Bakir Muhammad
Matsalar satan motar hawa wata matsala ce da aka dade ana fama da ita, wata motar idan aka sace ta to ta tafi Kenan har abada, wata kuma ayi sa’a a gano ta bayan wani lokaci. Wani kamfani a California na kasar Amurka ya fito da wani dan kankanin abu da ake likawa a cikin mota, wanda ake mishi saiti ta manyan wayoyin hannu wato (Smartphones).
Shi dai wannan abin yana amfani ne da fasahar gano guri a saukake ta (GPS), ana mishi saiti ne da wayar hannu, ta yadda duk inda aka shiga dashi to a take kana dubawa da wayar GPS din zai nuna maka daidai wajen da motar take, gashi ba shi da girma ko kadan don haka ko ina ana iya lika shi ta yadda ba wanda zai gane cewa an lika shi a wajen, sannan ba shi da tsada.
Karin amfanin wannan abu shine, ana iya lika shi a jikin ‘yar karamar jikar aje kudi da katin shaida wato (Wallet) ko jikin mabuden kofa, ta yadda in ka jifar da su kawai sai ka duba a wayar ka ta hannu a in aka jefar don ka dawo da abinka.
Babbar Matsala ce Yawan Manyan Wayoyi a Hannun Yara Masu Tasowa
Masana da dama sun yi nuni akan matsalolin manyan wayoyi a hannu yara masu tasowa, wannan matsalar ta zama ruwan dare matuka, ko’ina akwai ta, an yi kiyasin yara kashi 50 cikin dari suna amfani da wayar hannu, kuma dukkansu suna tsakanin shekaru 13-19 ne.
Hakazalika iyaye da dama sun damu da irin mugun sabon da yayansu suke yi ma manyan wayoyin, sannan suna tsoron illolin da manyan wayoyin ka iya jawowa, misali an danganta manyan wayoyi da cire ma yara tausayi a zuciyoyinsu, ta yadda zaka ga ya rage musu shakowa da mutane, ko kuma rashin damuwa da halin da wani yake ciki, ko kuma su zamanto masu keta.
Bincike ya tabbatar mafi yawan yara masu amfani da manyan wayoyi suna da wasu dabi’usabanin yara da basa yin amfani da manyan wayoyi, misali rashin gaskiya, halaye da suka saba ma al’adun yau da kullum, koyan wasu ayyuka na asha misali shaye-shaye ko kalace-kalace na batsa da sauransu.
Abin da yafi daga ma iyaye da masana hankali a cikin wannan matsala gaba daya shine, yadda manyan wayoyi suke sa yara su daina maida hankali a karatu, kasancewar wayoyi suna da wasanni masu dauke hankali (Games) da kuma kalace-kalace (Bideos) wannan ya sa mafi yawan yaran da suke amfani da wayoyin hannu basa maida hankali a karatunsu.
Maganin wannan matsala itace, ta farko, a zaunar da yaro a mishi nasiha kan yadda zai yi amfani da wayar ta hanyar da ya dace, na biyu, a takaita musu amfani da wayar, misali a hana su barci da wayar a tare dasu, a hana su amfani da ita a yayin cin abinci, da kuma hana su zuwa makaranta da ita.