Connect with us

LABARAI

Kirkiro Da Manhajar Daidaita Wa’azi A Duniya: Malamai Sun Yi Hannun Riga A Nijeriya

Published

on

*Manhajar Za Ta Amfanar Amma… Dakta Zubairu Madaki

*Hanyar Cusa Wa Jama’a Wahabiyanci Ne – Dakta Fatihu Bauch 

*Take Hakkin Wasu Bangare Ake Son Yi – Allaramma Idris Dauda

A ‘yan makwannin da suka gabata, mahukuntan kasar Saudiyya sun nuna yunkurin kirkiro da wata manhajar wayar hannu da za ta sa ido kan wa’azuzzuka da addu’o’i a masallatai domin bai wa masu ibada damar sanin ko mai wa’azi zai dade yana wa’azin ko a’a.

 

Sashen Hausa Na BBC Ya ruwaito Jaridar Al-Watan ta kasar Saudiyya na cewa Ministan harkokin Musulunci na kasar, Abdul Latif Al-Sheikh, ya bayyana cewa manhajar za ta bayar da damar sa ido a masallatai kan tsawon lokaci da kuma ingancin wa’azuzzukan duk minti kuma duk dakika.

 

A bisa wannan, a nan Nijeriya LEADERSHIP A YAU JUMA’A ta tuntubi wasu malamai domin bayyana fahimtarsu kan manhajar da kuma mahangarsu ta yiwuwar amfani da na’urar a Nijeriya domin daidaita lamurra. Wasu bangarori na malaman su suka kan lamarin suna masu cewar wata hanya ce kawai Saudiyya take son fitowa da shi domin dakile koyarwar wasu wadanda take da banbancin fahimta da su, hadi da cusa wa jama’a sha’awar Wahabiyanci karfi da yaji, inda wasu bangarori kuma suka goyi bayan shirin da cewar zai kawo ci gaba idan aka kawo Nijeriya.

 

Dakta Zubairu Abubakar Madaki daya ne daga cikin manyan malaman a bangaren Ahulus Sunnah, kuma Limamin Babban Massalacin Juma’a na Umar Bin Kaddab da ke Kofar Idi a Bauchi, ya bayyana ra’ayinsa kan wannan batun, inda ya nuna cewar wannan tsarin zai yi gayar kawo ci gaba wa gwamnatoci a dukkanin matakai.

 

Ya ce; “Da yake su kasar Saudiyya a yanzu haka suna kawo sauye-sauye a kan abubuwa da dama, dukkanin abun da suke ganin zai daidai musu musamman  shugabancinsu ba tare da sun samu matsala ba dole ne su yi amfani da shi, su kuma kallafa mutane su yi amfani da hakan.

 

“Masu wa’azi da masu karantarwar hadi da Limamai suna daga cikin wadanda suke da mutane magoya baya, kuma mutane suke saurarunsu da yarda da ababen da suke fada musu, don haka suna ganin cewa idan ba a sanya wa masu wa’azi da limamai takunkumi ba, lallai za su iya sanya mutane su yi musu bore ko zanga-zanga da yawan samun muzaharori ‘fito-na-fito’ kamar yadda aka yi wa kasashen Larabawa da dama, wanda hakan ya kai ga kifar da gwamnatocinsu daban-daban. Don haka ita kasar Saudiyya ta dauki wannan abun da  muhimmanci gaske; duk da kasancewa malamansu da limamansu suna da tsari domin basu cika dibo ta da fadi ba a sakamakon tsaurarawa da suke yi kan dukkanin malamai da basu bi tsari ba,” A cewar shi

 

Ya kuma kara da cewa idan aka ce za a kawo irin wannan tsarin Nijeriya zai taimaka wa gwamnatoci wajen kare musu martabarsu da muradinsu, “Idan aka ce za a kawo irin wannan tsarin Nijeriya, in dai gwamnatin Nijeriya ce ke bukatar hakan to tabbas zai taimaka mata gaya, domin babu banbanci a tsakanin gwamnatocin kasashen duniya, kowace gwamnati idan mutum ba zai bi ra’ayinta ba, ko malami ne ko dan adawa ne to za ta tabbatar da ta dauki mataki a kanta, saboda zai kwabar mata da gwamnati ko ya raba ta da jama’anta, don haka babu gwamnatin da za ta yarda da wannan, don haka idan gwamnati ne za ta amshi wannan hanu biyu-biyu,” A cewar Zubairu Madaki

 

Dakta Abubakar ya kara da cewa wannan tsarin ana nufin tsara yadda mai tafsiri zai rika gudanarwa ne, “Kimantawar ya yi daidai da ra’ayin gwamnati, sannan na biyu za a kimanta idan mutum zai yi huduba ko addu’a, ko wa’azi na minti talatin to ba a son ya wuce, idan mutum na son ya tsaya ya saurari tafisirin ka ga ya san minti nawa ko awa nawa zai kwashe,” Kamar yadda ya fadi.

