Fasto Yohanna Y.D. Buru" />

Kiristanci Rayuwa Ce

Wurin Karatu – Matta 5:16

“Haka nan ku kuma ku bari hasken shi haskaka a gaban mutane, domin su ga ayukanku masu – kyau, su girmama, ubanku wanda ke cikin sama” (Matta 5:!6)

Karban yesu Almasihu shine tushan  rayuwa Kirista a matsayinsa na mai imani da mutuwa da tashin sa daga rayuwa irin ta Kristi watau rayuwa na tsarki: Bin addinin Kirista, bin rayuwa iri na yesu almasihu a kowane mataki:

Rayuwa Kirista, wata rayuwa ne cike da kauna kuma rayuwan kauna irinta yesu Almasihu. Yesu Almasihu da kansa ya tabbatar mana da cewa bin sa rayuwa ne da ke dauke hankalin mutanen duniya. Ya kara bayane ne ga kowane mutum. Rayuwan Kirista bata boyuwa a ko ina a kuma kowane lokaci.

Rayuwa Kirista a kowane lokaci haske ta ke yi, matuka Kirista ya bayyana a ko ina domin rayuwan Kirista haske ta ke a kowane lokaci.

Rayuwan Kirista a ko ina da kuma kowane lokaci shi misali ne ga mutanen duniya. Matuka mutum Kirista ne to shi da bam ne da kowane irin mutum a ko ina domin rayuwan yesu da kuma hasken sad a ke cikin Kirista.

Duk wurin da Kirista ya bayyana, to duk komai game da rayuwansa Kirista ya boye kansa to boyuwansa bata boyuwa ko kadan. Baicin  rayuwan kowane Kirista na gaskiya haske ta ke a kuma ko ina. To ta halin yaya ne da Kirista zai iya ya boya har ba a sanshi a matsayin Kirista?

Kowane Kirista na gaskiya kadaran Allah ne shi. Domin kowane Kirista na gaskiya kainuwa da shen Allah ne. Kowane Kirista na kunshe da wata rayuwa da kowane mutum a duniya na sha’awa. Kiristan gaskiya mai tsaga gaskiya ne a kowane lokaci a kuma kowane mataki: Rayuwan kowane Kirista na gaskiya abin kwa kwayo ne ga kowane mutum kuma a ko ina ana amfani da rayuwan Kirista ne a kan yi misali da shi.

Rayuwan Kirista rayuwa ne na yi alheri ga kowane irin mutum domin rayuwan Kirista alheri ne daga Allah Ubangiji . Yin alheri ba umurni ne kadai ba, amma an kafa addini Kirista akan alheri ne.

Yesu Almasihu ya umurci kowane cikaken. Kiristan duniya da yayi rayuwa Kiristanci a ko ina domin mutanen duniya su gan bambancin. Tawurin ganin bambancin  rayuwan Kirista a aikace, tawurin kyawawan ayukansa, sai a girmama ubangiji Allah.

Da shike bin yesu Almasihu wata rayuwa ne musamma, to hakane ya kamata kowane Kirista ya yi rayuwa iri ta musamma da yesu Almasihu yayi. Rayuwan Kirista hake ne gareta, domin tsananin hasken ta shi ya sa bata boyuwa a ko ina Kirista ya ke. Domin manzo Bulus ya mutum na cikin Kristi  sabon halite ne, domin tsofofin alamura sun shude sabobin ne ke bayyana. (Ikorintiyawa 5:17)

Shudewan tsofofin alamura na tafiya tare da sabon rayuwa, halaiya masu kyan, kuma irin wannan rayuwan  shaida da ne ga duniya, da ke nuni da cewa wannan mutumin Kirista ne.

Domin Kirista sabon halita ne cikin Kirista, yana da tabbacin cetonsa. Rayuwan Kirista shaida ne da cewa yesu almasihu ya yantas da shi daga sarkokinshaidan. Rayuwan Kirista ya yi dabam a cikin furucinsa, da ayukansa a aboye ko a bayyane a ko ina ne a doron kasa. Rayuwan Kirista haskene ga wadanda ke cikin duhu.

Kowane cikaken Kirista baya tabayin rayuwa cikin Kristi ba tare day a tab rayuwan wadansu ba. Rayuwan Kirista na zama sanadin da wasu suka shiga addinin Kirista.

Rayuwan Kirista, wata rayuwa ne na ha kuri komai da kowa. Kirista na da wata rayuwa da Allah ya umurce shi day a kaunci makinyansa ya kuma yi wa masu tsananta masu adu’a. Rayuwan Kirista na kamun kai ne da kuma jimrewa a cikin kowane halin rayuwa.

Kirista na rayuwa ne aka dogara ga Allah a cikin komai da kuma rayuwa irin ta nasara da duniya. Yesu almasihu ya umurci kowane cikaken Kirista day a so wad an uwansa bil Adama abinda ya na so wa kansa.

Atakaice, ba za mu iya bayana dukan rayuwan Kirista a takaitacen lokaci kama haka ba. Domin rayuwan Kirista wata duniya a ne da bam. Domin kowane irin rayuwan Kirista na gaskiya darasi ne ga kowa da kowa. Rayuwa Kirista shien abin gwada dafi kai rayuwan Kirista rayuwan bin dokan kasa da kuma dokan Allah.

Ya Allah ka tabbatar mana da imaninmu ka kuma tabbatar mana da Aljanar mu, amin summa amin.

Shalom! Shalom!! Shalom!!!

 

Exit mobile version