Jamila Zhou, Sanusi Chen">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home BABBAN BANGO

Kirkire-Kirkiren Kimiyya Da Fasaha Ya Taimaka Ga Ci Gaban Beijing Mai Inganci

by Jamila Zhou, Sanusi Chen
April 5, 2019
in BABBAN BANGO
6 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

A cikin shekarun baya bayan nan, birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin ya shiga mataki na samun ci gaba mai inganci, wato ya fi mai da hankali kan ingancin kayayyakin da ake samarwa ta hanyar yin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha a birnin, a maimakon karuwan adadinsu kawai.

Kamfanin kimiyya da fasaha na Kuangshi wato MEGVII na Beijing yana yankin Zhongguancun na birnin Beijing, an kuma kafa shi ne a shekarar 2011, ya zuwa shekarar 2018, an zabe shi a matsayin daya daga cikin fitattun kamfanonin dake kwaikwayon tunanin dan Adam wato AI a bangaren hotunan bidiyo goma a fadin duniya, ayyukan da kamfanin ke gudanarwa sun kunshi fasahar tantance hoton fuska, da fasahar tantance hotun jikin mutum, da fasahar tantance hoton alamar hannu, da fasahar tantance takardar shaida, da fasahar tantance hotuna daban daban.

samndaads

Mataimakin shugaban kamfanin Xie Yinan ya yi mana bayani cewa, tun farkon kafuwar kamfaninsa, sun yi kokari matuka domin nuna fifikonsu inda suka yi amfani da fasahar zamani a bakin kofar kamfanin, misali sun kera na’urar tantance hoton fuska a bakin kofa, saboda a wancan lokaci, yana da wahala a yi amfani da fasahar, yanzu haka suna amfani da fasahar samar da bidiyon komai da ruwanka (IOT) wato Internet of Things, ta zamani.

Hakika ma’aikatan kamfanin kimiyya da fasaha na Kuangshi wato MEGVII suna ganin cewa, yin amfani da fasahar AI ba domin maye gurbin mutane ba ne, sai domin kara kyautata ayyukan da ake gudanarwa, makasudin kwaikwayon tunanin dan Adam, (AI) shi ne domin kara saukaka aikin mutane da kuma harkokin rayuwa, tare kuma da samar da alheri ga daukacin bil Adama.

Mataimakin shugaban kamfanin Xie Yinan yana ganin cewa, ainihin ma’anar yin kirkire-kirkire ita ce kyautata sana’o’i da kuma rage kudin da aka kashe kan su.

A yankin Zhongguancun, kamfanonin da suka yi kama da kamfanin kimiyya da fasaha na Kuangshi wato MEGVII suna da yawan gaske, a shekarar 2018, adadinsu ya kai sama da dubu 22, kwatankwacin adadin kudin shigarsu ya kai kudin Sin yuan biliyan 5800, adadin da ya karu da kaso 11 bisa dari idan aka kwatanta shi da na makamancin lokacin shekarar 2017.

Ya zuwa shekarar 2018, adadin kamfanonin kimiyya da fasahar zamani na birnin Beijing ya kai dubu 25, adadin da ya karu da kaso 25 bisa dari idan aka kwatanta shi da na shekarar 2017, adadin kamfanonin Unicom wato darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 1 a birnin ya kai 80, wato ko wace rana adadin sabbin kamfanonin kimiyya da fasahar zamani da aka kafa a birnin ya kai 199, kana adadin kwangilar fasahar da aka daddale shi ma ya karu da kaso 10.5 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2017.

Hakazalika, ya zuwa karshen 2018, adadin ’yancin mallakar fasaha na mazauna birnin Beijing dubu goma ya kai 111.2, kuma adadin bukatar rokon neman samun ’yancin mallakar fasaha da aka gabatar a birnin ya karu da kaso 13.6 bisa dari kuma adadin ’yancin mallakar fasahar da aka samu ya karu da kaso 15.47 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin shekarar 2017.

Yankin kirkiro sabbin fasahohi na unguwar E9 yana gabashin birnin Beijing, a da, yanki ne na wata masana’antar samar da kayayyakin madara ta Beijing. A shekarar 2012, aka sauyawa wannan masana’anta matsuguni zuwa yankin raya masana’antu na Yinghai na gundumar Daxing dake karkarar Beijing. Sannan a shekarar 2014, wannan tsohon yanki ya sauya fasalinsa zuwa wani yankin raya masana’antu da kamfanonin kimiyya da fasaha ko na al’adu. Kawo yanzu, an kafa masana’antu da kamfanoni fiye da 80, ciki har da manyan kamfanoni 3.

