Daga Muh’d Shafi’u Saleh, Yola
Shugaban kungiyar kiristoci ta kasa (CAN) reshen jihar Adamawa, kuma shugaban cocin Catholic Diocese Bishop Stephen Dami Mamza, ya raba kyautar naira dubu 10-10 ga nakasassu dari biyu a Yola fadar jihar.
Ya ce “dama mun saba gabatar da irin wannan kyautar duk shekara muna ziyartan gidajen yari mu kaiwa mutanen dake tsare, amma bana saboda matsalar annobar korona bamuje ba, mu ka ga ya dace mu tallafawa nakasassu 200.
“Manufana shi ne na samar musu da kayayyakin abinci, amma na canja, bisa la’akari da cewa watakila wasunsu wani abinci na musamman su ke ci, ko rage cin abinci, yasa yana dacewar a raba musu kudin” inji Mamza.
Wani abunda LEADERSHIP A YAU Juma’a ta lura dashi, shi ne cikin nakasassun da su ka amfana da tallafin lokacin rabiyan sun hada da muslmi da kiristoci.
Da ta ke jawabin godiya a madadin nakasassun da su ka amfana Godiya Simon, ta godewa shugaban kungiyar kiristocin da tallafin da ya ba su.
Ta kuma yi addu’ar Ubangiji Allah ya albarkaceshi ya dinkamishi, ya daukaka matsayinshi, bisa so da kaunar da ya nuna mu su, ta yi fatan Allah ya albarkaci abinda su ka samu.