Bala Kukuru" />

Kirkiro Matsala Tsakanin Makiyaya Da Manoma Aka Yi

Tsohon ministan shari’a, a lokacin Sardauna Honarabil Jostis Mamman Nasir Galadiman Katsina Hakimin Malumfashi, kuma shugaban kwamitin  sasanci tsakanin manoma da makiyan kasar nan, ya bayyana cewar tsakanin manoma da makiyaya  a shekarun baya da suka wuce lokacin ana zaune lafiya da juna babu irin wadannan fadace-fadacen da juna, amma sai ga shi yanzu babu jituwa da juna.

Ya ce, da manomi in ya je gona ruwan sama ya buge shi har ya yi makuwa da ya tafi  gidan fulani sai ka ga sun ba shi wurin kwana, su kawo masa abinci ya ci sannan idan Allah ya wayi gari lafiya sai sun raka shi kan hanyar da zai bi ya tafi gida, haka shi ma Bafulatani, idan hakan ta same shi shi ma sai ka ga manomin ya sauke shi a gidansa, ya yi masa goma ta arziki to amma yanzu babu wannan.

Shugaban kwamitin sasancin ya ci gaba da cewar to kuma mene ne ya kamata wadannan jinsi guda biyu monomi da Fulani su yi kokarin fahimtar junansu saboda asamu zaman lafiya da juna. Domin wannan rashin jituwar da ke faruwa a tsakaninsu kirkirar musu ita aka yi daga baya. Saboda haka ya kamata su fahimci hakan, kuma su ba makiya kunya.

Galadiman ya ci gaba da  cewa tashin hankali ba ya sa a samu dukiya ko wani abu makamancin hakan, kuma tashin hankali ba ya kawo zaman lafiya, tashin hankali ba ya sa idan mutum ya mutu ya samu Aljanna, a cewarsa karshe ma duk wanda ke da hannu a haifar da tashin hankalin Allah ya la’ance shi.

Saboda haka, ya ce, bai ga amfanin fada ba, domin hakan ya sanya yake ba da shawara a kan wadannan mutane guda biyu manomi da makiyayi da su kawo karshen wannan abu,

Daga nan sai ya yi kira ga wasu mutane da suka mai da yin miyagun ayyuka sana’arsu  da su ji tsoron Allah su daina su zama mutanen kirki, yadda za su amfani kansu tare da sauran al’umma.

Exit mobile version