Tare Da El-Zaharadeen Umar, Katsina 08062212010:
Babu shakka babu wanda ke musun irin halin kunci da ilimi ya tsinci kansa a Nijeriya ba musamman yankin arewa, saboda irin koma bayan da yake samu bisa dalilan hare-haren ‘yan bindiga da kuma cutar korona da ta addabi duniya da kuma Nijeriya baki daya.
A dalilin haka, al’amura da suka shafi ilimi sun samu tasgaro da koma baya a yanki arewa inda har aka rufe wasu makarantu bayan tafiya yajin aikin Malamai jami’a da ya yi sanadiyar tabarbarewar harkar Ilimi.
Ana cikin wannan hali ne, sai kuma ga wata sabuwar annoba da ta iske banagaran ilimi bayan kassara bangarorin tattazlin arziki da Noma da sauran al’amaru, sai sabon salon kashe arewa wato satar dalibai ‘yan makaranta.
Bisa ga haka wasu iyayen tuni sun yanke kauna da komawar yaransu karatu irin na kwana, wasu kuma sun hakura da maganar karatun Boko, wasu kuma sun dage sai ‘ya ‘yan su sunyi tunda su ba su yi ba.
Ana cikin kukan targade sai kuma ga kariya, a jihar Katsina an wayi gari, an bayyana sakamakon jarabawa tun watanni biyu da suka gabata, amma banda na ‘yan asalin jihar Katsina sakamakin rashin biyar kudin da gwamnati bata yi ba.
Gwamatin jihar Katsina ta sha yin ikirarin cewa tana kashe miliyoyin nairori game da biyan kudin jarabawa, amma dai a wannan karon shiru kake ji wai Malam ya ci shirwa, ba amo ba labari, abinda ya jefa da yawan iyayan raya cikin halin rashin tabbas game da karatun yaransu.
An shiga wani irin yanayi da wasu daga cikin ‘yan asalin jihar Katsina dalibai na fuskatan rasa guraban karatu a wasu jami’o’in kasar nan sakamakon kin biyan kudin jarabawar NECO da gwamnatin jihar bata yi ba.
Ya zuwa yanzu ana iya cewa, daliban ‘ya ‘yan talakawa ne wadanda gwamnatin jihar Katsina ta yi wa alkawarin biyawa kudin jarabawar NECO suna cikin tsaka mai wuya, saboda yadda suka zako su ga sakamakon jarabawar NECO da suka yi a shekarar 2020
Rahotanni da dama sun bayyana yadda uwayan yara suka kai kukan su ga hukumomin da wannan al’amari ya shafa kai tsaye wato ma’aikatar Ilimi ta jihar Katsina domin jin inda aka kwana game da wannan kalubale da yaransu ke fsukanta
Sai dai kamar yadda bayanai ke nuni, a halin da ake ciki daga bangaran hukumar Ilimi babu wata magana abin dogaro wajan warware wannan matsala, ta biyan kudin jarabawar dalibai ‘yan asalin jihar Katsina.
A dadin daliban da suke jiran wannan sakamakon jarabawa suna da da ywan gaske wanda gwamnati ta ce zata biyawa kudin NECO wanda yanzu haka suke jiran tsammani fitowar wannna sakamako domin tunkarar mataki na gaba.
Haka kuma jami’o’i a Nijeriya tuni suka fara yin jabarawar share fagen shiga jami’o’in domin baiwa dalibai dama su gwada basirar su sannan su samu tikitin shiga jami’ar amma dai rashin samun wannan sakamako na NECO ya zama karfen kafa a wannan lokaci.
Akwai iyayan yara da suke da’awar cewa sune da kansu suka biyawa yaransu kudin jarabawar ba wai gwmanati ba, amma dai sun biya kudin ne a makarantun gwamnati saboda haka suke kallon babu wani dalili da zai sa a rikewa ‘ya ‘yan su sakamakon jarabawar.
Wannan al’amari dai ya fara kamari ne a lokacin da hukumar shirya jabarawa ta kasa wato NECO ta bayyana sakamakon jarabawar ta shekarar 2020, sannan suka saki ta makarantun kudi (pribate Schools) wannan ne ya kara daga hankali iyayen yara game da sanin makomar ta ‘ya ‘yan su.
Sannan gashi sauran jami’o’I a Nijeriya sun saka ranar yin jarabawar share fagen shiga jami’io’in wanda wasu iyayan da kuma daliban ke ganin za su rasa wannan damar a wannan shekara, musamman ganin irin yadda karatu ke fuskatar baban kalubale a yankin arewa.
Jami’ar Bayero da ke Kano tuni sun shirya irin wannan jarabawa ta shafe fagen shiga jami’o’i kuma dalibai ‘yan asalin jihar Katsina da suka yi dogaro da jarabawar NECO sai dai su tari wata shekarar domin an riga an gama.
Wani abinda ya kamata kowa ya sani shi ne, yadda jami’o’i suka sanya wata doka cewa duk dalibin da ke san shiga jami’a to sai ya gabatar da sakamakon jarabawarsa kuma gashi da yawan daliban sun dogara ne da wannan NECO
Haka kuma akwai wata babar barazanar da ke tafe wanda iyaye tare da daliban suke neman kauce mata domin ta fi ta sauran matsala, ita ce wanda hukumar bada takardun shiga jami’o’I ke neman rufe nata tsarin wato JAMB.
Wannan labari na neman kara jefe dalibai ‘yan asalin jihar Katsina cikin halin rashin tabbas game da makomar karatunsu na wannna shekarar ta 2021 saboda rashin samun wancan sakamakon jarabawa ta NECO da suka ce gwamnatin taki biyan kudin saboda wasu dalilai nata.
Idan aka tafi a haka gwamnatin jihar Katsina bata yi wani sabon yunkuri ba, lallai akwai adadin daliban ‘yan asalin jihar Katsna da za su rasa guraban karatu a wasu jami’o’I da ke kasar nan.
Sannan kin bayyana dalilin rashin biyan wadannan kudadai da ake ganin ba su taka kara sun karya ba, ya sa wasu na ganin kamar gwamnati ta shigo da siyasa a cikin harkokin ilimi.
A baya can gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya sha fada da bakinsa cewa ilimi na daya daga cikin abubuwa da gwamnatinsa zata ba mahimmanci, kuma an ga irin kokarin da ya yi a wannan bangare to sai dai ana mantawa da wancan kokari, yanzu ana kallon matsalar da ake kokarin jefa ‘ya ‘yan talakawa acikinta.
Duk da irin wannan cece kuce da ake yi, mun yi yunkurin ji daga bakin wadanda wannan al’amari ya shafa a bangaran gwamnatin wato ma’aikatar Ilimi wanda yake ita ce ke da alhakin fyede biri har wutsiya game da wannan tirka-trika.
Sai dai kash! hakarmu bata cimma ruwa ba, domin mun kira kwamishinan ilim na jihar Katsina, Farfesa Badamasi Lawal Charanci domin jin matsayar gwamnatin jihar Katsina akan wannan muhimmin batu, bai dauki waya ba, kuma an tura masa sakon kar ta kwana babu amsa har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Muna rokon Allah ya baiwa iyayan raya da su kansu yaran mafita akan wannan al’amari da suke kallon ana wasa da makomar rayuwarsu, domin ance ilim gishirin zaman duniya kuma matasa sune kashin bayan kowace irin al’umma.