ya ce, “mun yi asarar sama da metric tan miliyan 10 na masara saboda rashin tsaro a daminar da ta gabata kuma hakan ya yi matukar tasiri ga noman mu. Wannan metric tan miliyan 10 ya kai biliyoyin nairori.

 

“Muna magana ne a kan kusan Naira biliyan 30 da aka rasa saboda rashin tsaro a lokacin noma daya. Kuna iya ganin cewa yana da kudi da yawa kuma wannan  don noman masara ne kawai. Amma zan iya gaya muku cewa ta shafi dukkan albarkatu kamar su shinkafa, masara, wake, da sauransu.”

Exit mobile version