KIMIYYA: Manyan Wayoyi Sun Sa An Daina Yayin Wasu Abubuwa Biyar

Bakir Muhammad

1-Kyamarar daukar Hoto (Camera): Sanadiyar fitowar manyan wayoyi kamar su “Android” da “iPhone” yasa mutane da dama sun daina amfanin da kyamara ta daukar hoto, ganin yawancin wayoyin suna da kyamara mai daukar hoto mai kyau sosai.

Sannan mafi yawan wayoyin basu kai kyama tsada ba, ga kuma saukin amfani, karin muhimmanci shine za ka ajiye hotonka a wayar duk dadewa. Ana iya daukar hoto (image) ko kuma hoto mai motsi (Bideo)

2-Akwatin Rediyo (Radio): Kafin fitowar manyan wayoyi kusan kowa yana da rediyo, ko ta jin kaset ko kuma karama ta jin labaru, amma daga fitowar manyan wayoyi zuwa yanzu mutane da dama sun daina amfani da akwatin Rediyo. Ana iya sa wakoki masu tarin yawa a manyan wayoyi ta yadda zaka saurare su cikin sauki, sannan duk yawansu zaka zabi wakar da kake son saurare cikin kankanin lokaci. Haka ma in labaru kake son saurare to wayoyin mafi yawansu ana iya kama tashoshin labaru dasu.

3-Agogo mai kararrawa (Alarm Clock): Ana amfani da wannan nau’in agogon domin tada mutum a barci, ko domin tunin wani abu, manyan wayoyi suna da nau’in wannan agogon, mai sauki amfani wanda in lokacin ya wuce to zai sake bada tazara na yan mintuna kafin ya sake kadawa domin tashin ko tunatar da mutum.

4-Na’urar Lissafi (Calculator): Kusan duk inda ake hada-hadar kudi to zaka samu na’urar lissafi, ko kuma dalibai a makarantu suma suna amfani da na’urar don lissafi, fitowar manyan wayoyi ya matukar rage amfani da nau’rar lissafi kasancewar dukkan wayoyi suna da nau’in na’urar lissafi, wacce mutum zai ga bashi da bukatar mallakar na’urar lissafi tunda ga wayar hannu.

5-Agogon Hannu (Watch): Daya ne daga cikin abubuwa da akayi yayin amfani dasu sosai, ana amfani da agogo don ganin lokaci ko kuma ado, bayan fitowar manyan wayoyin akasarin mutanen da suke amfani da agogon hannu sun rage amfani da shi kasancewar duk wayoyi suna da lokaci akansu, gashi mafi yawan lokuta ba sai an yi ma lokacin saiti sabanin na agogon hannu da yake yawan gocewa.

Exit mobile version