Daga Baƙir Muhammad
Masana kiwon lafiyar ƙwaƙwalwa sun yi gargadin cewa kallon hotuna da bidiyon batsa a Intanet na canza kwayar halittun ƙwaƙwalwar mutane musamman ma yara da suka balaga.
Masanan sun faɗi haka ne a wani babban taron duniya da aka kammala a Rome a kan hatsarin batsa da yara ke fuskanta a duniyar Intanet.
Donald Hilton wani babban likitan ƙwaƙwalwa a Amurka ya yi gargadi kan mummunan tasirin da bidiyon batsa a intanet ke yi a ƙwaƙwalwar yara.
A wajen taron masana sun yi nazari tare da tattauna illar kallon bidiyon batsa a ƙwaƙwalwar yara.
Masana sun ce halayyar ƙwaƙwalwa na canzawa a yayin da take nazari ko karatu, kuma yakan zama illa idan aka takura ƙwaƙwalwa.
An bayyana cewa matasa na shafe lokaci suna kallon bidiyon batsa domin ƙoƙarin gamsar da kansu ta hanyar wasa da al’auransu da hannu a yayin da suke kallon bidiyon na batsa.
Taron ya yi kira ga iyaye su farga su lura wajen ɗaukar matakan kula da dabi’un ‘ya’yansu tare da yin kira ga mahukunta su karfafa dokokin kare kananan yara.