Daga Bello Hamza,
Shugaban Gidauniyar Ahmadu Bello, Alhaji Abubakar Umar, ya nemi ‘yan Nijeriya su yi bukukuwan Kirismeti tare da tabbatar da zaman lafiya da juna.
Alhaji Umar ya bayyana haka a sanarwar da ya raba wa manema labarai a garin Kaduna ranar Juma’a.
“Muna a Gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello muna kira ga dukkan ‘yan Nijeriya su rungumi juna cikin zaman lafiya tare da kaunar juna, muna kuma yi muku murnar bukukuwan kirismeti na shekarar 2020,“ inji shi.
“Yakamata mu yi koyi da yadda su Sardaunan Sakkwato suka jagoranci al’umma arewacin Nijeriya cikin adalci da kaunar juna ba tare da nuna banbanci ba,’’inji shi.