 

Sai dai kuma Daktan Madaki ya bayyana illar da ke cikin wannan tsarin, yana mai cewa hakan zai hana malamai bayyana gaskiya a wasu lokutan, “Gaskiya wannan tsarin zai takura masu wa’azi gaskiya, domin abun da ya kamata su bayyana na gaskiya da abubuwan da suka dace, ba za a basu damar bayyanawa ba. Kowa zai kasance a tsorace yake, domin idan aka dauka na farko idan mutum ya fadi abun da ya saba wa gwamnati sau daya sau biyu zuwa ka ga da iyuwar gwamnati ta kama shi da like shi ba za a sake jinsa ba har karshen duniya, wannan shi ne babbar illar wannan tsarin,” In ji Dakta Abubakar Madaki.

 

A tasa fahimtar kuma, Dakta Fatihi Sheikh Dahiru Bauchi, malami a Jami’ar Kashere da ke Gombe, a gefe guda kuma da ga shararren Malamin Darika a Nijeriya, Shaikh Dahiru Bauchi ya yi karin haske kan batun.

 

Ya ce; “Mu dai gaskiya a matsayinmu na ‘yan Nijeriya wanda ba mu tare da bangaren Jama’atul Izalatul Bidi’a ba mu yarda da wannan tsarin sabo da kasar Saudiyya ke shirin kawowa ba,” In ji shi

 

Ya ce, akwai abun tambaya idan za a fara irin wannan zancen a Nijeriya wacce hanya daya ma za a fara, yana mai tambayar ta hanyar da za a fara kawo wata manhajar tantance tafsirai, “Idan akwai shirin hakan ai ba mu san ta yadda za a fara ba; shin gwamnati ce za ta ba su dama su shigo don shirya wannan? Ko kuma a’a wata kungiyace ta musulmai a Nijeriya za ta basu dama su shigo da wannan manufar.

 

“Mu kam ma ba ma za mu shiga ciki ba balle a ce za a tace mu; ai saudiyya suna magana ne da jama’ansu da suke Izala, mu kuma ba mu Izala. Idan suka ce za su kawo tsarin wa ‘yan uwansu ‘yan Izalah ne wannan su ta shafa; amma da zarar suka ce wannan wa al’ummar musulmai ne za su kawo tsarin, wannan basu yi daidai ba kuma ba za mu zura ido ba. Domin kasar Saudiyya ba su da hanu a kanmu,” Kamar yadda ya shaida.

 

Shehin malamin ya kuma kara da cewar Saudiyya suna da wata manufar dakile koyarwar dukkanin wata mazhaba da basu tare da ita ne, don haka ne suke shirin fara amfani da wannan tsarin a kasarsu, “Kwarai da gaske suna da manufa, babban manufarsu ita ce su canza ra’ayoyin mutane su samu zarafin tusa wa jama’a ra’ayin Wahabiyanci,” In ji Shaikh Fatihi.

 

Ya kuma kara da cewa, “Saudiyya tana shiga kwararo-kwararo tana shigar wa jama’a ra’ayin Wabiyanci da koyar da ‘yan Izala yadda za su shigar da ra’ayin Wabiyanci a zukatan mutane, don haka ne a kwanakin baya ma suka yi wani abu da ake kira Daura a garin Bauchi, manufar Dauran nan ba wai don su samar wa jama’a guraben karatu ba ne, a’a, ana yi ne domin a tusa wa wadanda suka halarci Daurar ra’ayin wabiyanci, domin sun yi Daura wa mutane dari hudu da hudu amma a ciki mutum shida kawai suke son dauka,”

 

Ya shaida cewar don haka ne basu tare da wannan tsarin ko kadan, “Don haka ba mu tare da tsarin na kasar Saudiyya ko kadan kuma ba za mu goya wa shirin baya ba,” Inji Shehin malamin

 

Ya kuma bukaci ‘yan Darika da sauran bangarori na addinin Musulunci da ba su Izala su hada karfe waje guda domin dakile yunkurin kasar Saudiya ta cusa wa jama’a ra’ayin Wahabiyannaci, “Kamata ya yi duk wanda ba ya da ra’ayin Izala; ba lallai sai dan Darika ba, ya dace da zarar aka fara shirin kawo mana wannan tsarin Nijeriya mu fito mu gaya wa gwamnatinmu cewar ba mu yarda ba. Mu shaida musu cewar wannan za su shigo mana da fitina ne, su je su fara kwantar da wutar fitinansu tukunna kafin su je su shiga wata kasa. Muna kira ga ‘yan uwanmu musulmai mu yaki wannan ra’ayin domin ana son a cusa wa jama’a ra’ayin Izala ne,” In ji babban Malamin.

