Daga Bello Hamza,
Kungiyar Kiristoci ta kasa CAN reshen jihar Kano ta yi kira ga mambobin ta da su kai taimako da dauki ga marayu da mabukata a daidai lokacin da suke gudanar da bukuwan kirsimeti da na sabuwar shekara.
Shugaban kungiyar, Rev. Adeyemo Samuel, ya bayyana haka a tataunawarsa da manema labarai a garin Kano ranar Alhamis.
Samuel ya kuma kara da cewa, ba duka iyalai suke iya samun abin da za su yi bukukuwa da shi ba a saboda haka ya kamata a taimaka musu a matsayin wani janibi na bikin da ake yi.
“Mu raba abinci da soyaya a tsakanin makwabtar mu da dukkan mabukata ta haka za mu kara dankon soyayya a tsakanin al’umma, Allah kuma zai ba mu lada,” iniji shi.
Ya kuma bukaci kiristoci su kara kaimi wajen ganin an samu zaman lafiya tare da kawo karshen matsalar tsaro a fadin tarayyar kasar nan.
Ya kuma bukaci Kiristoci su rungumi matakai na kariya daga cutar korona a yayin da suke gudanar da bukukuwan kirsimeti don kaucewa yaduwar cutar a fadin tarayyar kasar nan.