A wannan yankin kirkiro sabbin fasahohi na E9, akwai wani kamfanin da ya mallaki ilmin kimiyya da fasahohin zamani da yake ba da hidimomi ga sauran kamfanoni da hukumomin gwamnati da bankuna da kamfanonin sadarwa kusan dubu 1. Madam Cui Jingjing, babbar jami’ar kamfanin ta bayyana cewa, “Muna ba da hidimomi ga wadanda suke amfani da hidimominmu bisa fasahohin tantance mutum bisa sautinsa da fuskarsa, da kuma ba da hidimomi bisa fasahohin kwaikwayon tunanin dan Adam ta AI ga ayyukan tantance masu neman rance daga bankuna. Ban da haka, muna ba da hidima bisa bayanan zamani dake hannun kamfaninmu ga kamfanoni a lokacin da suke kula da kuma tantance dukiyoyi da farashin kayayyakinsu da dai makamatansu. A nan kasar Sin, yawan matsakaita da kananan masana’antu da kamfanoni ya kai wajen miliyan 65, galibinsu ba sa iya samun goyon bayan hada-hadar kudi. Muna ba su hidimomi ta hanyar nazartar bayanai, ta yadda za a iya tabbatar da ganin sun samu kudaden da suke bukata da kuma rage yawan kudin tafiyar da harkokinsu da suke kashewa a kullum.”

Birnin Beijing, wani tsohon birni ne da tarihinsa ya kai fiye da shekaru dubu 1, a lokacin da ake shiga sabon zamani, ana canja fuskarsa yana kuma zama wani birni dake cike da basira da kuma fasahohin zamani da aka kirkiro. Fadar Sarakuna dake cikin garin Beijing, an gina ta ne yau kusan shekaru 600 da suka gabata. A ’yan shekarun baya, bisa sabon halin da ake ciki, hukumar kula da ita ta kuma fitar da wasu kayayyakin tarihi, bisa fasahohin zamani, sannan bisa bukatun da masu yawon shakatawa suke da su wajen samun kayakyyakin zamani masu inganci a maimakon wasu kayayyakin nune-nunen al’adu kadai. Sakamakon irin wannan gyare-gyare, yawan kudin da hukumar kula da Fadar Sarakuna ta Beijing ta samu a shekarar 2017 ya kai RMB yuan biliyan 1.5 maimakon yuan miliyan 600 a shekarar 2013.

Yadda tattalin arzikin birnin Beijing yake samun bunkasa a ’yan shekarun baya, ya bayyana mana wani labari kan yadda ake sauya salon raya tattalin arziki a nan Beijing. A lokacin da ake yin watsi da tsoffin masana’antu wadanda ba su iya dacewa da sabon halin da ake ciki ba, ana kuma sa kaimi da raya tattalin arziki bisa fasahohin zamani da aka kirkiro. Sakamakon haka, birnin Beijing ya cimma burinsa na mayar da tattalin arziki irin na gargajiya ya zama sabon tattalin arziki, har ma ya samu ci gaba cikin sauri. Mr. Lin Keqing, mataimakin magajin birnin Beijing yana mai cewa, “A shekarar 2018, gudummmar da sabon tattalin arzikin ya bayar ga GDP na birnin ta kai kashi 33.2 cikin dari. Daga cikinsu, gudummawar da tattalin arzikin zamani, kamar na hada-hadar kudi, da ba da hidima bisa bayanai da ilmin kimiyya da fasahohin zamani ya bayar, ya kai kashi 67 cikin dari. Yanzu birnin Beijing ya kasance kamar wani abin misali ta fuskar kare al’adu da kuma bunkasa tattalin arzikin al’adu a duk fadin kasar Sin.”

A bayyane an lura cewa, ci gaban Beijing mai inganci yana da makoma mai haske.

SendShareTweetShare
Previous Post

Pauline Kedem Tellen: Macen Da Ta Kafa Tarihin Zama Mataimakiyar Gwamna A Arewa

Next Post

Daga Littafin Amanna (37)

RelatedPosts

Babbar Ganuwar Kasar Sin

Ziyarata: Ko Ka San Wani Abu Game Da Tarihin Babbar Ganuwar Kasar Sin?

by Jamila Zhou, Sanusi Chen
2 days ago
0

Babbar ganuwar kasar Sin, wato “The great wall of China”...

Nagartattun Al’adu Da Tunanin Da’a Na Kasar Sin Sun Ba Da Jagoranci Ga Ladabin Al’ummarsu

Nagartattun Al’adu Da Tunanin Da’a Na Kasar Sin Sun Ba Da Jagoranci Ga Ladabin Al’ummarsu

by Jamila Zhou, Sanusi Chen
4 weeks ago
0

A cikin shekaru sama da dubu biyu da suka gabata,...

Kauyen Longtan

Yadda Kauyen Longtan Na Lardin Fujian Dake Kasar Sin Ya Fita Daga Kangin Talauci

by Jamila Zhou, Sanusi Chen
2 months ago
0

Longtan, karamin kauye ne dake kan duwatsu cikin gundumar Pingnan...

Next Post

Daga Littafin Amanna (37)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version