 

A bangaren ‘Yan Shi’a kuma, LEADERSHIP Ayau Juma’a ta tuntubi Mukaddashin wakilin almajiran Shaikh Zakzaky na jihar Bauchi, Allaramma Idris Dauda kan wannan lamarin, inda ya yi suka hadi da bayyana cewar babu wani natija da irin wannan zancen zai janyo wa kowace kasa illa take hakkin wasu da kuma shigar da ra’ayin wata bangare daya ga jama’a.

 

Ya fara ne da cewa, “Shi Tafsirin Alkur’ani tsararren abu ne wanda Allah ya sauke wa Manzonsa ya isar ga jama’a, idan aka ce za a kawo wani sauyi ko tsari dole ne mu duba ya yi daidai da tsarin tafsiri idan ba haka ba babu amfaninsa. Sannan, kuma ita kasar Saudiyya babu abun da za ta iya kawowa da zai sauya yadda tafsiri ke gudanuwa domin abu ne yake a tsare, sai dai in suna shirin kawo rudani ne,”.

 

Ya ce; “Wannan lamarin a bayyana ne yake, duk lokacin da aka ce tsarin kimanta wa’azi zai fito, dole ne wasu ne za su zauna su tsara ita manhajar, idan kuwa haka ne su wadanda za su tsaran dole suna da tasu fahimta da ra’ayi wanda ya sha banban da na wasu, don haka ka ga kenan za su tusa nasu fahimtar ne a cikin tsarin wanda kuma kai tsaye hakan zai cutar da wasu sauran bangarori.

 

“Yanzu misali idan ita Saudiyya ta fara aiki da wannan tsarin; kowa dai ya sani ita kasar Saudiyya tana tafiya ne kan fahimtar Wabiyanci. Idan kuwa ta kawo wannan tsarin dole ne za ta take wa dukkanin wani musulmin da baida ra’ayin Wabiyanci hakki, misali akwai ‘yan shi’a a kasar Saudiyya, akwai masu bin fahimta ta darika da sauran wadanda basu tare da Wabiyanci, ka ga dukkaninsu kai tsaye za a tauye musu ‘yanci na karantarwa daidai da fahimtarsu. Domin ina da tabbacin kasar Saudiyya babu abun da za ta tsara wanda ya kauce wa ra’ayin Wabiyanci.

 

“Kuma ma, idan muka duba yadda kasar Saudiyya ke gudanar da lamarinta, ai kai tsaye tana tusa wa jama’a son Wabiyanci ne ta kowace fuska, ni a ganina da bari suka yi jama’a su gano kyan abun da suke bi har su zo su bi su ba tilasta wa jama’a bin tafarkin Wabiyanci ba,” A cewar Malam Idris Dauda

 

Malam Idris Dauda ya kuma daura da cewa kawo irin wannan tsarin a Nijeriya babu abun da zai jawo sai rashin fahimta da rarrabuwan kawuka, “Idan za ka fara amfani da wata manhajar daidaita ko kimanta wa’azi a Nijeriya da wacce akidar daya za ka tsara manhaja? Duk yadda ka ga manhaja dole da wani tsari aka tsara ta, don haka mu a Nijeriya muna da fahimta mabanbanta, kuma idan aka ce da fahimtar Wabiyanci ne za a shigo da abun hakan ba za ta taba ko yin tasiri a wannan kasar ba, domin Wabiyawan nawa ne a cikin Nijeriya?

 

Don haka ne ya nemi musulmai su ki yarda da wannan tsarin domin a cewarsa ba zai kawo ci gaba ba, “Da mu da ‘yan uwanmu ‘yan darika da sauran wadanda basu tare da fahimtar Wabiya ba za mu taba zura ido ana tusa mana Wabiyanci karfi da yaji ba. Don haka abun da zan ce idan da za a kawo wannan tsarin a Nijeriya shi ne ba ma zai yi tasiri ba balle ma a ce ya iyu,” Kamar yadda ya shaida.

Sha’anin wa’azi da sauran harkokin ibada Malamai ne ke da ruwa da tsaki a ciki, don haka hakkokin al’umma mabiya ya rataya a wuyansu wajen rabe zare da abawa domin samun maslaha.

Jama’a da dama sun zura ido su ga yadda manhajar za ta fara aiki a Saudiyya wadda ake tunanin da zarar ta yi tasiri, ba za a rasa kasashen Musulmin da ka iya amfani da it aba.

 

Advertisement

labarai