- Lauyoyin Malamin Za Su Gardaya Kotu
- An Fara Tantama Kan Yiwuwar Mukabala
Daga Abdullahi Muhammad Sheka,
Sarkin Kano na 14, Malam Mahammadu Sanusi II (Mai Murabus) ya yi kira ga daukacin malaman addini a Jihar Kano da su jingine duyk wani sabani da bamcance-bambance, su mara wa Gwamnan Jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, baya bisa takaddamar da ta taso kan fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, wanda ake zargi da bayar da fatawoyin da suka saba da koyawar addini da aka saba da su a jihar.
A wani bidiyon da Sanusi Murabus ya fitar, ya nuna goyon bayansa ga Gwamnatin Jihar Kano a karkashin jagorancin Gwamna Ganduje bisa matakin da ta dauka kan Sheikh Abduljabbar na hana shi gudanar da koyar da karatu ko bayar da fatawa da wa’azi a fadin jihar.
Sarkin ya kuma yi kira ga jama’ar Kano da su cigaba da tsayawa kan tafarkin da Shehu Usman Danfodiyo ya bari tun bayan Jihadin Usmaniyya.
A ta bakinsa, “mu Kano ba za mu tsaya akan komai ba sai abinda Shehu Usmanu Danfodiyo ya dora mu akai. Shi ne Akidar Ahlussunah Wal Jama’a.”
Sarkin ya kuma cigaba da cewa, “duk mutumin da zai zo, ko waye shi, ya fito mana da wani abu daban, ya kamata mu nuna masa cewa Kano ba za ta zama Markazee na wannan ba, kuma malaman Kano kun kyauta. A cigaba da abinda ake yi, kuma a cigaba da zama lafiya, sannan kuma wannan mataki da gwamna ya dauka, matakai ne da ya kamata a yaba masa akai kuma a goya musu baya.”
Idan dai za a iya tunawa, a makon jiya ne Gwamnatin Jihar Kano ta fitar da haramcin ga shehin malamin bisa zargin cin zarafin Manzon Allah (SAW), batun da ya sha karyatawa, yana mai cewa, yana kokarin fito da wasu kura-kurai ne dake jibge cikin litattafan Musulunci. Don haka ba shine ya kago maganganun ba, illa dai kawai yana kokarin wayar da kai ne, don a guje mu su. To, sai dai kuma irin wadannan karatu ba su yi wa wasu malamai masu fada-a-aji dadi ba, musamman bangaren ’yan Izalar jihar.
Jim kadan bayan sanar da sanya masa takunkumin ne kuma sai gwamnatin ta rushe tare da kwace wani fili daga hannunsa, wanda ta ce, ya mamaye shine a Filin Mushe dake unguwar Gwale ba bisa ka’ida ba, tana mai cewa, ta samu korafi ne daga al’ummomin unguwar.
Amma malamin ya shaida wa kafar yada labarai ta BBC Hausa cewa, wadannan abubuwa na faruwa da shine sakamakon kiyayyar dake tsakaninsa da wasu malamai da ya bamban da su ta fuskar fahimtar addini, wadanda ya ce, sun yi amfani da Gwamna Ganduje ne, saboda bai mara masa baya ba a zaben 2019, wanda ake ganin Gandujen ya sha da kyar.
Haka nan kuma Malam Abduljabbar din ya yi ta maimatawa cewa, yana kira ga dukkan malaman da suke da ja akan fatawarsa da su zo su yi makabaka da shi, don warware matsalar, inda kuam ya yi alkawarin cewa, zai janye tasa fahimtar matukar sun fi shi hujjoji masu kwari.
To, a shekaranjiya Lahadi ne kuma Gwamnatin Jihar ta sanar da cewa, za ta dauki nauyin shirya mukabala tsakanin malamin da sauran malaman da suke da jayayya da shi, a cikin wani lamari mai kama da jan linzamin doki kan dirar wa malamin da ta yi tun da fari.
Majiyoyi sun tabbatar wa LEADERSHIP A YAU cewa, hakan ya biyo bayan shiga tsakani da Kwamishinan Kula da Harkokin Addini, Dr. Baba Impossible, ya yi ne, wanda majiyar ta ce yana ganin cewa, ba a yi wa Sheikh Abduljabbar cikakken adalci kafin yanke masa hukunci ba, musamman idan aka yi la’akari da Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya, wanda ya bayar da damar fadin albarkacin baki da addini. Don haka ya nemi da a tattauna, don bai wa malamin dama, musamman ma don gudun kunyata a gaban kotu.
Bayanan sun kara da cewa, kwamishinan, wada shi ma malamin addini ne, yana so a gabatar da mukabalar ne, domin ko dai a samu damar fahimtar da shi cikin ruwan sanyi ko shi ya fahimtar da su manufarsa a fayyace ko kuma mukabalar ta zama wata hujja a gaban kotu nan gaba.
To, sai dai wasu bayanai da LEADERSHIP A YAU ta samu sun nuna cewa, akwai yiwuwar lauyoyin Sheikh Abduljabbar Kabara za su garzaya kotu, don nema masa ’yancinsa na fadin albarkacin baki, inda musamman suke ganin cewa, ana yayata abubuwan da ba shine ya fadi ba kuma manufarsa kenan ba.
Bugu da kari, yiwuwar zaman mukabalar, wacce gwamnatin jihar ta ce za ta dauki nauyin sanya su kai-tsaye a kafafen yada labaran jihar kuma a gaban wasu fitattun malamai daga wajen jihar, ya shiga tantama, saboda sharuddan da bangarorin ke namen kawowa a ciki.
Majiyar ta ce, yayin da manyan malaman dake jayayya da malamin suka ce ba za su bayyana da kansu a wajen mukabalar ba, sai dai tu turo almajiransu, shi kuma ya ayyana wasu malamai guda biyar da ya ce, sai da su kawai zai yi mukabalar.
Don haka da alama wadannnan batutuwa na neman jefa al’amarin cikin yiwuwar mukabalar a cikin shakku.