Connect with us

WA'AZIN KIRISTA

Kirista Da Zaman Lafiya

Published

on

Wurin Karatu – Matta 5:9: “Masu–Albarka ne masu–sada zumunta gama za a che da su yayan Allah” (Matta 5:9).

Addinin Kirista addini ne na zaman lafiya  a ta kowane fani. Addinin Kirista addini ne da ta kafu a kan zaman lafiya. Kirista bai zama chikaken Kirista ba,  matuka Kiristan ya zama mai zaman lafiya da kuma wanzar da zaman lafiya a aikace.

Addinin Kirista shine zaman lafiya, haka kuma zaman lafiya shine addinin Kirista. Anan Yesu Almasihu yana tabbatar wa masu sauraronsa da Kiristan duniya da cewa; “Kiristan gaskiya ko Kiristan duniya masu albarka ne masu – sada zumunta: gama za a che da su yayan Allah.”

Ma’anan wannan maganan shine, matuka mutum Kirista ne na gaskiya, to ba a raba shi da zaman lafiya. Kiristan gaskiya a ko ina yake ya zama wakilin Allah na zaman lafiya, shine chikaken bishara, watau shine maganar Allah. Domin duk addinin da bata koyar da  maganan zaman lafiya to ba chikaken addini ba ne.

Abinda ya bambanta addini Kirista da kowane irin addini shine zaman lafiya domin marubucin littafin ibraniyawa 12:14 yace:

“Ku nemi salama da dukan mutuane, da tsarkakewa wadda babu mutum da za shi ga ubangiji im ba tare da ita ba.”

Addinin Kirista ya umurci kowane Kiristan duniya daya nemi zaman lafiya da kowane irin mutum. Matuka Kirista ya nemi zaman lafiya da kowane mutum ko dukan mutane, shine alama cewa wannan mutumin Kirista ne na gaskiya. Bai cin neman zaman lafiya da dukan mutane. Kirista ba zai taba sami shigan mulkin Allah ba, in ba tare da tsarkakewan rayuwa da zuchiya. Watau duk Kiristan da ya nemi salama da dukan mutane, da tsarkakewa, to tabbas ne za shi sadu da Allah ubangijinsa a ranar karshe.

Yesu Almasihu na kara tabbatar wa Kiristan duniya da cewa alamar addinin gaskiya na kunshe da maganan zaman lafiya. In kuwa addini na kunshe da zaman lafiya ne, to gaskiyan shine, zama da tsarki da zaman lafiya watau Danjuma ne da Danjummai, ba a rabasu. Domin gadon mulkin Allah Ubangiji, ba a raba ta da zaman lafiya da zaman tsarki.

Addinin Kirista, addini ne da ana rayuwan tsarki ne, watau tsarkin zuchiya. Tsarkin zuchiya shine ke kawo Kirista har zai zauna lafiya da kowane irin mutum. Watau tsarkin zuchiya shine dalilin kauna in kuma akwai kauna to zaman lafiya tsakanin Kiristan duniya da kowane irin mutum ya zama doles, domin shine chikon addinin Kirista.

Kiristan gaskiya ya sani da cewa matuka baya zaman lafiya da marasa bin Yesu Almasihu in laifin daga gefensa ne, to babu yadda za a gan hasken Yesu Almasihu a rayuwansa kuma babu yadda zai yada bisharan cheto.

Yesu Almasihu ya tabbatar wa dukan Kiristan duniya da cewa kune gishirin duniya da fitilan ko hasken duniya (Matta 5:13 – 16).

Rayuwan Kirista na gaskiya a bayane ta ke, domin Allah Ubangiji ya bambanta Kirista da kowane irin mutum tawurin rayuwan sa. Rayunwan da ya bambanta Kirista da kowane irin mutum duniya na kunshe ne tare da irin zaman lafiyan Kiristan duniya da ke dabam da kowane irin zaman lafiya da wasu ke kiran.

Marubucin littafin Romawa 12:18 ya kara assasa maganan zaman lafiya da Allah Ubangiji ya umurci Kirista tun assail da cewa:

“Idan ya yiwu, ku zama lafiya da dukan mutane, gwalgwadon iyawarku.”

Ana marubucin yace matuka yana yiwu wa, to yakamata kowane Kiristan duniya fa ya zauna lafiya da dukan mutane, gwalgwadon iyawar kowane Kiristan duniya da sauran mutanen duniya. Anan zaman lafiya gwalgwadon iyawar Kiristan duniya be da zai iya zaman lafiya da kowane iron mutum.

Watau ba a iya yin addinin Kirista na gaskiya ba tare da zaman lafiya ba. In babu zaman lafiya babu yadda Kiristan duniya zai iya zuwa Ikkelisiya ko Coci domin bautan Allah ubangijinsa. Matuka babu zaman lafiyan a duniya to Kirista bashi da kyakyawan mu’amula da zamantakewa mai kyau.

In mun dauki lokaci muka yi tunani mai zurfi sausai, to zamu gane da cewa zaman lafiya a kowane mataki shine garkuwan yin addini. Zaman lafiya a kowane mataki shine sinadarin kowane addini da kuma cigaban kowane addinin da kuma cigaban kowane kasa a duniya.

Zama lafiya shine arzikin kowane Al’ummah, zaman lafiya shine alaman addinin gaskiya. A chikin littafin Matta 5:9, Yesu Almasihu ya tabbatar wa dukan Kiristan duniya da cewa matuka Kiristan duniyan masu–sada zumunta ne su, to wajibi ne su zama yayan Allah.

Zaman lafiya ba wai zai bambanta mutum da wadansu ba amma itace ke iya mayar da masu imani yayan Allah. Domin tawurin zaman lafiya ubangiji Allah ya lallaci duniya. Tawurin zaman lafiya ne masu imani za su gaji mulkin ubangiji. Amma matuka babu zaman lafiya, rayuwan da zai kai mu ga imani zata yi nisa da mu sai gadon mulkin Allah zai zama mana da wuya.

Watau zaman lafiya shine tushe addinin gaskiya, zaman lafiya shine tabbacin zaman mu yayan Allah ubangiji. Zaman lafiya shine mafitan mu, matuka dai mu masu imani da Yesu Almasihu. Zaman lafiya ita ce manunin da cewa mu masu imani ne na gaskiya. Zaman lafiyan ne ka dai, ke iya bambanta mu da marasa imani. Zaman lafiya ita ce alaman cewa mu yayan Allah ne.

Domin tsananin zaman lafiyan Kirista ne ya mayar da Kiristan na gaskiya mai nasara da duniya. Zaman lafiya ne ya mayar da Kirista mahakurci kuma mawadaci a chikin kowane hali da ya sami kansa. Zaman lafiya ne sandin da Allah ya albarkaci Kiristan duniya a bayane a chikin rayuwa Kiristan duniya. Ba a zaman lafiya ba tare da gaskiya ba, kuma in da gaskiya a kwai yanci, in kuma akwai yanci to akwai cheto.

Allah Ubangiji yabamu zaman lafiyan a kowane irin mataki a rayuwan mu da kuma duniya gaba daya amin.

Shalom! Shalom!! Shalom!!!
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: