Daga Khalid Idris Doya,
Kungiyar Likitoci ta Kasa (NARD) ta bukaci mambobinta da su fara shirye-shiryen tsunduma yajin aikin gama-gari a dukkanin fadin kasar nan daga ranar 31 ga watan Maris din nan na wannan shekarar.
Bayanai sun yi nuni da cewa wannan dai shine karo uku da Likitoci ke tsunduma yajin aikin gama-gari a cikin watanni tara kacal.
Kungiyar NARD ita ce babban kungiyar likitoci wacce ta kunshi likitocin gwamanti da na masu zaman kansu wadanda suka kasance na gaba-gaba wajen yaki da cutar Korona.
A watan Yuni da Satumban 2020 kungiyar ta shiga yajin aiki bisa rashin biyan ma’aikatanta albashi da kuma rashin ingataccen yanayin aiki.
A wasikar da shugaban NARD na kasa, Dakta Uyilawa Okhuaihesuyi da sakatare Janar, Dakta Jerry Isogun, suka fitar mai kwanan wata 18 ga watan Maris, 2021, inda suka nemi mambobin kungiyar da su tanadi kudin da zai rikesu domin shirin tafiya yajin aiki.
Yajin aikin na shirin faruwa ne sakamakon rashin aiwatar da wasu yarjejeniyar da kungiyar ta cimma da gwamnatin, wanda hakan ke nuni da cewa gwamnatin ta ki cika musu alkawuran da suka yi a tsakani.
Wasikar shelanta shirin yajin aikin mai lamba NARD/SG/2020/2021/180321/376 ta ce yajin aikin gama-gari ne kuma har sai Baabaa ta gani muddin suka tsunduma cikinta.
“Idan za ku iya tuna a zaman majalisar kolin kungiyarmu, an cimma matsaya baiwa gwamnati wa’adin mako biyu da ta gaggauta daukan matakan da suka dace kan bukatunmu da muka gabatar mata. Kuma idan za ku tuna din, NEC din a watan Janairu bada wa’adi wanda zai kare a ranar 31 ga watan Maris 2021. Mun bada wa’adin ne da tunanin za a shawo kan matsalolinmu kafin wannan ranar amma hakar mu ba ta cimma ruwa ba.
“Kan wadannan dalilan, muna neman mambobinmu da su shirya dukkanin ababen da suka dace gami da shirin tafiya yajin aikin gama-gari wanda zai fara aiki daga ranar 31 ga watan Maris.”
Shugaban kungiyar ya shaida cewar har zuwa yanzu alawus din da gwamnati ke biyan likitocin bai taka-kara ya karya ba, wanda suke neman gwamnati ta kara musu.
Ya ce, “A shekara da ta gabata, mun nemi su biya Inshura ga mambobinmu da suka rigamu gidan gaskiya. Gwamnatin tarayya ta ce su dai sun yi komai. Bayan shekara, babu wani mambanmu da ya samu inshoran nan.
“Har zuwa yanzu ana biyanmu alawus na hazard naira 5,000 yayin da mambobin majalisa suke amsar sama da naira miliyan 1.2 a kowace wata na hardship Alawus.
Okhuaihesuyi, ya kara da cewa ma’aikatar kwadago da samar da aikin yi, ta ki basu damar zaunawa domin tattauna muhimman ababen da suka dace.
“A ranar 26 ga watan Disamba, ya dace mu zauna da ma’aikatar kwadago ta tarayya amma daga baya an dage zaman zuwa wani lokaci har kuma zuwa yanzu babu wani abun da ya canza. Abun nan ya isa haka kawai.”